Skip to content

Barci

Barci wani yanayi ne na jiki wanda kan faru bisa al’ada da ke ba da dama ga ilahirin jiki da ƙwaƙwalwa su samu hutu. A duban farko, barci yana da sauƙi wajen yaudarar mutane. Ga mafi yawan mutane, barci hanya ce ta samun kwanciyar hankali da rufe idanu. Amma duk da yadda yake da sauƙi, barci yana ɗaya daga cikin mafi sarƙaƙƙiya yanayin tsarin jiki wanda kimiyya ke sani. Idan ba a samun isasshen barci ko ingantacce ba, wato ba a yi shi da kyau ba, tabbas za a gane hakan ta yadda za a ji sauyi a jiki. Rashin isasshen barci mai inganci kan haifar wa jiki da kwakwalwa su gaza yin aiki kamar yadda ya kamata.

child sleeping in bed 921x4810 1
Samun isasshen barci yana taimakawa wajen yin tunani mai kyau da fahimtar abu cikin sauri.

Barci ba yana nufin kasancewa a wani lokaci ko yanayi da ƙwaƙwalwa ba ta aiki kwata-kwata. Yayin da mutum ba shi da masaniya game da duniyar da ta kewaye shi, duk da haka akwai da yawan ayyukan ƙwaƙwalwa da za a iya ganowa. Wannan aikin ƙwaƙwalwa yana da sifofi masu iya tsinkaya. Masana sun tsara waɗannan alamu zuwa wasu matakai. Matakan sun kasu gabaɗaya zuwa kashi biyu: (Rapid eye movement (REM)) da kuma (None-Rapid eye movement (NREM)).

Matakin NREM

Akwai matakan NREM guda uku. Lokacin da aka yi barci, yawanci ana shiga matakin NREM mataki na 1 sannan ku zagaya tsakanin matakan NREM 2 da 3. Bayan haka, ana shiga matakin barcin REM. Bayan sake zagayowar matakin REM na farko, za a fara sabon yanayin barci sannan a koma mataki na 1 ko 2.

Zagaye ɗaya yana ɗaukar kusan mintuna 90 zuwa 120 kafin wani zagayen ya fara. Yawancin mutane suna yin kai huɗu ko biyar a kowane dare, wato sukan samu cikakken barci na sa’o’i takwas.

Mataki na 1 na NREM

Mataki na 1 a barcin NREM shi ne matakin mafi sauƙi na barci. Ana shigar da mataki na 1 daidai bayan kun yi barci. Wannan matakin yawanci yana ɗaukar mintuna kaɗan kawai, yana ɗaukar kusan kashi 5% na lokacin barci. Bayan haka, barci yana ƙara zurfi, yana kuma matsawa zuwa mataki na 2 na NREM barci.

Mataki na 2 NREM

A wannan mataki na 2, har yanzu dai barci ne mai sauƙi, amma ya fi mataki na 1 zurfi. A wannan mataki, jijiyoyin ƙwaƙwalwa suna raguwa kuma suna dakatawa. Kwararru suna tunanin waɗancan jijiyoyin ƙwaƙwalwar ne ke tsara abubuwan da za a iya tunawa da bayanai daga lokacin da aka farka.

Mataki na 2 na NREM yana ɗaukar kusan kashi 45% na lokacin barci, shi ne mafi yawan kowane mataki. Za a shiga zagaye da yawa na mataki na 2 na NREM a barci, kuma yawanci, kowannensu ya fi na ƙarshe tsayi. Bayan mataki na 2, ana matsawa zuwa mataki na 3 na NREM ko shiga matakin REM.

Mataki na 3 na NREM

Yanayi mafi zurfi na barci a matakin NREM shi ne mataki na 3. Yana daukar kusan 25% na jimullar lokacin barci ga manya. Amma jarirai da yara suna buƙatar ƙarin barcin mataki na 3, kuma idan suka girma, sai a samu ƙarancin buƙatar

A mataki na 3, jijiyoyin ƙwaƙwalwa suna da jinkiri amma suna da ƙarfi. Jiki yana amfani da wannan matakin barci mai zurfi don gyara raunuka da ƙarfafa tsarin garkuwar jiki. Haka rarrabuwar ayyukan ƙwaƙwalwa da ke faruwa a mataki na 2 na iya faruwa a mataki na 3, yayin da jijiyoyin ƙwaƙwalwa na musamman a mataki na 3 ke taimakawa wajen daidaita waɗannan rarrabuwar ayyuka.

Ana buƙatar mataki na 3 NREM barci don tashi hutawa. Idan ba a samu isasshen barcin mataki na 3 ba, za a ji gajiya da bushewar idanu ko da an yi barci na dogon lokaci. Wannan shi ne dalilin da ya sa jiki da kansa ke ƙoƙarin samun barci mai yawa na mataki 3 a cikin lokacin barci da wuri-wuri. Bayan mataki na 3 na NREM a barci, jiki yana matsawa zuwa mataki na 2 NREM, wanda shi ne mai tsaron ƙofar matakin REM barci.

Sakamakon mataki na 3 na NREM a barci yana da zurfi sosai, yana da wuya a tayar da mutum daga gare shi. Idan mutum ya farka, ƙila ya samu sami matsalar rashin barci, wannan yanayin ruɗani ne ko juwa. Wannan matsalar tana ɗaukar kusan mintuna 30.

Matakin REM

Rapid eye movement (REM) matakin barci ne, wannan mataki shi ne inda yawancin mafarki ke faruwa. Sunan matakin ya fito ne daga yadda idanu ke motsawa a bayan fatar ido yayin da ake mafarki. Yayin barcin REM, aikin ƙwaƙwalwa ya yi kama da aikin kwakwalwa yayin da ake farke.

Barcin REM shi ne kusan kashi 25% na jimullar lokacin barci. Zagaye na farko na REM na lokacin barci shi ne yawanci mafi gajarta, bai fi mintuna 10 ba. Duk wanda ya biyo baya ya fi na ƙarshe tsayi, har zuwa awa ɗaya.

Muhimmancin barci

Barci ba kawai lokacin da ƙwaƙwalwa da jiki suka rufe ba ne. Kwakwalwa da jiki suna aiwatar da ayyuka masu mahimmanci yayin barci waɗanda ke taimakawa a kasance cikin koshin lafiya da yin aiki mai kyau da inganci lokacin da aka farka. Barci tsari ne na halitta wanda jiki ke amfani da shi don hutawa da ingantawa.

Samun isasshen barci yana taimakawa wajen yin tunani mai kyau da fahimtar abu cikin sauri. A lokacin barci, jiki yana samar da ƙwayoyin hormones waɗanda ke taimakawa wajen gyara ƙwayoyin halitta da tantanin halitta da kuma yaƙar cututtuka.

Rashin samun isasshen barci na iya zama haɗari, ba kawai yana shafar aikin da mutum ke yi ba, har lafiya da yanayin mutum na samun matsala. Nazarin ya nuna cewa rashin barci na iya haifar da:

Ƙarancin fahimta da mantuwa

  • Shiga haɗari ko yanke shawarar da ba ta dace ba
  • Yawan yin fishi haka kawai
  • Samun saɓani abokanan hulɗa
  • Kasancewa cikin baƙin ciki a sauƙaƙe
  • Haifar da hawan jini, cututtukan zuciya, ciwon sukari da sauran matsalolin lafiya
  • Matsanancin nauyi da ƙiba

Adadin barcin da jiki ke bukata

Adadin barcin da jiki ke buƙata ya dogara da shekaru mutane. A nan an kawo ƙa’idoji na yau da kullun ga adadin barcin da ya kamata mutum ya yi:

  • Jarirai watanni 4 zuwa 12 suna bukatar jimullar barcin awanni 12 zuwa 16, da ya haɗa da barcin rana.
  • Yara shekara 1 zuwa 2 suna bukatar jimullar barcin awanni 11 zuwa 14, da ya haɗa da barcin rana.
  • Yara shekara 3 zuwa 5 suna bukatar jimullar barcin awanni 10 zuwa 13, da ya haɗa da barcin rana.
  • Yara shekara 6 zuwa 12 suna bukatar jimullar barcin awanni 9 zuwa 12, da ya haɗa da barcin rana.
  • Yara shekara 13 zuwa 18 suna bukatar jimullar barcin awanni 8 zuwa 10.
  • Manya shekara 18 zuwa sama suna bukatar jimullar barcin awanni 7 ko fiye.

Waɗannan alƙaluman adadin barcin ya shafi yawancin mutane, amma ba gabaɗaya mutanen duniya ba. Wasu mutane suna buƙatar ƙarin barci, wasu kuma suna buƙatar ragi. Bambance-bambancen yawan barcin da ake buƙata na iya zama na halitta. Alal misali, wasu mutane na iya gadon yin barci kaɗan daga iyayensu.

Halin mutum da yanayin lafiya na iya shafar yawan barcin da yake buƙata. Mutanen da ba su da lafiya ko suke murmurewa daga rauni ko cuta na iya buƙatar ƙarin lokacin barci. Masu juna biyu galibi suna buƙatar ƙarin lokacin barci a cikin farkon watanni uku.

Dabarun yin rarci

Idan ana fuskantar wahalar yin barci ko kuma barci mai wahala, a bi waɗannan shawarwari:

  • A kula tare da kiyaye jadawalin barci na yau da kullun. A kwanta a tashi a lokaci guda kullum.
  • A shakata a yi walwala kafin kwanciya barci.
  • A yi wanka da ruwa mai dumi kafin kwanciya barci.
  • A kula sosai da lokacin sanyi a cikin ɗakunan kwana, a samar da kyakkyawan yanayi.
  • A kau da abubuwan da ke ɗaukar hankalin mutum daga barci, kamar talabijin, hayaniya ko fitilu masu haske.
  • A guji shan barasa kafin barci. Yayin da barasa zai iya taimaka maka barci, ba ya taimaka maka barci.
  • Kada a ci abinci ko abin sha da yawa kafin barci don kada barcin ya haɗu da aikin narkewar abinci ko buƙatar fita fitsari.
  • Samun akalla mintuna 30 na hasken rana kowace rana. Hasken rana yana taimakawa wajen daidaita yanayin barci.
  • Kada a kwanta a kan gado alhali ba a fara jin barci ba. A tashi a yi wasu ayyukan har sai an ji alamar barci.

Biyan bashin barci

Bashin barci shi ne bambanci tsakanin adadin ingantaccen barcin da ake samu da adadin ingantaccen barcin da ake buƙata. Wannan zai iya haifar da ji gajiya fiye da ta al’ada, kuma ana iya jin buƙatar yin barci da yawa don hutawa.

Bincike ya nuna cewa bashin barcin da ake tarawa yana da matsala, ba abu ba ne mai kyau. Biyan bashin wannan barcin da aka rasa ba zai taimaka wajen kawar da tasirin bashin da aka tara ba. Misali ɗaya shine yadda bashin barci zai iya shafar metabolism (wato na’urorin jiki da ke aikin fitar da gurɓatattun abubuwa daga jiki), yana ƙara haɓakar ciwon sukari na 2 da sauran batutuwan lafiya. Akwai shaida cewa ko da an samu barcin da aka biya bashin, waɗannan na’urori na iya samun matsala sakamakon bashin barcin.

Manazarta

Ms, J. L. (2025, January 16). 5 reasons to get more sleep.Healthline.

Mayo Clinic: (n.d) 6 steps to better sleep. Mayo Clinic.

Suni, E., & Suni, E. (2024, May 13). How much sleep do you need? Sleep Foundation.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa
<p>You cannot copy content of this page</p>