Camfi na nufin mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to, ya gaskata wani abin zai faru da shi a dalilin wannan hasashen da ya yi. Camfi shi ne ƙudurcewa da mutum ya ke yi a zuciyarsa cewa idan ya aikata wani aiki, ko ya faɗi wata magana, ko wani abu ya faru da shi, to sakamakon faruwar wannan abin, wani abu kuma daban, wanda ka iya zama kakkyawa ko akasin haka na iya faruwa da shi.
Wasu masana kuma cewa suka yi, “Camfi wata hanya ce ta ƙudurce aukuwa ko faruwar wani abu da sakamakonsa zai iya zama mai kyau ko mai alheri ko mai muni.”
Saboda haka idan aka yi la’akari da waɗannan maganganu game da ma’anar camfi, za a iya fahimtar cewa, camfi ƙuduri ne da ake gina shi a kan zato. Saboda, zato ne ake yi cewa idan aka yi wani abu, ko aka faɗi wani abu, da sauran su, to wani abu na iya faruwa. Babu tabbas cikin faruwar wannan abun.
Camfi dai a takaice, hanya ce ta zato da Bahaushe ya gina kansa a kan ta dangane da faruwar wasu abubuwa. Camfi, na daga cikin munanan al’adun da Bahaushe yake da su tun dauri. Bahaushe yana aƙidantuwa da zace-zace da ya yi dangane da faruwa ko afkuwar wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa.
Ire-iren camfi
1. Camfin lokaci: Wannan camfin a kan lokaci yake magana. Misali ba a barin ƙaramin yaro a bakin garka da mangari. Wai in an bar shi yana iya gamo da iskoki/aljanu.
Hakan game da camfin lokaci Hausawa kan kudurec cewa, ba a tafiya daji da rana tsaka. Idan an yi shi ma ana iya gamo da aljanu.
2. Camfin rana: Wannan camfin shi kuma a kan rana Hausawa suka rataya shi. Misali, ba a tafiya ranar Talata. Idan an yi da wuya a samo nasara da sauran su.
3. Camfin tafiya: Shi kuma wannan nau’in camfi a kan tafiya Hausawa suke yin shi. Misali. Ba a fita gida lokacin sallar Magriba. Tana iya yiyuwa a kan hanya a haɗu da aljanu za su gida.
4. Camfin zama: Camfi ne a kan zama Hausawa suka ɗora shi. Misali. Ba a zama bakin dangarma. Idan aka zauna ragon ƙafa kan ture mutum.
5. Camfin cin abinci: Shi ne camfin da ya shafi abinci.. Misali Hausawa na cewa, ba a cin abinci a tsugunne. Idan ana ci zubewa yake a ƙasa, wai ba a koshi.
A wannan zamanin da muke ciki, mafi yawa daga cikin Hausawa ’yan bana-bakwai, ba su san ma me ake kira da camfi ba, don haka, mun kalato wasu daga cikin irin wadannan camfe-camfe domin kafa misali da su, musamman domin raya Adabin Hausa.
Misalan Camfe-Camfe
- Idan mutum ya kashi da safe, zai samu arziƙi a wannan rana.
- Idan mutum ya zauna a ƙofar ɗaki, aljanu suna iya bugunsa.
- Idan mutum ya ji ƙafarsa tana ƙaiƙai, to zai yi tafiya.
- Idan mutum ya ji hannunsa na dama yana ƙaiƙayi, zai samu arziƙi.
- Ga wasu daga cikin camfe-camfen Malam Bahaushe:
- Idan mutum yana lashe bayan ludayi, zai yi sanko.
- Idan mutum yana zama a kan murhu, to zai haifi da maye.
- Idan mace mai ciki tana zuwa dibar ruwa a kogi da dare, ’yan ruwa za su musanya mata dan da za ta haifa da aljani.
- Idan namiji yana zama a kan kujerar mata, to zai haifi ’ya’ya mata da yawa.
- Idan mace mai ciki ta tsallaka wurin da aka yi fitsari, to sai ta yi bari.
- Idan karamin yaro yana cin kwai, to zai yi sata.
- Duk wanda ya sha ruwan da gyartai ya sha ya rage, to zai yi arziki sosai.
- Cin abinci a tsugune, yana sa abincin ya ki zama a cikin mutum, wato ya zurare.
- Bai wa yara ruwan farko na damina, yana hana su yin laulayi.
- Idan mutum ya yi mafarki yana cin abinci, to zai ji wata muguwar yunwa a gaba.
- Idan aka shafa wa yaro jinin cibiyarsa a kan dasashi, ba shi ba kashin hakori.
- Idan aka soya busasshen kashi aka shafe jikin yaro da shi, yaron ba zai yi kyanda ba.
- Idan ka yi mafarkin kashi ko kuma mafarkin cewa ka fada masai, to za ka samu kudi a wannan ranar.
- Idan kana kwana daki daya da kuturu, idan gari ya waye ka riga shi fita daga dakin, to za ka zama kuturu.
- Duk macen da ta shiga rumbu, to za ta haifi barawo.
- Idan namiji ya taba jelar zomo, sannan ya shafi gaban wandonsa, to zai rasa mazakuntarsa.
- Idan ka shafa kwantsar doki a idonka, za ka iya ganin aljannu, amma fa za ka mutu.
- Duk wanda tsawa ta kashe, za a saka shi a Aljanna.
- Idan kana tafiya kuma kana cin abinci, to tare da Shedan kuke ci.
- Idan mutum ya yi dariya a lokacin da yake mafarki, to wani abu da zai sa shi kuka zai faru a gare shi.
- Idan direba ya banke kyanwa ko kare ko agwagwa da wani abin hawa, to wani mummunan abu zai same shi.
- Idan mutum ya ci kan bera, to zai zama barawo.
- Idan mace mara aure ta duba madubi da dare, to za ta rasa mijin aure.
- Idan mace ta yi mafarkin maciji ya cije ta, to ta sami shigar ciki ke nan.
- Idan mutum ya yi mafarkin shanu da giwaye ko wasu muggan namun daji, to maye ne ya kama shi ko kuma yake neman kama shi.
- Duk wanda ya fara hada ido da mai ido daya da safe, to a ranar ba zai samu ko anini ba kuma ba wanda zai ba shi ko anini.
- Idan mutum ya kwanta barci tare da yin filo da wandonsa, to zai yi mummunan mafarki.
- Duk wanda ya yi shara da dare, to sa’arsa ya ke sharewa.
- Idan mace ta haihu, to a sami danbida a sakaye a shinfidar jaririn, idan ba haka ba, to ’yan ruwa za su musanya jaririn.
- Idan aka yi barin gishiri, to a yi sauri a share shi, idan ba haka ba, matar gidan da mijin ba za su taba zaman lafiya ba.
- Duk ranar Laraba, a kife kaya gudun kar aljanu su yi ma fitsari.
- A daina barin kwandon wanka a waje, idan ba haka ba kuwa aljanu su dauka su yi wanka da shi.
- Idan mai takaba ta zauna a tabarma, to kar ka zauna, domin wani abu na iya faruwa da kai.
- Idan mutum ya bari wani mai yin shara ya share masa kafa, to zai rasa mai aurensa.
- Cin kasa ga karamin yaro yana kara masa kwarin gwiwa, idan kuwa ba a bar shi ya ci ba tun lokacin tatata, ba zai yi kwari ba.
- Idan mutum yana kwana daki daya dam aye zai iya zama maye shi ma, domin kurwarsa takan fita daga jikinsa duk dare, ta tafi farauta. Kuma idan ta dawo cikin rashin sa’a tana iya jikinka.
- Duk wanda aka kira sa sau daya ko biyu in har bai amsa ba, in an kai uku, to zai haukace ko kuma wani abu ya same shi.
- Wanda ya kwanta cikin hasken farin wata, mura za ta kama shi.
- Wanda ke zama a dankarin kofa zai zama gurgu.
Dukkan waɗannan misalai na camfe-camfe da suka ƙunshi ƙudurori, zato ne kawai da buruka. Don haka wannan al’ada ba ta da kyau. Kuma masana sun yi gargaɗi da a nuisance ta.
Manazarta
Paki, S. I. (2021, November 27). Camfe-camfe guda 50 da Hausawa suka yi amanna da su. Aminiya.
Rumbum Ilimi. (n.d.). Camfi a ƙasar Hausa Rumbum Ilimi
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.