Ciwon zuciya dai ciwo ne da ke kama zuciya ya addabi rayuwa gabaɗaya. Wannan ciwon na faruwa ne ya yin da jijiyoyin zuciya suka yi rauni ko kuma suka yi tsauri, abin da zai hana su harba jini ga sauran sassan jiki. Har ila yau masana a fannin kiwo lafiya sun bayyana ciwon zuciya da cewa ciwo ne da yake faruwa a sanadiyar gazawar jijiyoyin zuciya wajen aika jini zuwa ga sassan jiki kamar yanda sassan jikin ke bukata.
Ciwon zuciya ciwo ne mai wuyar sha’ani da ɗaga hankali wanda mafi akasari yana faruwa ne a lokacin da wani ɓangare na tsokar zuciya bai sami wadataccen jini ba. Saboda toshewar magudanan jini da ake kira da arteries, wato jijiyoyin da ke dakon jini daga zuciya zuwa sassan jiki. Hakazalika waɗannan magudanan jini su ne dai jijiyoyin da ke dakon isar da iskar oxygen da jini da abubuwan inganta jiki zuwa tsokar zuciya. Idan aka samu toshewarsu, wani yanki na tsokar zuciya zai iya daina aiki ko ya mutu gabaɗaya saboda rashin iskar oxygen, wanda ke zama silar kamuwa da ciwon zuciya. A yayinda haka ta kasance, masu fama da ciwon kan yi galafaita, wanda kan iya kai su ga rasa rayuwarsu.
Wannan ciwo na zuciya yana daga cikin manyan ƙalubalen kiwon lafiya a cikin al’ummar yau, domin kuwa yana ɗaya daga cikin miyagun cutukan da ke laƙume rayuka a duk faɗin duniya. A kowace shekara, miliyoyin rayuka ake rasawa ta dalilin kamuwa da wannan cuta. Ciwon zuciya shi ne mafi girma wajen kawo ajalin mutane da dama a ƙasashe masu arziki, domin an yi kiyasin cewa a kowane rabin minti mutum guda na mutuwa a sanadiyar ciwon zuciya a ƙasashen Yamma, duk da cigaban da suka samu a fannin kiwon lafiya musamman cututtukan zuciya da aikin tiyatarta.
Alamomin kamuwa da ciwon zuciya
Kasala
Rashin kuzari da yawan jin kasala na daga cikin alamomin ciwon zuciya wanda zai iya kai mutum ga kasa yin wani aikin. A cewar masana, hakan ya sanya a lokacin ciwon zuciya jinin da ke zagayawa a zuciya yakan ragu tare da sanya jin gajiya a damtse.
Karancin numfashi
Za a riƙa jin raguwar numfashi, misali idan aka hau bene za a riƙa yin haki. In har ana jin wannan yanayi na yin numfashi da kyar da jin gajiya bayan an yi ‘yar tafiya, to hakan alama ce da ke nuni da an kamu da bugun zuciya.
Zafi mai radadi a zuciya
Wata alamar ciwon zuciyar kuma shi ne za a riƙa jin zafi mai raɗaɗi a zuciya, wanda kuma ba lallai ne ya cika damun mutane ba, don haka a tabbatar da an tuntuɓi masana kiwon lafiya domin wannan alama ce ta bugun zuciya kuma hakan yana hana jini yawo zuwa zuciya.
Lalacewar ciki
Bugun zuciya wani lokacin yakan janyo lalacewar ciki kamar jin amai, saboda hakan yakan faru ne dalilin wani irin nau’in abinci da aka ci.
Bayyanar ƙuraje a baya da ƙirji da damtsen hannu
Bayyanar ƙuraje yana haifar da raɗaɗi a waɗannan wurare, jin kuwa alamomi ne na an kamu da ciwon zuciya kuma hakan yana janyo rashin fitar iska saboda kasancewar jijiyoyin jini a toshe.
Rashin jin daɗin makogoro ko wuya ko mukamuki
Yana daga cikin alamomin ciwon zuciya ko bugun zuciya a dinga jin rashin daɗi a maƙogwaro ko a wuya ko kuma a muƙamuƙi, wanda kuma ba a saba jin irin sa a baya ba. Saboda haka mutane masu fama da ciwon zuciya sukan mayar da hankali a dukkan wani canji da suka ji a jikinsu.
Rabe-raben ciwon zuciya
Ciwon zuciya na hawan jini
Hawan jini na kawo ciwon zuciya, sai dai hakan na faruwa ne idan hawan jinin ya ɗaɗe a jikin mutum ba a sauko da shi ba ta hanyar shan magunguna waɗanda za a iya samu a asibiti.
Mai ɗauke wannan ciwo zai iya jin numfashi sama-sama, musamman idan ya kwanta, wanda hakan kan sa mutum kwanciya da matashi biyu ko uku. Numfashi sama-sama zai iya sa mutum ya kasa barci, domin da ya kwanta sai ya ji kamar an shaƙe shi. Sai kuma a fara tari, da kumburin ƙafafuwa. Wani lokaci akwai ciwon ƙirji.
Ciwon zuciya na ƙwayoyin cuta
Ƙwayoyin cuta daba-daban kan samu damar shiga cikin zuciya su samu wurin zama idan jini ya kwaso su daga wasu sassan jiki musamman waɗanda suke daga baki da maƙogwaro, su sa wa zuciya. Akwai irin wannan ciwon zuciya da ƙwayoyin cuta kan kawo har iri biyu, wato ‘Rheumatic Valvular Heart Disease’ mai kama murafan zuciya da ‘Infective Endocarditis’ mai kama tsokar naman zuciyar.
Ƙwayar cutar bakteriya ita ta fi samun sukuni a jikin zuciya, duk da cewa ƙwayoyin irin su virus da fungus sukan iya sa wa zuciya ciwo.
Ciwon zuciya na haihuwa
Akwai ciwon zuciya wanda ake haifar jarirai da shi, kuma yana da nau’ika guda biyu; mai tsanani da marar tsanani. Mai tsanani shi ne wanda wasu jariran ma ba sa kwana, da zarar an haife su suke komawa. Nau’i marar tsanani kuma shi ne wanda jariri zai rayu har ya girma da shi ba tare da ma an gane ba.
Alamomin da za a fahimta jariri na da wannan ciwo ya danganta da tsanani ko rashin tsananin ciwon. Wani lokaci ba wata alama da ake gani, kuma hakan na nufin yaro zai iya rayuwarsa lafiya ba tare da matsala ba. Wani lokaci kuma, akan ga wasu alamomi waɗanda suka haɗa da yawan haki, ko kuma ya kasance jariri ba ya iya shan nono sosai, idan ya sha kaɗan sai ya huta sannan ya ƙara sha, ko a ga leɓensa yana yin duhu ko baƙi-baƙi maimakon launin hoda.
Ciwon zuciya na ciwon hunhu
Akwai kuma nau’in ciwon zuciya wanda ciwo a hunhu ne kan haifar, wato idan aka samu matsala a hunhu matsalar takan iya shafar zuciya. Cututtukan hunhu da za su iya sa ciwon zuciya sun haɗa da ciwon tarin fuka, da ciwon daji na hunhu, wanda ya fi kama masu shan taba sigari.
Ciwon zuciya na ƙiba
Kiba tana lahani ga zuciya idan daskararren mai ya toshe magudanan jini da suke zagaye da zuciyar, don su ne suke ba ta nata kason na jini. Idan hakan ta faru ɓangaren da abin ya shafa a jikin zuciyar zai iya mutuwa, ya kuma jawo matsala ga zuciyar bakiɗaya. Yawancin masu ƙiba kuma suna da hawan jini, wanda hakan kan haɗu ya ƙara wa zuciya ciwo.
Babbar alamar da ake ji idan irin wannan ciwon ya kama mutum shi ne ciwon tsakiyar ƙirji, daidai saitin da zuciya take. Ciwon ya fi tashi idan aka ɗan yi wani kazar-kazar, ko aka ji mummunan labari.
Abubuwan da ke barazana ga kamuwa da ciwon zuciya
Damuwa
Matsananciyar damuwa da yawaita tunani, yawan fishi kodayaushe, wannan matsala ce da kan iya haifar da ciwon zuciya.
Hawan jini
Babu shakka hawan na iya lalata jijiyoyin jini da ke kaiwa ga zuciya a kan lokaci. Hawan jini da sauran cututtuka suna ƙara haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.
Ciwon sukari
Idan sukarin cikin jini yana tashi lokacin da jiki ba ya samarwa ko amfani da sinadarin insulin na hormone yadda ya kamata, to yawan sukarin jinin yana janyo afkuwar ciwon zuciya.
Shan taba sigari
Wannan ya haɗa da shan tabar da kuma shaƙar hayaƙinta na dogon lokaci, suna barazanar haifar da ciwon zuciya.
Nau’in abinci
Abincin mai yawan sinadarin sigari da kitsen dabba da abinci mai yawan maiƙo da gishiri ba shakka suna ta’azzara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya.
Tsufa
Tsufa ko yawan shekaru shi ma na zama dalilin kamuwa da ciwon zuciya. Maza masu shekaru arba’in da biyar (45) da mata ‘yan sama da shekaru hamsin da biyar (55) sun fi shiga haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.
Gwaje-gwaje ciwon zuciya
Ana gano ciwon zuciya ta hanyar lura da hawan jini, bugun jini, da zazzabi. Ana yin gwaje-gwaje don tantance yadda zuciya ke bugawa da kuma tantance lafiyar zuciya gabaɗaya. Gwaje-gwajen na’urori da ake yi don gano ciwon zuciya sun haɗa da:
1. Ɗaukar hoton ƙirji (X-ray)
Ɗaukar hoton kirji yana nuna yanayi da girman zuciya da hunhu. Ana amfani ne da na’urar lantarki a asibitoci domin ɗauka da bincika ƙirjin marar lafiya.
2. Electrocardiogram (ECG)
Wannan gwaji ne da ake yi don gano ciwon zuciya da kuma lura da na’urorin da ke aiki a cikinta. Ana sanya na’urar (electrodes) a ƙirjin marar lafiya, a wasu lokutan kuma hannaye da ƙafafu.
3. Gwajin jini
Gwajin ya kasance hanya da masana kan bi don gano cutukan da ke damun mutane daban-daban. Ciwon zuciya ma na daga cikin cutukan da ake iya bincikowa ta hanyar gwajin jini. Bayan ciwon zuciya, wasu sinadaran zuciya suna ci gaba da sauka cikin jini. Ana iya gano waɗannan sinadaran ta amfani da gwajin jini.
Ku karanta maƙala game da yadda zuciya take da ayyukanta.
Manazarta
BBC News Hausa. (2015, May 25). Ciwon zuciya na da alaka da bacin rai. BBC Hausa News
Garba, I. (2018, July 14). Alamomi 7 da za ka fara ji idan ka kamu da ciwon zuciya. ISYAKU.COM.
Kiranmayi, P. (2022, May 26). Ciwon Zuciya: Alamu, Dalilai, Dos da Don’t, Jiyya. Medicover Hospital