Skip to content

Bikin budar dawa

Bikin Buɗar dawa biki ne da Hausawa suka daɗe suna aiwatarwa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa. Bukin yana da sunaye daban-daban, wasu kan kira sa bikin buɗin daji, wasu kuma su ce bikin shekara. Manyan bokaye da ‘yan bori da manyan mafarauta su ne ke kan gaba wajen aiwatar da bikin. Akan yi bikin ne da rani kafin saukar ruwan sama. Waɗannan mutane suke jagorantar bikin. Sukan nemi wani dutse ne a cikin daji domin tattaunawa a tsakaninsu inda za su yi duba ta hanyar harba kibiya sama.

hq7207

Shi wannan bikin ana yin sa ne shekara-shekara don neman tsari daga bala’o’in wannan shekarar. Akan yi duba, don gano abin da shekarar ke tafe da shi, ko na alheri ko na sharri alfarmar da wasu hallitu suke da shi wajen Bahaushe.

Yadda  ake aiwatar da Buɗar dawa

Yadda ake aiwatar da shi wannan biki na Buɗar dawa shi ne da zarar damina ta wuce, bayan wata huɗu (a ranar sha huɗu ga wata) ake yin wannan biki tun kafin lokacin za a sanar da mutanen gari da na kauyuka, wato dai ana karaɗe gari ne da shela tare fadin ranar da za a yi. Haka zalika za a fitar da ƙauyen da za a gudanar da wasan tare da dajin da za a aiwatar.

Waɗanda kuwa suke lissafin watannin ɗaukewar ruwa  da ranakun wata sukan san ranar tun kafin ta zo. Tun kafin ranar jama’a za su yi ta taruwa a garin da za a yi Buɗar dawar, idan ana gobe za a yi bikin, da La’asar sai manyan manoma da bokaye da maharba a karkashin shugabancin babbansu su fita su kewaye dajin da za a yi farauta a cikinsa.

A ranar da za a yi bikin da sassafe  sai manya da sauran jama’a tare da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe za su tasar wa dajin domin yin farauta. Idan an fita duk dabbar da aka fara cin karo da ita sai a kashe a kawo a gaban manya. Bayan sun yi al’adar da za su yi sai su sa a feɗe dabbar da aka yo farautar a gaban jama’a, da zaran an feɗe sai a fito da tumbinta sai manyan su zauna nazarin kayan cikin tumbin don su gane abin da zai faru a shekarar a dalilin dubiya da za su yi wa tumbin da nazarin sa.

Idan an fede wannan dabbar akan sami abubuwa da damar gaske cikin wannan dabba ko da kuwa ƙarama ce, fitattu daga cikin irin abubuwan da ake samu cikin dabbar da ke nuna musu abin da shekarar ke tafe da shi sun hada ne da:

  • Ƙwari (ko a mace ko masu rai)
  • Ruwa (mai yawa ko kaɗan)
  • Yayi/Ciyawa (ko danya ko busasshiya)

Ƙwari (ko a mace ko suna da rai)

Da zaran an fede wannan dabbar, kuma aka samu kwari ne a cikin wannan dabbar to wannan kwarin sukan dauki matsayi biyu ne wato ko su kasance masu yawa ne kuma masu rai kadan ne daga ciki matattu, ko kuma masu yawa ne amma matattu daga cikinsu sun fi yawa. Idan ya kasance kwarin an same su da rai ne to wannan yana nuna musu cewa a wannan shekarar da za su shiga ba za a samu yawan cututtuka da mace-macen jama’a ba. Idan kuma an sami kwarin da yawa ne kuma matattu daga cikinsu sun fi yawa, to wannan yana nuna musu cewa a wannan shekarar da za su shiga za a samu yawan cututtuka da mace-macen jama’a.

Ruwa (mai yawa ko kaɗan)

Wannan na daya daga cikin abin da dan Adam yake dogaro da shi wajen gudanar da harkokinsa na rayuwa. A yayin gudanar da bikin budar dawa na Hausawa na gargajiya, akan sami ruwa wani lokaci, domin kuwa shi ma yana daya daga cikin abubuwan da Hausawa ke auna mizanin abin da shekara ke tafe da shi a yayin bikin budar dawa.
Da zaran wannan dabbar an fede, kuma aka samu ruwa ne a cikin to zai tabbatar musu daya cikin abu biyu ne wato ko damina mai labarka za a samu a wannan shekarar ko kuma daminan ba za ta yi albarka ba, domin kuwa wannan ruwan kan dauki matsayi biyu: mai yawa ko kadan ne.

Idan ruwan mai yawa ne to wannan yana nuna musu cewa a wannan shekarar da za su shiga za a samu damina mai albarka wannan shekarar domin ruwan zai wadata kuma ba zai yi musu barna ba. Idan kuma ruwan da aka samu ya kasance kadan ne a cikin dabbar da aka farauto, to wannan yana nuna musu cewa a shekarar za a yi fari ne, domin ruwa ba zai yawaita ba. Ta wannan hanya ne suke gane abin da wannan shekarar ke dauke da shi na sharri ko na alheri.

Ciyawa/yayi (ko danye ko busasshe)

Wannan ita ma tana daya daga cikin abin dubawa yayin gudanar da bikin budar dawa na Hausawa na gargajiya. Domin akan sami ciyawa wanda Hausawa ke auna mizanin abin da albarkar abinci da wannan shekara ke tafe da shi a yayin bikin budar dawa.

Da zarar wannan dabbar an fede ta, kuma aka samu ciyawa ne a cikin to zai tabbatar musu daya cikin abu biyu ne wato ko amfanin gona zai yi yabanya a wannan shekarar ko kuma ba za ta yi albarka ba, domin kuwa in ciyawan ya dauki matsayi biyu: wato mai yawa ko kadan ne. A bushe take ko danye?

Idan ciyawar mai yawa ce kuma danya to wannan yana nuna musu cewa a wannan shekarar da za su shiga za a samu amfanin gona mai albarka domin ciyawan yana da yawa. Idan kuma ciyawan da aka samu ya kasance kadan ne a cikin dabbar da aka farauto kuma busasshe, to wannan yana nuna musu cewa a shekarar za a yi karancin abinci ne, domin abinda za a noma ba zai wadata mutane.

Ta wannan hanya ne suke gane abin da wannan shekarar ke dauke da shi na sharri ko na alheri game da abinci.

Bayan waɗannan mutanen sun gudanar da wannan binciken domin gano abin da wannan shekarar ke dauke da shi, wannan dabbar da aka fede za a dafa, a yi dage-dage, kuma kowa a wannan gari zai yi kokari ya samu ya ga ya ci wannan naman ko da tsoka daya ne wasu kuma koda romon ne su samu su sha. To a ganinsu duk wanda bai samu wannan naman ko romon wannan dabbar ba zai iya fadawa cikin wannan matsalar da wannan shekarar ke tafe da shi. Saboda haka ‘Yan bori da maharba suke girmama wannan biki.

Bayan an gama karanta abin da ke cikin tumbin, sai kuma a shiga rabon naman zuwa kungiyoyin mutane. Kowa zai ƙoƙarin ya sami naman dabbar nan komai ƙanƙantarsa, wanda ya sami naman sai ya kai gida a saka cikin girkin abincin gidansa. Irin wannan abinci idan an gama ana raba wa dangi kowa ya samu ya ci, sun ce cin irin wannan abinci  da ake yi da wannan nama zai tsare wanda ya ci daga sharrin cututtuka da masifun wannan shekara.

Irin wannan biki ya ragu bayan zuwan musulunci amma har yanzu ana yin shi a birnin Ƙwanni cikin jamhuriyar Niger.

Waɗanda ke gudanar da bikin

Mutanen da ke aiwatar da biki na Buɗar dawa kuwa kamar yadda bayani ya gabata an ga cewa Manoma ne da Mafarauta tare da Bokaye ke aiwatar da shi. Sannan mutanen gari su mara masu baya domin aiwatar da shi.

Dalilan yin bikin buɗar dawa

Dalilqn da suke sawa ake gudanar da bikin Buɗar dawa su ne kamar haka:

  • Domin riga kafin kariya daga cututtuka
  • Domin samun kariya ga al’ummar gari daga masifu da bala’o’in shekara
  • Domin bunƙasa tattalin arziki
  • Domin samar da ƙarin haɗin kai tsakanin al’umma
  • Domin sada zumunta tsakanin mutanen cikin gari da na ƙauyuka

Tasirin bikin ga al’ummar Hausawa

Tasirin wannan biki ga al’ummar Hausawa a bayyane yake domin kuwa tun tali-tali an san Malam Bahaushe da farauta da noma, hakan ya sa ake ganin lallai Buɗar dawa yana da tasiri a cikin Hausawa.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page