“Haihuwa maganin mutuwa, ba don ke ba da iri ya kare!” Wannan shi ne kirari da ake wa haihuwa. Kuma sukan kara da cewa, “Kyan gida da magaji!” kirarin haihuwa kirari ne na karuwa.
Ma’anar haihuwa
Haihuwa ita ce, yayin da miji da mata suka sami karuwa da samun ɗa ko ‘ya. Masomin haihuwa kuwa shi ne, lokacin da mace ta samu juna biyu, wato ta sami ciki, bayan an tabbatar da igiyar aure tsakaninta da mijinta. karshen haihuwa kuwa shi ne yayin da jariri ya fito daga cikin uwarsa ta hanyar al’ada. Tun daga wannan lokacin ne iyaye za su shiga tattalin abin da suka samu, har sai ya girma ya kai munzalin mutane, wato ya kama kansa.

Neman taimako
Da zarar mace ta samu ciki (juna-biyu) sai iyayenta ko masu lura da ita su dukufa wajen neman taimako don ta sauka lafiya. Akan kuma kafa mata dokokin da za ta kiyaye, kamar kada ta rika cin abinci, ko abin sha mai zaki, kamar zuma da sukari ko rake ko muzarkwaila ko alawa, saboda saukin nauyin fitowa abin haihuwa wanda yake faruwa da ciwon zaki. To, kuma akan umurce ta da ta rika shan magani a kai a kai, kamar sabara da bauri. Da kuma wasu tadodi na mai ciki kamar rashin fita da dare ba tare da wani makami ba, kamar wuka ko lauje ko kan makoki ko mashinjiri ko dagi, saboda shu’umi da aljani.
Goyon ciki
Wannan shi ne yarinya ta tafi gidan iyayenta don ta haihu, amma idan haihuwar ta farko ce, saboda a taimake ta, a kuula da ita sosai da sosai, don gudun hadari da barkwanci wajen haihuwa, da rashin iya yin wankan biki kamar yadda ya dace.
Nakuda
Anan in an ga alamar cewa haihuwa ta kusa, sai a shiga neman maganin saukin guiwa, kamar shan rubutu da jike-jike. Sai a aika a kirawo wata mace, watau arbiki ko ungozoma, don ta kula da mai haihuwa. Kuma in ta sauka lafiya a kula da abin da aka Haifa. Kuma ta yanke cibiya, ta binne uwa, watau mahaifa. Kuma ba za a ba da sanarwar haihuwa, sai in an ga faduwarta, kana arbiki ko ungozoma ta kan ce “Alhamdu Lillahi, barka da arziki!” da sauran maganganu ko addu’o’i da a kan yi bayan mahaifar ta fadi.
Guɗa
Akan yi guda sau uku (3) idan na miji aka samu. Idan mace ce kuma guda hudu (4) wannan guda tamfar shela ce, cewa ga irin abin da aka Haifa.
Lugude
Sai a kama yin lugude don a sanar wa makwabta an sauka. Na nesa kuma a aika musu da manzo takanas. Lugude daka ne da akan yi shi cikin raha, ana yi ana guda kada turmi, da kwarya , da sauransu. Akan taru a yi gayya wajen dakan luguden. Baicin sanarwa ana kuma yin maganar boye ta hanyar lugude. Masu lugude suna iya yi wa makwabta ba’a ko zambo ko wani abu makamancin haka. Su kuma idan sun gane, sai su girka nasu luguden, don su mayar da martini.
Wankan biƙi
Wannan wani irin wanka ne na tilas da yarinya take yi ko ake yi mata, da cewa ta sauka lafiya, wannan wanka ana yin sa ne da tafasasshen ruwa mai zafin gaske, tare da ganyen runhu ko sabara ko kuma darbejiya, saboda maganin sammatsin ciwon sanyin Haihuwa, wanda ya kan sukukuce yarinya ya kuma gadar da kurumta da sumkwita da susuta. Wani lokaci ma yakan aukar da barna fiye da haka.
Yarinya dai takan yi wankan sau biyu a yini safe da maraice, tun daga ranar Haihuwa har ta yi kwana arba’in (40) sa’anan ta mayar da shi sau daya a yini da safe kawai ko da maraice. Har ma ta bari sam idan aka amince da cewa wata cuta ta sanyi ba za ta bijiro mata ba faufau. Wannan wankan muhimmi ne kuma wajibi ne ga duk mai Haihuwa. Domin sau da yawa idan har aka kuskure, ba a yi shi da kyau ba, ko ma ba a yi shi bas am-sam-sam duk cutar da ta same ta sai a danganta da rashinsa. Har an masa kirari ana cewa:
- wankan biƙi maganin sumbwita.
- Yarinya daure ki yi shi ki huta.
- In kin kuskure shi sai buzunki!
Kunun kanwa
Wannan wani irin nau’in kunu ne wanda ake dafa shi kana a sanya masa kanwa da kayan yaji citta da masoro da kanamfari da ka-ji-ji domin mai biki ta sha watau, ‘kunun kanwa’ tun daga ranar da ta haihu sannan a ci gaba da ba ta maganin kaikayin nono da sauran irin su.
Yaji
Wannan kaya ne da miji ke kaiwa bayan an haihu da kwan uku (3) na barka da Haihuwa, wadanda suka kunshi kayan yaji da hatsi da ita ce da man fitila da kayan yaji da kayan jinjiri da na mai Haihuwa da kudin sayen nama.
Ƙauri
Sayen ganda ko langabu na sa ko na tunkiya, ko Ma a yanka tumkiya, ko dan bunsuru, ga mai hali, wannan shi ake kira kauri. Daga nan sai a rarraba shi ga ‘yan’uwa da abokan arziki, musamman ma wadanda ba a kai musu kunun biki ba.
Tanade-tanaden bikin suna
A bisa tsarin al’adun Hausawa, akwai tanade-tanaden da mazaje magidanta kan yi domin tarbar abin da za a iya haifa masu da zarar mutum ya fahimci cewa matarsa ta sami juna biyu. Daga cikin irin kayan da ake tanada kuwa sun haɗa da:
Magungunan dauri
Waɗannan magunguna ne da miji ke tanadar wa matarsa ko kuma iyayen miji ko na matar su tanada domin bai wa mai juna biyu ta sha musamman idan cikin ya kai kimanin wata bakwai zuwa haihuwa. Amfanin magungunan shi ne domin ta sami sauƙin haihuwa. Magungunan za su wanke zaƙi da maicon da ke cikin ciki na mai juna biyu, wanda hakan zai sanya ta sami sauƙin naƙuda a lokacin haihuwa.
Itacen biƙi
Maigida zai fara tanadin itatuwan da za a yi amfani da su a wajen shagulgulan wankan jego har zuwa bikin suna da kuma kwanakin da mai jego za ta yi tana wankan ruwan zafi.
Kayan barka
Waɗannan kayayyaki ne da suka danganci suturar maijego da abin da ta haifa. Maigida zai tanade su ne tun kafin a haihu ko kuma bayan an haihu. Daga cikin kayan akwai turamen atamfa da kayan jinjirai da turare da man shafawa da na kitso da sauran su da yawa gwargwadon halin magidanci.
Al’adun da ke tattare da bukin sunan Hausawa
Waɗannan al’adu ne da suka shafi shagulgulan da ake yi a ranar suna. Waɗannan al’adun kuwa sun haɗa da;
Taron suna
Taro ne da ‘yan’uwa da abokanin arziki inda za su taru domin taya murna ga mahaifin jinjiri da maijego a ranar da aka cika kwana bakwai da haihuwar jinjiri. maza sukan taru ne a kofar gida, su kuwa mata suna zama a cikin gida ne domin hidimar shirya abinci ga baƙin da suka halarci bukin.
A lokacin bikin akan kawo goro a raba shi kasha biyu, wato gefen maigida da gefen mai haihuwa, domin kowa ya raba wa mutanensa da suka zo taya shi murna. Akwai wani kaso da ake keɓe wa Malamai masu addu’o’i da kuma wamzamai da ma’aska da maƙera su ma da nasu kaso na al’ada. Wannan shi ne ainihin bikin wanda a dalilin raɗa sunan ne ake shirya taron suna. Sai dai zamani ya fara yi wa wannan al’adar rauni domin wasu a masallatai suke yi wa ‘ya’yansu addu’ar raɗin suna.
Yanka dabbar suna
Dabbar suna, dabba ce da akan tanada domin a yanka ta hanya tabbatar wa da jinjiri suna yanka. Galibi a ƙasar Hausa akan yanka Rago ko Tumaki ko Awaki ko ma a wasu lokuta Shanu a wajen raɗin suna.
Tsagar gado
Wannan tsaga ce da ake yi a tsakanin Hausawa domin a nuna irin ƙabilar da mutum ya fito daga cikin kasha-kashen Hausawa. Misali, akwai Zamfarawa da Kabawa da Katsinawa da Kanawa da Zazzagawa da sauransu. A bisa al’ada akan yi wa abin da aka haifa tsagar gado ne tun ranar bikin sunansa.
Wasannin gado a ranar suna
Wasanni ne da suka shafi martaba irin gadon gida ko sana’o’in da mutum ya tashi a cikinsu. Misali idan a gidan Mahauta ne akan yi wasan hawan ƙaho, ko a yi wasa da wuta idan a gidan maƙera ne da sauran su.
Abincin gara
Wannan abinci ne da ake yi na musamman domin bukukuwan aure ko suna a ƙasar Hausa. Galibi irin wannan abinci ya shafi masa (waina) da alkaki da dubilan da fanke da naman kaji. Akan raba wa mutanen da suka zo shaidar raɗin sunan domin su ci, kuma su tafi da shi a gidajensu.
A cikin wannan maƙala an kawo tare da bayanin abubuwan da suka shafi al’adun haihuwa da bikin suna a alummar Hausawa.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.