Tsafi ko kuma a ce sihiri, shi ne amfani da ikon allahntaka don yin mugunta bisa wasu dalilai na son zuciya ta hanyar aiwatar da mugayen ayyuka don hallakar da wani ko cutar da shi. Ana iya yin tsafi ta amfani da gashi, tufafi, hoto, ko kallon idanu kai tsaye na wanda ake son azaftarwa ko cutarwa ko ma hallakawa gabaɗaya. Yin tsafi ba sabon abu ba ne a duniya, an yi shi tun tali-tali, don haka muna buƙatar yin taka tsantsan a wannan lokacin kasancewar bai takaitu ga wata al’umma ba ko yanki, duk duniya ana yin tsafi.
Tsafi kalma ce da ake amfani da ita don bayyana wani nau’in sihiri ko ikon allahntaka wanda aka yarda ana amfani da shi don mugunta ko mugun nufi. A yawancin al’adu da tsarin imani na al’umma, ana kallon tsafi a matsayin hanyar da za a iya amfani da karfi dok sarrafa ƙarfin allahntaka don cimma wata manufa, sau da yawa wannan hanya ce ta cutarwa.
Mafi akasari tsafi bai cika azabtar da wanda aka nufa da shi ba da wuri, amma akwai wasu alamomi da kan fara bayyana kamar firgita a cikin barci, munanan mafarkai kamar faɗowa daga bene, tsintar kai cikin tsananin duhu, ciwon kai, gurɓatattun ɗabi’u, da sauransu.
Nau’ikan tsafi
1. Curse (La’anta): Nau’in tsafi ne na kiran masifa ko tsine wa wani don haifar da cutarwa ko bala’i gare shi.
2. Hexing (Tsibbu): Yin amfani da fasahar sihiri don sarrafa wani ta hanyar da akasari cutarwa ce ga wanda ake sarrafawa.
3. Necromancy (Magana da aljanu ko matattu): Wannan nau’in tsafi ne da ake tattaunawa da matattu ko aljanu don samun ilimi ko ikon yin wani abu.
4. Demonology: Fasahar ilimin sarrafa aljanu ko bautar aljanu ko wasu mugayen halittu.
Yana da mahimmanci a lura cewa fahimtar mene ne tsafi yana da mahimmanci sannan yana iya bambanta a mahangar al’adu daban-daban da tsarin imani. Wasu na iya kallon wasu ayyuka a matsayin tsafi, yayin da wasu suna ganin su a matsayin marasa kyau ko nagartattu.
Alamomin tsafi
Ga wasu alamomi na yau da kullun da ke da alaƙa da tsafi ko sihiri ga jikin ɗan’adam:
- Matsalolin lafiyar jiki ko ta hankali marar bayyana
- Mafarki mai yawa ko mafarkai marasa kan gado
- Canje-canje a cikin hali ko yanayin da ba zato ba tsammani
- Tsoron rashin hankali
- Mutum ya riƙa jin kamar ana kallon shi ko ana bin shi
- Bayyanar wasu alamomi ko yanayin da ba a saba gani a jikin mutum ba
- Yawaitar mantuwa ko rudani
- Yawan jin gajiya ko kasala
- Rama ko matsananciyar ƙiba marar fa’ida
- Samuwar canje-canje a cikin dangantaka ko zamantakewar aure
- Jin surutu ko motsin da ba a saba gani ba ko marar tushe
- Sauye-sauyen sha’awa ko yanayin barci ba zato ba tsammani
- Yawaitar jin kamshi marar dalili
Waɗannan alamomin na iya bayyana sakamakon wasu dalilai daban-daban, ba lallai su zama na tsafi ba. Kamar yanayin lafiyar jiki ta fannin likitanci, damuwa ko tunani, ko abubuwan da ke muhallin da ake zaune.
Abubuwan da ke haifar da yin tsafi
Abubuwan da ke haifar da yin tsafi ko sihiri, wanda kuma akasarin su marasa kyau ne na iya bambanta ta fuskar tsarin imani da al’adu da kuma yarda da aljanu. Ga wasu abubuwan gama gari da kan janyo aikata tsafi:
- Kishi ko hassada
- Ɗaukar fansa ko huce fishi
- Kwaɗayi ko son mulki
- Tsoro ko rashin tsaro
- Jahilci ko rashin fahimta
- Mugayen iskoki ko mahalli
- La’anta ko tsinuwa
- Mugun nufi ko tunani
- Baƙin ibadoji ko ayyuka
- Ƙarfi ko kuzari
- Rikice-rikicen da ba a sasanta ba
- Karma ta iyali ko kakanni
- Abubuwan da suka faru a baya ko rauni
- Mummunan tunani
- Rashin daidaiton ruhi
Tsafi a mahangar addinai
1. Addinin Kiristanci ya bayyana tsafi ta fuskoki kamar haka:
- Yana da alaƙa da Shaidan, ikon aljanu, da mugayen runduna.
- Ana kallon tsafi a matsayin nau’in tawaye ga Allah.
2. Addinin Musulunci ya kalli tsafi kuma ya bayyana shi da cewa:
- Wanit ne na shirka da Kuma kafirci.
- Aljanu da shaiɗanu da su ake aiwatar da tsafi.
3. Addinan Gargajiya na Afirka kuwa ya bayyana tsafi da cewa:
- Shi ne bautar kakanni da amfani da sihiri don kariya da ɗaukar fansa.
- Hanyar sadarwa ce tare da duniyar ruhi.
Tsafi a mahangar kimiyya
Tsafi da kimiyya suna da dangantaka kuma galibi suna cin karo da juna. Ga wasu ra’ayoyi:
1. Kimiyya tana kallon tsafi a matsayin:
- Camfi
- Pseudoscience
- Rashin fahimtar al’amuran halitta
- – Tasirin magani ko nuna son kai
2. Matsafa na kallon kimiyya kamar haka:
- Iyakacin fahimtar ilimin kimiyya shi ne duniya
- Yin watsi da al’amuran ruhaniya ko na allahntaka
- Rashin fahimtar abubuwan da suka shafi bokanci
3. Wuraren da tsafi da kimiyya suka yi ittifaki:
- Psychology: nazarin tasirin imani da shawara
- Neuroscience: fahimtar aikin ƙwaƙwalwa a cikin ƙwarewa
- Anthropology: nazarin akidar al’adu da ayyuka
- Physics: binciken yanayin gaskiya da sani
4. Bayanin kimiyya game da abubuwan ban mamaki na tsafi:
- Yaudara da ruɗu
- Rashin daidaituwa da tabbatar da son zuciya
- Jirkita ilimin halayyar dan’adam
- Abubuwan da suka faru na dabi’a ana bayyana su a matsayin allahntaka
Matakan kariya daga tsafi/sihiri
1. Nemi ƙwararren boka: Tuntuɓi amintaccen jagora na ruhaniya, guru, ko mai warkarwa.
2. Gano tushen matsalar: Yana da matuƙar muhimmanci a fahimci asali da manufar yin tsafin.
3. Kariya: A yi amfani da matakan kariya kamar guru, ko kambu, ko wasu abubuwan masu ba da kariya.
4. Tsarkaka: A yi wanka na tsarkaka ko, addu’a, don tsaftace jiki da zuciya.
5. Karya tsafi: A yi amfani da tabbatattun addu’o’i don warware tsafin ko sihirin.
6. Taimakon ƙwararru: Idan ana buƙata, a nemi taimako daga kwararrun masu kula cutar tabin hankali ko ƙwararrun likita.
Wasu takamaiman magunguna sun haɗa da:
- Kona sassaƙe ko ciyawa don tsarkakewa
- Amfani da ruwa mai tsarki don kariya
- Karanta addu’o’i don samun kariya
- Sanya laya ko guru ko kambu don kariya
Yadda za a warware tsafi ko sihiri
A samu rigar wanda aka yi wa tsafin da baƙin zare a ɗaure kulli bakwai. A samu busasshen jajayen barkono guda bakwai sai a zuba cikin rigar a naɗe su a ɗaure da baƙin zaren.
Kuma a ba da sadakar baƙaƙen tufafi guda bakwai ga mutanen ga a daren da aka yi wannan magani.
Lallai wanda aka yi wa sihirin ya guji shan barasa, domin mutanen da suke ta’ammali da barasa sun fi sauƙin farmaka da tsafi.
Idan ana sha’awar wani abu mara kyau, kuma zamantakewar aure ta ɗan bambanta da tsari na yau da kullun, to sai a ƙona kafur kowace safiya da maraice a cikin gida.
Za a samu ganyen tulsi, ganyen mint, bawon lemo, da tsaba da man nilgiri ko ganyen nilgiri sai a tafasa a ruwa na tsawon mintuna bakwai sai a raba kashi bakwai sannan a riƙa zubawa a kowane ɓangare na jikin mutum. Za a yi ta yin haka har tsawon kwanaki bakwai a jere.
Manazarta
Mahir Amil baba. (n.d.). get love back Astrologer Online Amil Baba
ProQuest. (n.d.). Islam’s views on sorcery and Black Magic –
Gnanaolivu, S. D., Campera, M., Nekaris, K. A., Nijman, V., Satish, R., Babu, S., & Singh, M. (2022). Medicine, black magic and supernatural beings: Cultural rituals as a significant threat to slender lorises in India. People and Nature, 4(4), 1007–1019.
Daruwalla, C. B. (2022, December 23). What is Black Magic? How can we protect ourselves from it? The Times of India.