Zakatul fidr wato zakkar fidda kai sunnah ce mai karfi tana wajaba a kan kowanne musulmi babba da yaro mace dana miji ɗa ko bawa da sharadin akalla sa’i guda ya ragu daga cikin abincin da mutum ya mallaka a ranar da ta wajaba a kansa.

Zakkar fidda kai nau’in sadaka ce ta farilla wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya farlanta ta yayin da aka kammala Azumin watan Ramadan. Ana kira ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an kammala Azumin Ramadan gabaɗaya.
Hukuncin zakkar fidda kai
Zakkar Fidda kai wajibi ce a kan dukkan Musulmi, wanda ya mallaki sa’i ɗaya na abinci (kwatankwacin kwano ɗaya ke nan) wanda ya fi yawa a cikin nau’in abin da yake ciyar da iyalansa da shi. Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take karkashinsa, har ma ɗan jaririn da yake cikin ciki ana fitar masa.
Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga Ɗan Umar, Allah ya yarda da shi ya ce, “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wajabta zakkar fidda kai, sa’i ɗaya na dabino, ko sa’i ɗayan da sha’ir, an wajabta ta a kan bawa, da ɗa, namiji da mace, babba da yaro daga cikin Musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Lokacin da ake fitar da zakkar fidda kai
An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan Alfijir ya ɓullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a fitar da ita kafin ranar idi da kwana ɗaya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin Ɗan Umar wanda ya gabata in da yake cewa, “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.
Haka ma a cikin hadisin Abdullahi Ɗan Abbas, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karɓaɓɓiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
A wani kauli kuwa an ce ba ta wajaba sai washe garin sallah. Amma dai a kowanne hali sunnah ne a yi saurin fitar da ita da fitowar alfijir na ranar sallah.
Wannan yana nuna mana ana son mutum ya yi gaggawar fitar da ita kafin sallar idi, amma ko da bayan sallar idi ne ba ta fadi ba a kan mutum sai dai idan ba shi da abin yi kwata-kwata, to a nan kam ta fadi a kansa. Dan Allah yana cewa “Ba ma dora wa rai abin da ba ta da iko a kansa” kuma Allah ya sake cewa “ku ji tsron Allah gwargwadon ikonku”.
An tambayi Annabi SAW a kan ayar nan da take cewa “hakika wanda ya tsarkake kansa ya rabauta ya kuma ambaci sunan Allah ya yi sallah saboda shi”. Annabi ya ce ai wannan aya ta sauka ne don tabbatar da zakkar fidda kai. Ɗan Huzaima ya rawaito wannan hadisin.
Adadin da ake fitarwa a zakkar fidda kai
Gwargwadon abin da za a fitar sa’i ne na alkama, ko sha’ir ko zabibi, ko wanin haka daga mafi rinjayen abincin mutanen garin. Sa’i kuwa a ma’aunanmu na zamani yana daidai da kilogram (2.176). An rawaito daga Ibn Umar cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya wajabta sadakar Fid-da-kai a sa’in na alkama.
Nau’in abubuwan da ake fitarwa
Ba ya halatta a fitar da ita sai daga daya daga cikin nau’in abincin nan:
- Alkama
- Sha’ir
- Sultu
- Dabino
- Zabib
- Cukui
- Gero
- Dawa
- Shinkafa
- Alasu
- Masara ko garin masara
- Wake
- Maiwa.
Amma idan an rasa ɗaya daga cikin waɗannan ya halatta a fitar da ita daga irin abincin da mutanen wajen suke ci. Saboda hadisin Abu Sa’id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha’ir da zabibi da cukwi. (Cukwi shi ne nonon da ya bushe, ana girki da shi) da dabino.” [Bukhari ne ya rawaito shi].
Halaccin ƙimanta kuɗi ko kadarori a matsayin zakkar fidda kai
Malaman fiƙihu na Hanafiyya sun halarta fitar da ƙimarta daga kuɗi, ko kadarori, domin manufa dai ita ce, toshe bukatar mabuƙata a ranar idi, wannan kuwa yakan samu ta hanyar ba da kuɗi, kamar yadda yakan samu da ragowar jinsunan da suka zo a cikin hadisin. Sai dai jamhurun malaman fikihu sun tafi a kana rashin halarcin fitar da ƙima a cikin zakkar fid da kai, domin hadisai sun bayyana wasu nau’ika abubuwa na musamman daga alkama da sha’ir da zabibi.
Waɗanda ake bawa zakkar fidda kai
Ana ba da ita ga musulmi fakiri ko miskini, kuma ba a bayar da ita ga bawa ko kafiri, da mawadacin mutum. Mutum shi zai fitar da zakkar nan ga wanda ciyar da shi ta wajaba a kansa da sababin zumunta ko aure ko bauta. Idan ta wajaba a kan mutum amma ya yi jinkirin fitar da ita to ba ta faduwa a kansa, saboda haka zai fitar da ita ko bayan watanni masu yawa.
Ana ba wa waɗannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin faɗin Allah Maɗaukakin Sarki “Abin sani kawai, dukiyoyin sadaka na faƙirai ne da miskinai da masu aiki a kansu, da waɗanda ake lallashin zukatansu, kuma a cikin fansar wuyoyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.”
(Suratul Tauba aya ta 60)
Hikimar zakkar fidda kai
Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da ba su da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa’ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin waɗanncan maganganun haramun da ya yi, waɗanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
Yalwata wa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roƙon mutane, roƙon da yake ɗauke da ƙasƙanci da wulaƙanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farinciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farincikin ranar idi.
Sharuɗɗan zakkar fidda kai
Musulunci
Don haka ba ta wajaba a kan kafiri ba, koda yana da makusanta Musulmai waɗanda ciyar da su ya wajaba a kansa, domin zakka idaba ce ta Musulunci, ba ta wajaba a kan wanda ba Musulmi ba.
‘Yanci
Ba ta wajaba a kan bawa a asali, domin ba ya mallakar dukiya, amma idan bawan ya zama mabiyi ne ga shugabansa, to a nan zakka ta wajaba a kan Ubangidansa, saboda wajabcin ciyarwarsa a kansa take, faɗin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama “Ku ba da (zakkar Fid-da-kai) a madadin duk wani ɗa, ko bawa da kuke ciyar da shi”.
Iko na dukiya
A kan fitar da ita, wannan iko kuwa yana tabbata ne, da mallakar dukiyar da ta ƙaru a kan buƙatarsa a daren idi da yininsa, don haka zakkar tana wajaba idan mutum ya mallaki wannan gwargwado na dukiya, ko da ya cancanci a ba shi zakka.
Shigar lokaci
Zakkar Fid-da-kai tana wajaba bayan gama azumin watan Ramadana, wannan kuwa na kasancewa ne da faɗuwar ranar yinin ƙarshe na azumi, domin babu azumi a bayansa. Kuma lokacinta yana ƙarewa ne da zarar a gama sallar idi. Kuma ba ya halatta a jinkirta ta, daga ranar idi. Idan ba a fitar da ita a ranar idi ba, ya fitar daga baya to ta zama sadaka ba zakka ba.
Idan mutum ya zama mai gida, zai fitar da ita ga kansa, da wanda yake ciyar da su, kamar mata da ɗa, ko da ƙarami ne, da uwa da bawa da mai hidima. Hadisin “Ka fara da wanda kake ɗaukar nauyinsa”. Yana ƙarfafa haka. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, “Ku ba da (zakkar fid da kai) a madadin kowane ɗa da bawa, daga waɗanda kuke ciyarwa”.
Shi kuwa jinjirin da ba a haifa ba kafin iadin zakkar Fid-da-kai, a madadinsa ba ta wajaba a kan mahaifinsa ba, amma babu laifi idan ya fitar da ita, kuma zai sami ladan nafila.
Manazarta
Alkur’ani Mai Tsarki: Suratul Tauba aya ta 60.
Sahihaini: (Bukhari da Muslim)
Sunanu Abu Dawud
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.