Skip to content

Zazzabin Lassa

Zazzabin Lassa cuta ce mai saurin yaduwa da ke haddasa zazzabi mai tsanani da zubar jini da mutuwar gaɓoɓi. Ƙwayar cutar Lassa ce ke haifar da wannan zazzaɓi. Cutar dai na yaɗuwa a ƙasashen yammacin Afirka da dama da suka haɗa da Najeriya da Saliyo da Laberiya da kuma Guinea.

Zazzaɓin Lassa, wanda wani nau’in bera ke yaɗawa, ya fi ƙamari a wasu ƙasashe da ke yammacin Afirka ciki har da Najeriya.

Yaɗuwar zazzabin Lassa

Zazzabin Lassa na yaɗuwa ne ta hanyar shigar ƙwayar cutar cikin abinci ko kayayyakin amfanin gida waɗanda suka gurɓata da fitsari ko kashin berayen da ɗauke da wannan ƙwayar cuta. Haka nan tana iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar saduwar ta kai tsaye ta jini ko fitsari ko kashi ko sauran abubuwan ruwa-ruwa daga jikin mai ɗauke da cutar. Wannan hanya ta yaɗuwar cutar ta zama ruwan dare musamman a wuraren kiwon lafiya inda ba a samar da ingantattun matakan dakile kamuwa da cututtuka ba.

Mutanen da ke zaune a yankunan karkara inda berayen Mastomy (wato nau’ikan berayen da yaɗa cutar) suka yi ƙamari suna cikin haɗari mafi girma na kamuwa da cutar. Haka nan ma’aikatan kiwon lafiya da masu jinyar da ke kula da masu ɗauke da cutar su ma suna cikin haɗari musamman idan babu isassun matakan kariya.

Alamomin zazzabin Lassa

Akwai alamomi da dama da ke nuna cewa an kamu da wannan kwayar cuta mai haifar zazzaɓin Lassa. Kuma alamomin sun kasu gida biyu, akwai alamomi na farko; sauƙaƙa da kuma alamomi masu tsanani.

• Alamomin farko

Alamomin farko na zazzaɓin Lassa sukan bayyana daga mako 1 zuwa 3 bayan kamuwa da cutar. Waɗannan alamomin farko na iya yin kamanceceniya da sauran cututtukan zazzaɓi na yau da kullun, suna zama tarnaki wajen gano cutar Lassa da wuri. Sau da yawa alamomin ba su da taƙamaiman sigar ganewa suna iya haɗawa da:

  • zazzaɓi
  • mutuwar jiki gabaɗaya
  • rauni
  • ciwon kai

• Alamomi masu tsanani

Yayin da cutar ke cin jikin mutum har ta kai wani mataki, alamomin cututtuka masu tsanani na iya bayyana kamar:

  • Hemorrhage (misali, gumi ko hawaye ko yoyon hanci)
  • Matsalolin numfashi
  • Yawaitar amai
  • Kumburin fuska
  • Jin zafi a kirji da baya da ciki

A wasu lokuta, matsalolin neurological kamar jiri ko girgiza, da encephalitis za su iya faruwa. Kusan kashi 20% na mutanen da suka kamu da cutar suna fuskantar wannan matsalar.

Gwaje-gwajen Lassa

Ma’aikatan lafiya kan bincika zazzabin Lassa ta hanyar gwada samfuran sinadaran ruwa daga jikin wanda ake zargin ya kamu da cutar. Domin yin wannan gwaje-gwaje, ma’aikatan lafiyar na iya yin:

  • Gwajin jini
  • Gwajin fitsari
  • Kakin marar lafiya

Zazzabin Lassa na yin iya kama da wasu cututtuka, ciki har da zazzabin cizon sauro da zazzaɓin dengueZazzbi da Ebola. Don haka yana da wahala a gano shi cikin sauƙi. Sanar da ma’aikatan lafiya idan an yi tafiya zuwa wuraren da zazzabin Lassa ya zama ruwan dare na taimakawa wajen gano cutar.

Magungunan zazzabin Lassa

Mastomy, su ne nau’in berayen da ke yada ƙwayar cutar Lassa

 

An gano cewa Ribavirin, maganin kashe kwayoyin cuta, yana da tasiri wajen magance zazzabin Lassa idan aka yi amfani da shi da wuri a lokacin da cutar ba ta yi ƙamari ba. Maganin na aiki ta hanyar hana haihuwar ƙwayar cuta, da rage yawanta da tsawon lokacin da take ɗauka na rashin lafiya. Likitoci na iya ba da wasu magunguna dangane da yanayin cutar waɗanda suka haɗa da:

  • Dialysis don lalacewar koda.
  • Ƙarin iskar oxygen don taimakawa numfashi.

Riga-kafin zazzabin Lassa

Riga-kafi ko daƙile yaɗuwar zazzaɓin Lassa ya haɗa da rage cuɗanya da berayen Mastomys. Ingantattun matakan riga-kafin sun haɗa da:

  • Ajiye abinci a cikin mazubin da berayen ba za su iya budewa ba
  • Tsaftace gidaje da wuraren taruwar jama’a
  • Yin amfani da tarkuna da maganin beraye
  • Ma’aikatan kiwon lafiya su bi tsauraran matakan kauce wa kamuwa da cuta don hana yaɗuwarta daga mutum zuwa mutum. Wannan ya haɗa da:
  • Amfani da kayan kariya kamar safar hannu, abin rufe fuska, da riguna
  • Tabbatar da ingantattun hanyoyin tsabtace hannu
  • Ware abubuwan da ake zargi ko tabbatarwa
  • Wayar da kai da ilimantar da al’umma game da illolin zazzabin Lassa da inganta matakan riga-kafi na da mahimmanci don shawo kan yaduwar cutar.

Matsalolin zazzabin Lassa

Zazzaɓin Lassa na haifar da matsaloli da dama bayan an kamu da shi. Hatta a yanayin da cutar ke da sauƙi, kusan mutum 1 cikin 3 na mutane masu fama da zazzabin Lassa na fuskantar wani ɓangare na matsala ji ko ma su rasa jin gabaɗaya. Wannan matsala na iya zama ta ɗan lokaci ko ta dindindin. Har ila yau masu fama da zazzaɓin Lassa na iya fuskantar rikice-rikicen rashin lafiya na daban masu barazana ga rayuwa waɗanda suka hada da:

  • Rashin ɗaukar ciki ko zubewarciki. Fiye da kimanin kashi 75 cikin 100 na masu juna biyu suna fuskantar barazanar zubewar cikin a lokacin da suka kamu da cutar Lassa.
  • Kumburin haƙarƙari musamman sashen da ke rufe da zuciya.
  • Taruwar wani ruwa a kusa da huhu (pleural effusion).
  • Bayyanar kumburin wasu gaɓoɓi ko sassan jiki kamar hanta (hepatitis).
  • Haifar da ƙananan platelets (thrombocytopenia). Wannan na iya haifar da zubar jini mara tsari.
  • Gazawar aikin ƙoda nan take, ƙoda kan daina yin aikinta nan take.
  • Matsalolin da suka shafi aikin kwakwalwa.
  • Matsalolin ciwon numfashi mai tsanani, wanda kan iya hana jikin mutum samun isasshiyar iskar oxygen.
  • Matsanancin ciwon daskarewar jini
    Sepsis, mummunan dauki ga kamuwa da cuta.

Cutar Lassa a jikin mai juna-biyu

Masu ciki suna buƙatar kulawa ta musamman. Yawancin lokaci, ɗan-tayi ba zai iya tsira daga kamuwa da cutar zazzabin Lassa ba. Ma’aikatan lafiya kan sa ido a kan dukkan alamomin zubewar ciki. Masu juna-biyun na buƙatar cire duk wani ɓurbushin ɗan-tayi da wuri idan zubewar ta faru. Wannan yana taimakawa wajen inganta yanayin masu larurar.

Tsawon lokacin da cutar ke ɗauka

Yawancin cututtukan zazzabin Lassa suna da sauƙi idan an ba su kulawar gaggawa. Cutar na iya ɗaukar mako guda ko fiye kafin a samu sauƙi da jin daɗin jiki. Kimanin rabin mutanen da ke fama da rashin ji sakamakon cutar suna dawowa ji a cikin ‘yan makonni.

Adadin mutanen da ke mutuwa

Yawancin mutane masu fama da cutar suna da ƙananan alamomi ne kuma cutar tana a matakin da bai ta’azzara ba, don haka adadin waɗanda ke tsira daga cutar yana da yawa. Yawan mace-mace dalilin zazzabin Lassa ya dogara ne da yanayin ƙarfin cutar  da sauran dalilai kamar:

  • Adadin mace-mace na duk wanda ya kamu da cutar, mai sauƙi da mai tsanani ya kai kashi 1%, wato 1 cikin 10 na masu fama da zazzabin Lassa zai mutu a dalilin cutar.
  • Mutanen da aka kwantar da su a asibiti kuwa, adadin mace-macen ya kai kusan 15%. A lokacin barkewar cutar, wannan na iya zama mafi girma.
  • Mata masu juna-biyun ma, yawan mace-mace kusan kashi 33% ne ko kuma 1 cikin mutane 3.

Manazarta

Cleveland Clinic: Lassa Fever. (2024, May 1). Cleveland Clinic.

Medicover Hospital: Zazzabin Lassa Dalilai, Alamu, da Magani. (n.d.). Medicover Hospital

World Health Organization: (2019, July 10). Lassa fever. WHO

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×