Skip to content

Yanayin Sanyi

Yanyi wani yanayi ne mai armashi da kuma samar da nutsuwa ga ɗan’adam. Sai dai a wurin wasu yanayi ne mai matuƙa wuyar sha’ani. Ta fuskar zamantakewa ko kuma mu’amala ta yau da kullum. Sanyi na ɗaya daga cikin nau’ikan yanayen da Allah Ya hallita a doran ƙasa wanda suke jujjuyawa a cikin duniya ta fuskar mu’amalar ɗan Adam da kuma ban ƙasa da duk wata hallita.

Yanayin sanyi na tattare da ƙura da hazo.

Yanayin na ƙunshe da busasshiyar iska mai ƙura, wacce ke busowa daga hammadar sahara ta yammacin Afirka.

Binciken masana ya tabbatar da cewa a lokacin sanyi, yanayin zafi kan ragu zuwa ƙasa da kashi 15 cikin 100, wanda hakan kan haifar da illoli ga lafiyar ɓangarorin jikin ɗan Adamwanda suka haɗa da fata, da idanu, da tsarin numfashi, gami da ƙara. Sauyin yanaye-yanayen kan haifar da matsaloli da dama ciki hadda tsanantar cutar asthma.

Alamomin sanyi

Alamomi da yawa na nuna shigowar sanyi ko kuma ƙaratowar lokacin, daga ciki akwai:

  • Lullumi-lullumi wanda kan iya haifar da yanayi kamar na damina.
  • Haza-hazo wanda kan iya haifar da sauyawar iska.
  • Hango murtukakkiyar ƙura daga gabashi ko kuma yanayi mai jaja-jaja musamman idan rana ta taho faɗuwa.
  • Tasowar iska haɗa da yanayi mai kama da na guguwa sai dai ba ta kai ta guguwa ƙarfi ba.
  • Haɗuwar hadari sai dai maimakon ya ba da ruwa sai ya saki iska wanda hakan kan iya sa garin ya yi sanyi.

Watannin da aka fi yin sanyi

Akasarin sanyi yana somawa ne daga watan Oktoba, wasu lokutan kuma ya kan fara daga watan Nuwamba. Amma kuma ya fi tsananta a lokacin watan Disamba da kuma watan Janairu. Wato watan goma da kuma watan ɗaya.

Abubuwan da ake shukawa lokacin sanyi

A lokutan sanyi ana iya shuka abubuwa kamar su:

Tafarnuwa

Tafarnuwa da duk dangin ire-irenta ana shuka su daga Janairu zuwa Maris. Wanda kowa ya san cewa watan Janairu wata ne na sanyi muku-muku.

Alkama

Ita ma ana shuka ta ne a watan sanyi, a wasu lokutan ma masu shukarta har sake roƙo yanayin suke yi ta hanyar yin wasu abubuwa da su suka yarda da su.

Karas

Ana shuka karasa ne tsakanin watan Janairu zuwa Maris. Wato dai a tsakanin watannin da ake yin sanyi.

Albasa mai lawashi

Albasa mai lawashi ta fi yin bozo lokacin sanyi, haka ma kayan lambu dangin su kayan miya sukan yi bozo a lokacin.

Cutukan aka fi yi lokacin sanyi

A lokacin sanyi akan samu ɓullar waɗansu cuttuka da kan addabi mutane a irin wannan yanayi da kan zo a yankin yammacin Afirka tsakanin ƙarshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar watan Maris na kowa ce shekara. Hakan kan haifar da wasu cuttuka wanda suke damun rayuwar ɗan Adam kamar:

Faso cuta ce da ke kama ƙafafuwa a lokacin sanyi.
  • Toshewar hanci
  • Yawaitar tari
  • Masu ciwon asma kan fama da yawan tashinta.
  • Masu ciwon haƙori su ma kan fama da yawan motswarsa.
  • Kumburi n wasu sassa.
  • Ciwon ido.
  • Ciwon kunne.
  • Ciwon haƙori.
  • Motsawar masu ciwon taɓin hankali.
  • Mura mai zafi.

Matsalolin sanyi

Matsalolin da sanyi kan haifar suna da yawa. Mafi girma daga ciki akwai motsawar wasu nau’in kan cuta da suka kasance kwantattu ba su cika tasiri ba sai lokacin sanyi. Kamar masu asma da taɓin hankali da ciwon haƙori da kuma sauransu. Matsalolin sanyi sun haɗar da:

Bushewar fata

A lokacin sanyi akan yi fama da bushewar fata saboda sauyin yanayi. Wanda hakan kan haifar da rashin jin daɗi ga al’umma da dama. Kasancewar mutane kowa akwai irin nau’in fatarsa, wasu fatarsu tana da maiƙo wato (Oil skin) wash kuma ta su tana da tauri wato (Dry skin) irin hakan idan aka rasu rashin kula sai a samu wata fatar ta samu matsalar dadddarewa sakammakon rashin kula yadda ya kamata.

Matsalar fason ƙafa

Matsala ce da ka iya addabar maza da mata, yara da kuma ƙanana wato matsalar kaishi. Wannnan matsala akasari mata na fama da ita, ko da ya saka ce su din ma’abota kwaliya ne amma yanayin yana yi wa mata da dama cikawa musamman ta fuskar gudanar da bukukuwa.

Rashin sakewa

Da dama daga cikin mutane ba sa iya sakewa a lokacin sanyi, a irin wannan yanayin wani ko ƙofar gida baya fitowa idan sanyi ya yi tsayi.

Naƙasun kasuwanci

Kaɗan daga cikin matsalar sanyi shi ne matsalar koma baya a harkar kasuwanci. Idan aka haɗu da wanda ba ya son sanyi ko kadan wani ma ranar ko shagon ba zai leko ba balantana ya siyar da wani abu. Misali masu sana’ar wanki. Suna fama da matsala ta rashin sakewa wurin gudanar da kasuwancin su.

Ƙarancin ruwa

A lokacin sanyi akan samu karancin mau siyar da ruwa, saboda kowa na ɗari-ɗari da lafiyarsa. Wanda hakan kan sa masu siyar da ruwan yin ƙaranci, alhali kuma a lokacin ana buƙatar ruwan saboda yadda ƙasa ta bushe ana samun ƙafewar rijiyoyi babu wadatacen ruwa yadda ya kamata.

Yawaitar ƙazamai

Akan yi fama da yawaitar ƙazamai a lokacin sanyi. Musamman da ya kasance yanayin kan iya ɓoye ɗumamar yanayi balantana har ya haifar da wani tashin wari. Wani ko kuma wata sai su shafe kwanaki goma ko bakwai ba su yi wanka ba. Musamman idan ya kasance ana yin muku-muku sanyi mai rikitarwa wanda Hausawa kan kira da wucewar jaura.

Kula da kai lokacin sanyi

A duk lokacin da aka ce sanyi ya durfafo, da yawan mutane kan fara fargabar yadda fatar jikinsu ko wasu sassan jikin kan yamushe saboda yanayin iskar hunturun. Hakan ta sa sai a fara tunanin me ya kamata a shafa don kaucewa hakan.

Ga shi kuma a daidai lokacin da sanyi ke kunno kai a ƙarshen shekara a wannan yanki na Afirka irin su Najeriya, a lokacin ne aka fi yin bukukuwa, mata kuwa sun fi kowa ado da kwalliya lokacin biki, amma kwalliya ba lallai ta yi kyau ba idan har jiki ya bubbushe.

  • Ƙwararru sun ba da shawarar a yawaita shan ruwa
  • Cin ganyayyaki da ƴaƴan itace
  • Cin ganyayyaki dangin su Salak da Kabeji da Karas da Gurji da irin su Dankalin Hausa da sauransu.
  • Akwai wasu dabaru da za a iya bi don inganta kyawun fatar jiki. Daga ciki akwai yin halawa da dilka, wani salo da ya samo asali daga Larabawan Sudan da ƴan Chadi.
  • Ana dafa sikari ne sosai a zuba wasu sinarai sai a dinga sawa a jikin mutum ana cire gashi da duk dattin da ya maƙale a fatar. Sannan a mulke jikin da sinadarin dilke ɗin a yi ta bi ana murzawa na wani ɗan lokaci.
  • Ƙafa wata muhimmiyar ɓangare ce ta jiki da take buƙatar a dinga kula da ita sosai, musamman a lokuta irin sanyi. A yawaita kula da ƙafa tare da yawan shafa mata mai da sanya safa mai taushi da saka ɗumi.
  • Shi ma gashi kamar yadda aka sani ya fi buƙatar kulawa sosai lokacin sanyi. Don haka ƙwararrun suka ce: A dinga yawan shafa masa mai da kuma rufe shi. Idan da hali a dinga zama da kitso maimakon barin sa a tsefe. A dinga shan ruwa sosai don yana kare gashi daga karyewa. Idan da hali a dinga yin abin da ake kira steaming, wato turara gashin makar bayan duk mako biyu.
  • Shi ma leɓe muhimmin waje ne da ke son kulawa ta musamman a lokacin sanyi. Jawahir ta ce yana da kyau a dinga yawan shafa man baki a leɓen saboda gudun bushewarsa.

Amfanin yanayin sanyi

Sanyi yana da amfani a wurin ɗan Adam kaɗan daga cikin amfanin sanyi sun haɗar da:

  • Ƙarancin sauro, lokacin sanyi babu yawaitar sauro sosai, domin shi sauro ruwa da ma shi ke sanya shi haihuwa akai akai.
  • Masu siyar da gawayi suna matukar ciniki a lokuta irin na sanyi, domin idan ka ɗauke damina sun fi kowa ne yanayi ciniki a lokacin sanyi.
  • Mata masu sana’ar hannu ta saƙa suma ana damawa da su a lokutan sanyi. Saboda iyaye da dama kan nemi kayan sanyi domin ɗumamar yanayi ga yaransu.

Manazarta

BBC News Hausa. (2023, December 19). Cutukan da yanayin sanyi ke haifarwa da yadda za ku kare kan ku. BBC News Hausa.

Focus, K. (2020, November 17). Yanayin sanyi: Hadarin da ke tattare da sana’ar wanki a Kano. Kano Focus.

Mustapha, O. (2018c, May 26). Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi. Aminiya.

Sánchez, M. (2024, March 15). Shuka shuke-shuke na lambu a lokacin sanyi. Jardineria On.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×