Skip to content

Al’adar mutuwa

Kalmar mutuwa baƙuwar kalma ce da aka aro daga harshen Larabci watau “Al Maut.” A harshen Larabci tana nufin ƙarewar rayuwa ko amfanin wani abu. A harshen Hausa kuwa, kalmar tana nufin rasuwa ko ƙarshen ran mutum ko dabba ko duk wani abu mai rai. A bisa tsarin al’ada da addinin Bahaushe duk sun aminta da faruwa mutuwa a kan kowace rayuwa da ke a doron ƙasa. Mutuwa kan riski mutum ta hanyoyi daban- daban, wani rashin lafiya, wani hatsari wani lokaci kuma haka kurum idan kwana ya ƙare.

A wata mahangar an bayyana mutawa da, ”Rasa rayuwa ko barin aiki ga abu mai rai ko marar rai, mutum ko dabba ko tsiro ko wata halitta ko kuma wani abu mai amfani ta yadda ake ganin alamun ba zai taɓa dawowa yadda yake a da ba kafin ƙaddarar rasa rayuwar ta auka masa.” Mutuwa ita ce ƙarewar abu mai rayuwa ko lalacewar abu marar rayuwa, ya zama ba za a iya sake wani amfani da shi ba kamar yadda aka saba a da face sai an gyara abin nan, misali mota da sauran injiman na’ura.

Ire-iren sunayen mutuwa

Dangane da sunayen mutuwa na asali a cikin harshen Hausa, kamar rasuwa, raguwa, fakuwa, ƙaura, kasawa, wucewa, shukuwa, rigaya, ya kau, ƙarewa, dogon kwana/barci da sauransu sai a duba wannan shafin da aka ambata.

Bahaushe yakan yi amfani da kalmomi da dama wa]anda kan maye gurbin sunan mutuwa. Sai ga dukkan alama kalmomin sukan jiɓinci rasa rayuwar mutane ne ko dabba.Kaɗan daga cikin kalmomin da suke wakiltar sunan mutuwa ga Hausawa kamar yadda sun haɗa da:

  • Rasuwa
  • Raguwa
  • Fakuwa
  • Ƙaura
  • Kasawa
  • Tafiya
  • Dogon Barci/kwana
  • Wucewa
  • Shukuwa
  • Rigaya
  • Ya kau
  • Ƙarewa
  • Shurewa
  • Rai ya yi halinsa
  • Babu shi
  • Kwanta dama
  • Wafati
  • Halaka
  • Ya sa kai
  • Ya shuri bokiti

Dalilan faruwar mutuwa

A imanin Bahaushe mutuwa kan faru ne bisa ga dalilai mabambanta, duk da yake yana da yaƙinin faruwar mutuwa irin ta ba zato ba tsammani, wadda ake ganin mutum kawai ya yanke jiki ya faɗi. Irin wannan tunanin ne ya biyo har zuwa ga Hausawan yau, inda za a ga da an sami sanarwar mutuwa sai ka ji ana tambayar, rashin lafiya ne ko hatsari. Dangane da haka, wasu daga cikin dalilan da kan haifar da samuwar mutuwa a Bahaushen tunani sun haɗa da:

  • Tsufa
  • Rashin Lafiya
  • Hatsari
  • Maita
  • Camfi
  • Annoba
  • Tsafi
  • Faɗe/baki
  • Tsoro
  • Rantsuwa
  • Yaƙi
  • Shan guba
  • Farmakin dabba
  • Tsotsayi

Alamomin fitar rayuwa

Hausawa suna da wasu fitattun alamomin da suka aminta da cewa idan sun bayyana ga mutumin da yake fama da jinyar rashin lafiya,to ana kyautata mai zaton zama kusa da barin duniya. Waɗannan alamomin kuwa sun haɗa da:

  • Tsananin sanyin jiki ko zafin jiki.
  • Farin ido ko rashin ƙiftawarsu
  • Bu]ewar baki
  • Rufewar Idanu
  • Karyewar harshe na rashin iya magana mai ma’ana
  • Shaƙuwa
  • Yi wa ‘ya’ya da dangi wata muhimmiyar magana (wasiyya)
  • Sandarewar jiki ko gaɓa.

Tabbatar da faruwar ta

Hausawa suna da hikimar tantance faruwar mutuwa gabanin su yanke hukunci an mutu ko bayar da sanarwar mutuwa tun zamani mai tsawo. Hikimar hakan shi ne domin su kaucewa bizne mutum da sauran rayuwarsa ko banza ma akwai abin da suke kira doguwar sumainda mutum zai suma kamar ya mutu ne daga baya a ga yana numfashi. Dangane da haka, daga cikin dabarunsu na gane rai ya yi halinsa an mutu sun haɗa da:

  • Fesa ruwa a jikin maras lafiya, yin hakan zai sanya idan yana da sauran rayuwa a gay a motsa,
  • Motsa babbar yatsar ƙafarsa
  • Bugun hannu a ƙasa kusa ga kansa, a nan za a bugi hannu aƙalla sau uku.
  • Za a kira sunansa a gani ko za ya motsa.
  • Akan zuba yashi a ƙirjinsa a gani ko zai motsa.

Idan duk an yi waɗannan dabarun aka ga bai motsa ba to daga nan za a yanke hukuncin rayuwarsa ta fita sai a dangana. Daga nan sai faɗar mutuwa ga dangi da abokan arziki.

Binne mamaci

Hausawa sukan bizne mamaci da tun a ranar da ya mutu, sai fa idan tsakiyar dare ne akan bari sai da safe a bizne gawar. Kodayake akwai ra’ayin cewa wasu maguzawan Hausawa sukan bar gawa har bayan kwana uku. Akasarin Hausawa sukan binne gawa ne tun ranar da aka yi rasuwa, wannan al’adar kuwa ana gudanar da ita ne tun gabanin bayyanar musulunci ga Hausawa. Yanayin haƙar ramin da za a binne gawa kuwa akwance ne akan sanya gawa. Kuma akan sanya mutum da kayan aikinsa kamar warki ko makamantansa a cikin ƙabari, idan kuma mace ce akan sanya ta da kayan aikin gida da ta saba amfani da su. Ƙananan yara kuwa sai a shafa masu shuni a fuska wai idan sun je su ba mutuwa tsoro kada ta sake dawowa ta ɗauki wani.

Bayan zuwan musulunci sai abin ya sauya, inda kafin a binne mamaci sai an yi masa wanka an sanya masa turare da kuma sutura. A yi masa sallah sannan a kai shi ƙabarinsa.

Al’adun mutuwa kafin Musulunci

Waɗannan wasu fitattun al’adu ne da Hausawa kan yi game da sha’anin mutuwa tun kafin zuwan musulunci a ƙasar Hausa. Waɗannan al’adun kuwa sun haɗa da:

  • Amfani kwarya wajen wanka tare da kife su da zarar an gama. Ba za buɗe ba sai ran uku.
  • A cika kwaryar da hatsi da kayan mamaci na sawa a ba wa mai wankan gawa, sai kuma a ba wa matar mamaci sanda ta rika yawo da ita wai ko da zai dawo mata ta doke shi.
  • Zubar da ruwan randa zarar an yi mutuwa tare da kife randunan da zummar cewa wai ba za a yi amfani da ruwan ba, tun da ba a san da wacce mutuwa ta wanke wuƙarta da shi ba. In ma da rijiya a gidan akan yi ƙoƙarin kwarfe ruwan mai tarin
    yawa a zubar, dan cewar watakila da wannan ruwan mutuwar ta wanke wuƙar.
  • Sanya wa yara toka a zagaye musu ido, idan ba a sami toka ba sai a zagaya musu bakin tukunya wai don kar su yi mafarki da wannan mamacin.
  • Sanya ko ɗora faifai ko takobi ko dutse ko kuma takobi a kan cikin mamacin da daddare, da zimmar cewa wannan shi zai hana cikin ya kumbura kafin wayewar gari.

Manazarta

Abdullahi I.S.S “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa. Kundin Digiri na uku UDUS, 2008

C.N.H.N (2006) Ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero, Kano.

Ibrahim, S.M (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”. Kundin Digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×