Auren sadaka wani irin aure ne da uba zai bayar da diyarsa ga wani Malami ko wani talaka wadanda ba za su iya yin hidimar aure da kan su ba. Uban diyar ba ya sa ran samun komai daga auren, domin ya yi ne saboda Allah, shi kuma mijin ba ya kashe komai in ba tukuicin da zai ba wadanda suka kawo yarinyar ba don nuna godiya. ‘Mamaki sai wanda ya gani ga Angon’. Domin ba a ga ya ma sa cewa ga shirin da a ke yi. Dubi wannan makala da ta yi bayani akan rike sirri shi ne ginshikin zaman aure.

A yau ba a yin irin wannan aure sosai saboda gurbata shi da a ka yi da wadansu abubuwa. Yanzu mutane ba don Allah su ke aurar da ‘ya‘yansu ba. Domin har wadanda suna da hali suna ba su, har ma ga mai mace daya ko biyu ko uku. Iyaye na amfani da wannan hanyar domin aurar da ‘ya’yansu munana, wadanda babu wadda ya ce ya na so. Bayan haka wanda ake son ba wa yarinya, ana gaya masa watanni kafin ranar daurin auren. Saboda haka zai fara yi wa yarinyar kyauta da kuma yi wa iyayenta wadansu ‘yan hidimomi. Idan aka kawo yarinya, angon zai bayar da rago, a matsayin tukwici.
Da tafiya ta yi tafiya, sai mutane suka fara dawowa daga rakiyar irin wannan aure. Yanzu ana iya kawo wa mutum yarinyar, amma ya ce, ba ya so, idan ya ga ba ta da kyau ko kuma idan ba ya iya kara wata matar. Ana yin wannan cikin kawaici. Zai gode wa wadanda suka kawo ta kwarai da gaske. Ba yan haka, ya ce, masu ya zama tilas ya mayar da hannun wannan babbar kyauta don ba ya da wani dakin da zai sanya ta. Daga nan sai a wuce da yarinyar wajen wani mutumin, wanda ya na iya amsa ko kuma ya ki.
Auren sadaka a zamanin baya
A lokutan baya abu ne da yake yin ƙarko duba da yanayin abubuwa masu yawa, haka kuma daga macen har mijin suna karɓar abun cikin martabawa. Namijin yana ganin cewa cancanta ce ta sanya aka bashi yayin da macen take hangen namijin a matsayin wanda ya rufawa rayuwarta asiri ya karɓe ta matsayin mata. Haka kuma duk wani abu da zai zo da shi ta kan karɓe shi cikin martabawa da mutuntawa tare da nuna masa cewa ya kai namiji a gidansa.
Auren sadaka a yau
Auren sadaka a yanzu ya sauya daga tsarin da al’adar Hausawa ta kimsa masa. Wasu na ganin auren sadakar ya sauya duba da tasirin zamani. Ta yadda za ka ga daga macen har namijin babu wanda yake duban abokin zamansa a matsayin wani mai girma tare da mutuntawa. Ko dai macen tana kallon namijin a wanda aka haɗata da shi aka dakushe mata rayuwa ko kuma wani mugu wanda ya samu aurenta tamkar birin da ya hau bishiyar mangwaro nunanne.
Haka kuma da dama mazan na duban matan matsayin wasu masu tawaya ko kuma nasakara rayuwa ko wani giɓi da aka manna musu ita domin rufe wani abu na ta da ba a so duniya ta sani. Takai ta kawo ko mace ba ta da wani abin nunawa idan aka ce an bayar da ita sadaka ake tsoron karɓar auren tare da sauyawa kyakyawar al’adar wata manufa ta daban.
Auren sadaka a zamanin yanzu yana ci gaba da kasancewa batun jayayya, musamman duba da yadda zamantakewa, al’adu, da tattalin arziƙi da suka canja. Ga wasu abubuwa da suka shafi auren sadaka a yau:
Sauƙaƙawa matasa
Auren sadaka zai taimakawa matasa matuƙa da gaske wurin ba su damar da za su yi aure cikin sauƙi. Wanda hakan zai rage yawaitar ‘yan matan da masu da masu auren su.
Takurawa
A wasu wurare, iyaye da al’adu suna buƙatar sadaki mai yawa kafin su yarda da aure. Wannan yana hana wasu yin aure cikin sauƙi. Auren sadaka yana sauƙaƙa wannan matsalar, amma wasu iyaye ba sa amincewa da shi.
Tasirin Ilmi
A yau, mutane da dama sun fi fahimtar cewa sadaki bai kamata ya zama cikas ga aure ba. Wasu malamai suna goyon bayan rage sadaki domin sauƙaƙa aure, amma suna jaddada cewa dole ne sadaki ya kasance a cikin aure.
Dalilan auren sadaka
Dalalai da yawa kan iya haifar da yin auren sadaka a da da kuma lokacin da zamani ya kawo kai. Sai dai kuma dalilan da dana zamanin duk suna goggaya da juna ta fuskar manufa ko kuma wani dalili na daban. Daga cikin dalilin akwai;
Jinkirin aure
Rashin samun miji da wuri ko kuma ganin an aurara da duk sa’anin yarinya akan yi amfani da wannan damar a bayar da ita sadaka ga wanda ake ganin ya cancanta.
Rashin jin magana
Yarinyar da ba ta jin magana ko kuma tara samari barkatai tare da ƙin tsayar da tsayayye ka iya sanyawa magabatan yarinyar su tunzura su zaɓi wani cikin manemanta su ce sun ba ta shi kuma sun yafe komai.
Nagarta
Malamin da ya yi shura a wata shiyar ko kuma ya sauka a wani gari ya ba su ilmi ko kuma Limamin da yake wani gari. Sukan rabauta da auren sadaka a mafi yawan lokuta. Dattawan wannan gari masu karamci sukan iya yin kyauta da ɗiyar su domin nuna kara ko kuma kyautatawa gareshi. Wasu kuma kan yi amfani da wannan dama domin cewar; yaransu za su raɓu da wannan nagarta ta wannan malami ko limami har a samar musu da jikoki hafizai ko malamai domin samun kyakyawar zuri’a.
A mafi yawan lokuta bincike ya tabbatar da cewa dai-dai kun matan malamai ne suka nema da kansu. Yawancin lokuta ba su ake yi. Wannan gaɓar ta yi tarraya da lokacin baya da kuma yanzu, domin a yanzu haka ma ya kan iya faruwa.
Masu arziki
A wasu lokutan akan samu iyayen da suke baiwa masu kuɗi auren ɗiyarsu saboda wata manufa ta su. Ita ma wannan gaɓar ta yi tarraya domin ya kan faru a lokutan baya da kuma yanzu. Ka ga an ɗauki yarinya sukutum da guda an bawa wani mai kuɗi an ce ga ta nan ya aura ba tare da shi ya nuna ra’ayin hakan ba. Wannan aure ba shi da maraba dana sadaka, domin ko da ya yi hidima a kan auren a kwan a tashi sai an samu mai gorantawa amaryar cewa sadaka aka bayar da ita.
Abin kunya
Ana iya bayar da yarinyar da ta yi abin kunya a auren sadaka saboda danginta na son sakaya wani abu da ta aikata ko kuma hukuntata bisa wannan abin da suke ganin ta ɓata musu zuri’a sakammakon aikata shi.
Abota
Abota kan iya zama dalilin ɗaukar ɗiya a bayar da ita ga abokin babanta aure, wanda a wasu lokutanma shi wannan aboki ya kan iya zama maɗaaurin aurenta. Amma sai a wayi gari an ba shi aurenta, wani nagarta ce take haifar da hakan domin sake ƙarfafa zumunci wani kuma manufa ce ta daban tsakanin mahaifinta da abokin nasa.
Talauci
Yana taka muhimmiyar rawa sosai wurin haifar da auren sadaka.
Matsalolin auren sadaka
Auren sadaka na taka muhimmiyar rawa wurin haifar da matsaloli da dama a rayuwar malam Bahaushe. Ga wasu daga cikin matsalolin:
Tauye haƙƙin mace
Sadaki haƙƙin mace ne a cikin aure. Idan an hana ta ko an rage shi fiye da ƙima, ana tauye mata haƙƙinta. Hakan kan sakata cikin damuwa har ma a wasu lokutan ya zame mata abin gori cikin al’umma.
Rashin daraja da ƙimar aure
Sadaki yana daga cikin abubuwan da ke nuna darajar aure da ƙimar amarya. Idan aka yi auren sadaka ba tare da kulawa ba, yana iya rage darajar aure a idon wasu. Irin hakan kan sa a wasu wuraren da ilmi bai wadata ba mace ba ta da sakewa ko a tsakar gida. Idan ma haihuwa ta yi daga ita har ya’yanta va sa wuce gori a cikin gari musamman ya kasance akwai abokiyar zama.
Haɗarin wulaƙanta mace
Idan ba a biya sadaki yadda ya kamata ba, wani lokacin namiji na iya raina matar ko ɗaukar ta a matsayin wadda ba ta da matsayi mai girma a gidansa. A irin wannan gaɓar har tutiya suke yi su samu kuɗi su auro matar so.
Sauƙin rabuwa
Mawuyaci ne ka ga auren sadaka ya yi tasirin jimawa. Wasu mazan da suka yi auren sadaka suna ganin ba su yi wahala ba wajen aurar da matar, don haka za su iya sakin ta cikin sauƙi, ba tare da tunani mai zurfi ba.
Haifar da matsaloli a zaman aure
Idan an yi auren sadaka saboda matsin lamba ko wani dalili, amma ba tare da yardar zuciya ba, yana iya jawo matsaloli a cikin aure, kamar rashin girmama juna ko rashin kwanciyar hankali. Wasu lokutan ma macen ta kan yi ƙoƙarin saɓawa mijin ta hanyoyi da dama. Kamar kujewa ba shi hakkinsa ko kuma makamantansu.
Auren sadaka yana iya zama mai kyau idan an yi shi da niyya mai kyau kuma an mutunta haƙƙoƙin kowane ɓangare. Amma idan aka yi shi ba tare da bin ƙa’idojin aure na addini da al’ada ba, yana iya zama matsala.
Alfanun auren sadaka
Auren sadaka na taimaka ƙwarai da gaske ta fuskokinda dama ga rayuwar malam Bahaushe. Ga tarin wasu daga cikin alfanun auren sadaka.
- Sauƙaƙa aure
- Rage matsalolin zamantakewa
- Riƙe sirri
- Ƙarfafa soyayya
- Kaucewa rashin adalci
- Kiyayye doka da addinni
Manazarta
Al-Qur’ani: Suratul Nisa’i (4:4) da Suratul Baqara (2:236-237).
Hadisan Annabi (SAW): “Mafi albarkar aure shi ne wanda aka fi sauƙaƙa masa.” (Sunan Abu Dawud, Hadisi na 2117).
Ibn Qudamah, “Al-Mughni” – yana bayani akan dokokin sadaki a musulunci.
Al-Mawardi, “Al-Ahkam al-Sultaniyyah” – yana tattauna alakar aure da zamantakewa.