Skip to content

Asalin camfi

Kamar yadda bayanai suka nuna, abu ne mawuyaci a fadi lokacin da al’ummar Hausawa suka fara wasu daga cikin al’adunsu da dabi’unsu, domin abu ne wanda yake da makusanciyar dangantaka da kafuwar al’umma. Al’adar camfi ma na daga cikin al’adun da ba za a iya tantance lokacin da aka fara su ba.

baobab tree0
Akwai camfe-camfen da ake dangantawa da itaciyar kuka.

Camfi, hanya ce ta zato da Bahaushe ya gina kansa a kan ta dangane da faruwar wasu abubuwa. Wannan al’ada ta camfi, na daga cikin munanan al’adun da Bahaushe ya ke da su tun dauri. Bahaushe yana aƙidantuwa da zace-zace da ya yi dangane da faruwa ko afkuwar wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa. Wannan al’ada masana suna yi mata kallon mummunar al’ada ce.

Ma’anar camfi

Camfi wasu aƙidoji ne waɗanda suke a zukatan Hausawa bisa yarda cewa in aka aikata wani abu, za a ga wani abu a matsayin sakamako. Irin wannan hanyar rayuwa ta Hausawa ta ƙunshi hani da horo. Misali,

  • Ba a fita ɗaki da dare sai an yi tari sau uku
  • Cin Aya yana ƙara ƙarfin gani
  • Idan mace ta ƙetare wanda, za ta yi mafarki
  • Yawan cin tuwon dawa yana ƙara ƙarfin gaɓoɓi.

Imanin Bahaushe da camfi

Camfi yana ɗaya dagga cikin shika-shikan imanin Bahaushe, inda ake gasgata faruwar abubuwa da wani abu na daban da ba wahayinsa aka yi ba. Magabata suka ƙirƙiro shi domin ya dace da rayuwar al’umma. Haka za a ci gaba da aiwatar da shi, tare da koyar da shi ga masu tasowa, ta yadda za a samar masa da babban bagire a cikin imanin mutane.

Shehun Malamin nan wato Farfesa Bunza, ya tafi kan cewa ‘Camfi shi ne imanin da Bahaushe ke da shi dangane da wasu al’amurra da abubuwa waɗanda magabata suka tsara bisa ga fasalin hani da horo da sakamakon abin da zai biyo baya. Camfin Bahaushe yana tafiya ne a kan yarda da imani. Kuma ana ɗora shi kan matakin hani da horo da sakamako. Idan aka umurci a yi abu, aka aikata, za a ga sakamako mai kyau. Idan kuwa aka hana abu aka aikata za a ga mummunan sakamako.

Misali, hani na kar a aiwatar da tatsuniya da rana tsaka ido na ganin ido camfi ne, amma an samar da mafita game da hakan. Mafita kuwa itace, a tabbatar da cewa an ɗaure Gizo. Idan har an aikata hakan to, ba shakka ba wata matsala da za ta auku. Amma idan aka ƙi bin wannan dokar aka aikata, to kuwa sakamakon da zai biyo baya shi ne ma makancewa, ko ɗimaucewa ko makuwa wanda ko ba hukunci ne mai kyau ba.

Asalin samuwar camfi

Camfi ya samo tushe ne tun lokacin da dan’adam ya fara tunanin lalle akwai wasu abubuwa da ke da tasiri a kansa da harkokinsa da rayuwar da ke kewaye da shi. Ta haka ne yakan kagi gurbataccen tunani na yanki-fadi, ya shirya wani bayani, ya dauki wasu abubuwa ya jingina su da tasirin wani abu.

Yahya da wasu (1992:18-19). Suka ce ga alama wajen kokarin samar da ingantacciyar al’umma ta yin horo da hani, al’ummar Hausawa suka kagi dabarar camfi ta neman taimako daga wani abu wanda ya fi karfinsu don tsayar da ka’idoji da dokokin samun zaman lafiya.

Bello (2004) kamar yadda yake cewa dangane da asalin samuwar camfi “Yana da wuya mutum ya ce ga lokacin da dan’adam ya fara yin camfi  da kuma dalilin yin su a duniya, amma ta hanyoyin nazarce-nazarce da tarihin rayuwar dan’adam dangane da al’adunsa, a iya kafa hujja dangane da wasu abubuwa da ake ganin su ne kila masomin camfi da kuma lokacin fara su”.

Hasashe kan samuwar camfin Hausawa

Akwai hasashe-hasashe da yawa da masana al’ada ke yi kan tarihin samuwar camfi a al’adar Bahaushe, idan aka yi la’akari da ma’anoni da magabata kuma masana al’ada suka bayar game da camfi za mu ga cewa akwai tazarar hasashen camfi kamar haka:

Hasashe na daya

Ibrabim, (1982) Ya ce “tun lokacin da mahiccin halitta ya halicci halittu, Hausawa sun tarar da sama da kasa a shimfide, yanayin da Bahaushe ya samu kansa a farfajiyar duniya ya taimaka wurin haifar da camfe-camfen Hausawa. Tsarin sararin samaniya da kawace-kawace da ke tattare da ita irin su rana, da wata da sauyawar dare, da rana, ya ba wa Bahaushe damar gina camfe-camfe da dama bisa abubuwan da ya ga sun wakana a ciki. Idan ana laluben tarihin camfin Bahaushe, dole ne a yi la’akari da wadannan abubuwa ta fuskar nazari, musammam ta fuskar camfe-camfe da aka gina a kansu. Misali.

  • Idan rana ta kama wata wani abu babba zai faru
  • Hazo alama c eta yanayin daminar da ke tafe.
  • Kwanciya a hasken farin wata na debe budurcin mace.
  • Idan hasken wata ya bayyana da dare ko akwai hadari ba a ruwa.
  • Idan zunni (bakan-gizo) ya bayyana a hadari ba a ruwa ranar
  • Ruwan kankara alama ce ta samun wake wannan shekara

Idan aka dubi wadannan misalan, za a ga cewa Bahaushe ya gina camfinsa ne akan wadannan yanayi saboda ganin akasarin lokaci hakan na kasantuwa gare shi, wannana ma shi ne asalin abin da ya sanya shi yin amannah da hakan.

Hasashe na biyu

Bunza (2006) ya ce “Tarihin samuwar camfi yana da alaka ta fuskar da Bahaushe ya kiyaye fasulan shekara kamar: Rani, da Damina, da Bazara, da Hunturu. A cikin wadannan lokuta wasu abubuwa muhimmai suna aukuwa kuma Bahaushe yana kiyaye su, da yanayi da suke faruwa, da kuma dalilin da ke sa su faruwa. Da haka ne Bahaushe ya gina wasu camfe-camfe kamar haka: Misali

  • Kashe kwaron damina yana kawo fari.
  • Idan shamuwa ta zo cikin gari, damina
    ta kusa.
  • Idan ana ruwa ba a son ana surutu.
  • Iskan hunturu ne ke motsa haukar mahaukata. Da sauransu

Hasashe na uku

kamar yadda bincike ya bayyana dangantakar Bahaushe da tsirarrai, da itacen magani na gargajiya, yana da muhimmiyar rawar da ya taka wajen tarihin samuwar  camfi. Ga alama, Bahaushe shi ya tarar da tsirrai, bas u suka tarar das hi ba. To yanayin itace da tsirran magani musamman kan mahadinsu, da yadda ake sarrafa su, ya yi naso sosai ga tarihin samuwar camfin Bahaushe idan aka dubi wadannan mislan kamar haka:

  • Shan itacen shashatau na haifar da mantuwa.
  • Shan tsimin gawo na bushe zuciya da kore tausayi a cikinta.
  • Ba a kwance laya, idan an kwance ana yin hauka.
  • Ba a yin jima’i da guru, in an yi ya lalace.
  • Ba a dariyar maras lafiya cutar za ta koma kan mai dariyar.

Hasashe na hudu

Yanayin lafiyar jikin Bahaushe, da huldarsa a duniyan mafarki, na daga cikin abubuwa da ya kyautu a kula idan ana son a kwakulo tarihin samuwar camfi. Bahaushe ya kiyaye da wasu abubuwa dab a sa shafa wa lafiyar jikinsa lafiya, wasu kuwa suna razana lafiya, wasu na karfafa lafiya wasu kuma kashe jiki suke. Daga nan ne ya gina mafi yawa daga cikin camfe-camfensa.

  • Cin naman akuya na kara harzuka cutar kuturta.
  • Cin kwayar takiyar tsakiyar goruba na sa makoko.
  • Kwana da wando yana raunana karfin namiji.
  • Ketara wando na sa mata mafarki.
  • Yawan cin waina na haifar da mura.
  • Cin dawa na kara karfin gabobi.
  • Cin dankali na rage karfin namiji.
  • Cin aya na kara karfin gani.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page