Skip to content

TikTok

Tiktok dai kamar sauran manhajajjon sadarwa ne na kafar yanar gizo. Wanda ake yin amfani da shi ta fuskoki da dama da suka haɗa wallafa faya-fayen bidiyo. Masu bincike sun tabbatar da manhajar ta ƙasar China ita ce kaɗai manhajar da ba mallakin Facebook ba da ta kasance cikin manyan manhajoji biyar da aka fi saukewa a duniya.

Manhajar TikTok ta kasance manhajar mafi farin jini da ake wallafa faya-fayen bidiyo.

A kasar ta China, kamfanin ByteDance da ya mallaki TikTok shi aka fi amfani da shi tare da wata manhajar bidiyo da ke amfani da harshen China Douyin. Manhajar ta TikTok ta samu karɓuwa duk da yunƙurin da tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya yi na haramta ta.

Tun a shekarar 2018 lokacin da aka soma bin diddigi kan shafukan intanet, manhajoji mallakin Facebook suke kan gaba a jerin waɗanda aka fi saukewa kuma har yanzu su ne aka fi mu’amala da su.

TikTok, Yadda shafin sada zumuntar ya zama matattarar samari da ‘yanmatan Arewa. Manhajojin kamfanin sada zumunta na Mark Zuckerberg su ne suka kasance sauran manhajoji huɗu da suke a jerin waɗanda aka fi saukewa – wato Facebook, WhatsApp, Instagram da Facebook Messenger.

A shekarar da ta gabata, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar haramta sauke manhajar TikTok a Amurka. Gwamnatin Trump ta yi zargin cewa TikTok yana bazarana ga tsaron ƙasar saboda China tana karɓar bayanai daga wurinsa. Sai dai kamfanin ya sha musanta zargin.

Amfanin Tiktok

Manhajar TikTok ta karbu a duniya.

Kamar yadda muka sani kowane abu na duniya yana da amfani da kuma rashin sa, hakan ne ya kasance ga wannan manhaja. Tiktok yana da amfani ta fannoni da dama.

Kasuwanci

Tiktok na taka rawa ta fannin kasuwanci da dama, tare da saukaka hanyar saye da kuma sayarwa kamar dai yadda yake faruwa a wasu kafofin sadarwar.

Ƙulla abota

Tiktok ya taka rawar gani wurin ƙulla abota tsakanin mutane musamman waɗanda suka kasance ba gari ko jiha ba har ma da waɗanda suka kasance ‘yan wata ƙasar daban.

Auratayya

Tiktok ya yi silar samun auratayya, misali auren Sadiya Haruna da Al’amin G-Fresh duk da cewar auren nasu ya yi ƙarkon kifi.

Nishaɗi

Tiktok ya taimaka ƙwarai wurin samar da nishaɗi a tsakanin al’umma wanda dama mafi yawa abin da ya kai su manhajar ke nan. Babban misali game da masu gudanar da abin da ya danganci nishaɗi shi ne wani matashi da ake kira Jooker.

Koyo da kuma koyarwa

An samu koyo da kuma koyarwa a sanadin manhajar TikTok, misali kamar masu koya girke-girke da suke dorawa suna koyawa mata da dama abin da zai amfane su. Wannan ya taka muhimmiyar rawa wurin koyawa mata da dama girki.

Samun kuɗin shiga

Mafi aksari masu gudanar da ɗora waƙe-waƙe ko raye-rayensu a manhajar suna ɗorawa ne domin nishaɗi ko kuma wani ra’ayi na kai da kai ko kuma cim ma wata manufa. Sai dai da yawansu akwai waɗanda zuwa yanzu hakan ya zame musu manufar rayuwa. Domin sun mayar da shafukan su wurin samun shigowar kuɗi ko kuma samun kuɗi a sauƙaƙe. Sannan bincike ya tabbatar da cewa ko mutum bai mayar da shafinsa wurin neman kuɗi ba matuƙar yana da mabiya to akwai gejin da wannan shafin nasa zai kasance yana samun wani kaso daga gare shi.

Matsalolin Tiktok

Tabbas manhjaar TikTok ta taka muhimmiyar rawa wurin haifar da matsaloli a rayuwar malam Bahushe da kuma al’adunsa. Ta fuskoki da dama wanda hakan ya zamo barazana ga cigaban gobensa.

Zamantakewa

A sanadin TikTok an samu taɓarɓarewar zamantakewar auratayya da dama, mata da mazan aure sun koyi wasu ɗabi’u wanda sam ba su yi kama da ɗabi’un al’ada ba. Mace mai ƙima da igiyar aure a kanta za ta shiga TikTok tana raye-raye da karairaya ta yi magijin kanta ta watsawa duniya ba tare da sanin mijinta ko kuma tunanin ƙimar aurenta ba.

Haka ma manyan mata wanda suna da manyan ‘ya’ya suke mayar da hakan abin sha’awa, za ka ga sun taƙarƙare suna rawa da juyi ba tare da tuna cewa su ɗin iyaye ba ne wata ma ‘ya’yan nata ne suke ɗaukarta. Ko kuma ka ga uba ya taƙarƙare yana rawa da ‘ya’yan cikin da ya haifa, an dora a duniya da sunan nishadi da fahimtar juna. Wanda sam hakan bai dace da tarbiyar Malam Bahushe ba. Domin idan nishaɗi suke son yi ba sai sun ɗora duniya ta ga ni ba sai su yi nishaɗi iya gidajensu.

Tarbiya

Ta fuskar tarbiya za mu iya cewa shi ne kankat, domin an yi nasarar cusa wa yara wata ɗabi’a wadda ta bambanta da tsarin rayuwar da Musulunci da kuma al’ada ta gina su akai. Yarinya ba ta kunyar yin rawa a ko’ina. Ba ta kunyar saka kowace irin surtura ta yi magiji da ita ta nuna wa duniya da sunan wayewa ko kuma nishaɗi. Yara da dama sun koyi ƙarya da raina arziƙi da ni’imar da Ubangiji ya yi musu saboda gidajen iyayensu ba su kai su yi abin da suke muradi a cikinsu ba. Sai an fita maƙota ko kuma wata uwa duniya a samu abin da suke kira da suna (background).

Rinjaye

Sai dai duk da waɗanan tsarin abubuwan da aka samu matsalolin da suke tattare da TikTok sun zamo masu rinjaye a rayuwar malam Bahaushe. Sun yi masa kaka-gida tare tare da wargaza duk wani tasiri na al’adu da kuma zamantakewarsa. An cire wa Bahaushe kunya da kuma jin kunya a zamantakewarsa.

Manazarta

BBC News Hausa. (2021, January 26). TikTok: Yadda shafin sada zumuntar ya zama matattarar samari da ƴan matan arewaBbc Hausa

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×