Skip to content

Tumasanci

Tumasanci roƙo ne cikin sigar wayo da dabara, kuma abu ne wanda ake yi tun a shekarun baya har zuwa wannan lokacin da ake ciki. Saboda an mayar da shi babbar sana’ar da ake ci kuma a sha a cikinta.

Wa ke yin Tumasanci?

• Makiɗa
• Maroƙa
• ‘Yan maula
• Zauna-gari-banza

Wa ake yiwa Tumasanci?

• Sarakuna
• Masu kuɗi
• Masu Mulki
• Manyan ‘yan kasuwa

Yadda ake yin Tumasanci

Ana yin Tumasanci ne a cikin sigar yabon da yake wuce ƙa’ida. Ana kambama mutum da abubuwan da suka zarce matsayinsa ko waɗanda ke jawo masa girman kai domin ya hango kansa ya wuce inda mutane suke kallon shi. Ta yadda girman Tusamasanci zai iya saka mutum ganin ya fi kowa mutunci da kyauta, bayan tarin jama’ar da ke nuna masa soyayyar gaban ido saboda abin hannunsa.

Sau da yawa mutane masu Tumasanci suna hana kansu yawo su yi zaman ɓata wani ko gulmar wani domin su samu abin da suke nema. Sannan su miƙar da mutum a hanyar da yake kai da kambamawa ko da gurɓatacciyar hanya ce, matuƙar za su samu to za su wanke ta fes har da guzurin soso da sabulu don ƙara wa manufar armashi. Duk abin da mutum ya ce shi ne fari komai baƙinsa sunansa ƙalƙal.

Saboda suna nuna wa mutum soyayyar ƙarya a bisa biyan buƙatar ransu. Sannan da sun tashi daga dandalin su koma yi da mutum bayan sun gama ingiza shi yin abin da su kansu sun san ba ya bisa turbar gaskiya. Kuma ba za su iya sanar da shi zahirin gaskiya ba saboda kada kwanon abincinsu ya faɗi ko kuma su daina samun hasafin da suke yi wa Tumasancin babu dare babu rana.

A cikin masu Tumasanci wasu suna zabga wa mutum kirari ta sigar kallon matsayin da yake kai ko kuma wuce adadin matsayin nasa ana jayo wa mutum burinsa na gaba ya dawo kusa da shi saboda ya ji daɗin damƙa musu kyautar da bai yi niyya ba.

Misalan Tumasanci

1. Tumasanci ga mai kuɗi

Ka tara, an tara maka, kai ma za ka bari har bayan bayanka. Tsatson kuɗi asalin alheri sa gabanka inda kake so ka yi mun gani kuma mun yaba, mun ci mun sha kuma an ɗaura wa iyalanmu zane Alhajin Alhazzai mai tafiya da ƙamshin arziƙi. Kyautar Makka shan ruwa ya fi ta wahala idan ka yi nishin alheri. Sun sani, mu ma muna sane kai ne uban marayu ko da ji ko da ambaton sunanka. Sukari kake ba ka yi farin banza ba. Mai hannun kyauta irin ka gaba yake yi abadan babu komowa baya. Hanyarka miƙe mai gumi da ƙamshin alheri.

2. Tumasanci ga mai mulki

Gaba salamun, baya salamun Sarki mai takalmin ƙarfe. Ɗan na gada babu taka a haye, jinin mulki ɗan asalin masu gari kowa ya zo dole yana bayanku. Da yardar Allah kai ne yau, kai ne jiya shekaranjiya ma kai ne. Mulkin naku ne kuma ku kuke da iko sai wanda kuka dafa ya samu tagomashin alheri. Mai kyautar ban girma da bajinta babu lissafi sai dai damƙo miƙa. Sa gudu, ƙi gudu kuma sa maza zurawa da gudu. Farar aniyar laya balbela sa gabanki inda kike so. Rigiji gabji toron giwa.

3. Tumasanci ga ɗan kasuwa.

Ka ci dubu sai ceto don kowa ya sani kayanka sun yi wa saura zarra. Kai ne dilan kaya na duniya sai ka so ake raba sari. Allah Ya ba ka kai ma ka ba mu muna godewa. Sannu tirim ka fi ƙarfin kwasa, kai giwa ne ko ka faɗi ka fi ƙarfin wawason marasa albarka.

Waɗannan su ne ire-iren Tumasanci, waɗanda idan aka yi wa mutum zaƙin kalaman kan jefa mutum cikin shauƙi, sannan ido yakan rufe mutum ya yi hangen komai ya bayar bai faɗi saboda farincikin da aka jefa shi cikinsa. Sannan a wasu lokutan akan buɗa wa mutum wani sirrin a kan tuggu ko makircin da ake ƙulla masa ko da ƙarya ce aka tsara, zai ji daɗin Tumasancin kuma ya gode har ma ya yi alheri saboda ganin an tseratar da shi daga tarko.

Domin sau da yawa a kan shirya ƙarya ko a samo ƙagaggen labari a yi masa ado da ƙyallin gaskiya saboda a samu abin da ake nema. Saboda masu Tumasancin suna riƙo da irin baiwar tasu, kuma su dogara da ita kacokan saboda suna da tabbacin duk inda suka yi Tumasancin da wuya su tashi a banza. Saboda kaska ne su masu jini suke liƙewa domin su ma su tsotsi wani abu daga jikin masu hannu da maiƙo, sarakai ko masu mulki da kuka ‘yan kasuwa.

Wannan shi ne cikakken bayanin Tumasanci. Wanda aka mayar al’ada kuma ake yi tun zamanin iyaye da kakanni har zuwa ƙarnin da ake ciki. Wanda kuma akwai yiwuwar ya ci gaba da wanzuwa har zuwa ƙarshen lokaci. Saboda babbar sana’a ce da mutane suke riƙo da ita a da suna da wata sana’ar ko kuma aikin yin da ya fi abin da suke samu a Tumasancin. Saboda ɗabi’a ce idan ta shiga jikin mutum da wuya ta bar shi idan ba mutuwa ce ta raba ba. Domin mutane suna amfani da Tumasanci a ko’ina kuma a kodayaushe matuƙar suka hango hanyar samu.

Manazarta

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×