Skip to content

Bakan gizo

Bakan gizo ko rainbow a Turance, wani abu ne mai launuka da ake iya hangowa a sararin samaniya, musamman lokacin da hadari ya fara haduwa ko bayan ɗaukewar ruwan sama lokacin da rana take haskawa. Bakan gizo yana bayyana kamar wani layi ko zobe mai launuka daban-daban da ke yin jerin gwano a sararin samaniya.

A wata mahangar kuma bakan gizo wani muhimmin haske ne da yake bayyana a cikin giza-gizai a sararin samaniya wanda za ka ga ya yi lanƙwasa kamar misalin baka ya dangana daga kusurwa zuwa kusurwa. Shi dai wannan abu yana ɗauke da launuka daban-daban har kusan guda bakwai, mafi akasari yana bayyana ne lokacin da hadari ya taso, cikin ikon Allah da zarar bakan gizo ya bayyana, nan take za ka ga hadarin ya lafa ma’ana zai washe zuwa wani dan lokaci daga nan kuma sai ruwa ya kece. Amma mafi akasari wani lokacin sam ba za ma a yi ruwan ba.

Yadda bakan gizo yake samuwa

Bakan gizo yana samuwa ne lokacin da hasken rana ya wuce cikin ƙwayoyin ruwan sama da ke cikin iska. Wannan haske yana shiga cikin ruwan, ya karye (refract), ya watse (disperse), sannan ya dawo waje (reflect). Wannan juyawar haske ne ke haifar da jerin launuka masu kyau da muke kira bakan gizo.

Launukan bakan gizo

Akwai launuka bakwai a bakan gizo, waɗanda suke kamar haka:

  • Launin ja
  • Launin ruwan lemo (Matsakaicin ja da rawaya)
  • Launin Rawaya
  • Launin kore
  • Launin shuɗi
  • Launin shuɗin mai duhu
  • Launin ruwan hoda mai duhu ko shanshanbale

Bakan gizo a kimiyance

Masana ilimin kimiyya sun yi ruwa sun yi tsaki domin binciko mene ne haƙiƙanin bakan gizo, kuma daga ina yake, kuma me yasa yake bayyana, sannan kuma ta yaya yake bayyana.

Binciken ya tabbatar da cewa bakan gizo hasken rana ne da yake bayyana a sararin samaniya a wasu lokuta idan hasken rana ya ratsa ta cikin giza gizai masu ɗauke da feshin ruwa wanda ya haɗe da iska mai zafi.

Wannan shi ne abin da yake faruwa yayin da bakan gizo ya bayyana a sama, wato idan hasken rana ya ratsa ta cikin iska mai zafi ko giza-gizai masu ɗauke da feshin ruwa wanda ake kira “water droplet” a Turance, to sai muga bakan gizo ya bayyana.

Bakan gizo a al’adance

Bakan gizo a al’adance yana da ma’anoni masu zurfi a cikin tatsuniyoyi da labaran gargajiya. Wasu lokuta ana danganta shi da alamar albarka ko wani abu mai ban al’ajabi da ke faruwa bayan wani canji ko wahala (kamar ruwan sama).

Ana iya ganin bakan gizo ne kaɗai yayin da aka baiwa rana baya, shi ya sa idan bakan gizo zai bayyana da safe to sai dai a ga ya fito a yamma, idan kuma da yamma zai bayyana to sai dai ya fito ta gabas, kenan sai yayinda mai kallo ya juyawa rana baya ke nan kaɗai idanuwansa za su iya ganin bakan gizo. Ana kuma iya ganinsa ta hanyar amfani da na’ura ko kuma hanyoyin kimiya.

Bakan gizo ta wasu hanyoyi

Idan kana so ka gwada fitar da launukan bakan gizo za ka iya da kanka ba tare da amfani da na’ura ba.

Abu na farko da ake bukata shi ne ruwa sai a guntsa a baki sai a fita cikin hasken rana sai a fesa ruwan, ana fesawa ana kallon cikin feshin nan take za a ga launuka daban-daban sun bayyana makamancin na bakan gizo.

Ko kuma a sami madubi sai a ba wani mutum ya tsaya a cikin haske rana sai ya walwala hasken da ke cikin madubin zuwa cikin ɗaki ko dai wani lungu mai ɗan duhu sai a fesa ruwa a cikin hasken nan take za a ga launuka sun bayyana har da lanƙwasa kamar dai misalin yadda yake bayyana a sama.

Yanayin bakan gizo

Bakan gizo kamar sha-tale-tale siffarsa take wato “circle” amma mai gani ba zai iya ganinsa duka ba saboda ana iya hangensa ne daga nesa, idanuwanmu kuma ba za su iya kaiwa mu ga dukkan sashin kewayensa ba, shi yabsa muke ganinsa kamar baka.

Matsalolin bakan gizo

A cikin al’ada da kimiyya, bakan gizo ba shi da matsala kai tsaye domin ba wani abu ne da ake iya taɓawa ba. Abu ne da ke samuwa daga haɗuwar hasken rana da ruwan sama. Amma idan muna magana daga ɓangarori daban-daban, akwai wasu “matsaloli ko ruɗani” da ake dangantawa da bakan gizo:

Tsoro da ruɗani

A wasu yankuna, ana ganin bakan gizo a matsayin alama ce ta wani abin al’ajabi ko tsoro. Wasu na ɗauka cewa yana da alaƙa da fatalwa ko aljanu.

Hana nuna shi da yatsa

A al’adun Hausawa, ana wa yara gargaɗi kada su nuna bakangizo da yatsa, saboda ana jin hakan zai sa yatsarsu ya kumbura.

Matsala ga masu hoto

Sau da yawa, bakan gizo yana da wuya a ɗauke shi da kyamara saboda yanayin haske da saurin canjin iska. Idan rana ta rufe da gajimare ko iska ta canja, bakan gizo na ɓacewa cikin mintuna kaɗan.

Alama

A wasu ƙasashe, launukan bakan gizo ana amfani da su a matsayin tutar ‘yan luwaɗi da masu jima’i daban-daban (LGBTQ+). Wannan yana kawo muƙabala ko jayayya a tsakanin al’ummu masu aƙidu daban-daban.

Alfanun bakan gizo

  • A al’adu da dama, bakan gizo alama ce ta kyakkyawan fata, zaman lafiya ko albarka.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ana danganta bakan gizo da alƙawarin Allah bayan ruwan ɗufana.
  • A kimiyya, yana taimaka wajen fahimtar yadda haske da iska suka cuɗanya.
  • A cikin tatsuniyoyi da labaran gargajiya, bakan gizo na nufin wata halitta ce ko abin al’ajabi da ke da alaƙa da iska da ruwa. Wasu tsoffin labarai na cewa yana sha ruwa daga ƙasa ko sama sannan ya fitar da shi a wani lokaci.
  • A wasu lokuta, idan bakan gizo ya bayyana ba bayan ruwan sama, ana ɗaukar hakan a matsayin alamar albarka ko rahama daga Allah, musamman a ƙauyuka inda ruwa ke da matuƙar muhimmanci.
  • A wasu yankuna, ana ƙin nuna bakan gizo da yatsa, musamman ga yara, ana cewa yana iya kawo illa ko tsinuwa. Wannan ra’ayi yana da tushe a cikin gargajiya domin ƙarfafa ladabi da tsoron abubuwan al’ajabi.
  • A waƙoƙi da karin magana, ana amfani da bakan gizo a matsayin misali na kyau da launuka daban-daban. Misali: “Idonta kamar ruwan dorawa, fuskarta kamar bakan gizo.”

Manazarta

Contributors to Wikimedia projects. (2024, August 7). Bakan gizo. Wikipedia.

NOAA’s National Weather Service. (n.d.). How do rainbows form? 

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×