Ƙyanda cuta ce da ke haifar da zazzaɓi da ƙuraje. Tana da saurin yaduwa kuma tana yaduwa ta iska lokacin da mai cutar kyanda ke magana, tari ko atishawa. Cutar ƙyanda wasu ƙwayoyin cuta ne da akasari iska suke bi, sai a shaƙe su idan an yi tari ko atishawa. Wasu ƙwayoyin cuta ne da ‘birus’ ne ke kawo su.
Tun da aka samar da maganin allurar riga-kafi, cutar kyanda ba ta tasiri kamar kafin a samu riga-kafin. Duk wanda ba a yi masa allurar rigakafin cutar kyanda ba yana cikin hadarin kamuwa da ita.
Ƙwayoyin cutar sun fi kama yara ’yan ƙasa da shekaru biyar waɗanda garkuwar jikinsu ba ta yi ƙwari ba. An kiyasta cewa dubban yara ne kan riga mu gidan gaskiya da dama sakamakon ciwon.
Alamomin ciwon ƙyanda
1. Zazzabi mai zafi.
2. Ido ya yi ja yana ƙaiƙayi ko zafi
3. Tari da atishawa
4. Rashin jin daɗin jiki
5. Bayyanar wani fari-farin abu kan harshe.
6. Leɓe yanayin ja.
7. Ƙuraje a jiki wanda galibi ba su cika yin ƙaiƙayi ba amma suna bayyana bayan alamomin farko
Alamun ciwon su ne da farko yaro zai fara ciwo kamar mura, har idanu su riƙa yin ruwa suna yin ja, daga nan sai zazzabi, yaro ya kasa cin abinci.
Bayan haka sai wasu ƙananan kuraje su feso masa duk jikin, har baki. Daga nan kuma ko dai jiki ya yaƙi ƙwayoyin cutar, ko kuma su ci gaba da jawo lahani. Misali, daga maƙogwaro har cikin kunne sukan iya shiga su kawo ciwon kunne. A ido ma sukan iya huda farin ido, idan suka shiga ƙirji kuma su kawo numoniya.
Sai an ɗauki matakin ƙarawa yaro kaifin garkuwar jiki kafin ya iya shawo kansu. Duk wannan yakan ɗauki misalin sati biyu yaro na fama. Yara masu karyayyar garkuwar jiki kamar masu ciwon ƙanjamau da ciwon suga ke nan sun fi shan wahala, tun da jikinsu yakan ɗauki lokaci mai ɗan tsawo yana yaƙar su.
Amma idan yaro yana da ƙwarin garkuwar jiki ba za a ma gane ƙyanda ba ce, domin ’yar mura kawai zai yi ta kwana uku zuwa huɗu ya warke. Wasunsu ma ko murar ba sa yi, amma za su iya sa wa wani. Ita ce ake kira da bi-iska.
Wurin da cutar ke fitowa
Ƙurajen ƙyanda na fitowa a sassan jiki yan kwanaki bayan sauran alamominta sun bayyana. Ƙurajen na fitowa a kan fuska da bayan kunnuwa kafin su bazu zuwa sassan jiki. Suna wahalar gani a baƙar fata.
Matsalolin ƙyanda
Matsalolin da suka fi tsananta sakamakon ƙyanda akwai ciwon kunne da gudawa. Wasu mutanen na iya fama da matsalolin da suka tsananta kamar cutar sanyi ta pneumonia da kumburin ƙwaƙwalwa da ake kira encephalitis a Ingilishi da kuma makanta. Daga cikin matsalol ko kuma illolin cutar ƙyanda sun haɗar da:
1. Makantarwa.
2. Kurumtarwa.
3. Sa jiki yin baki ko dabbara-dabbara wanda bai cika barewa ba.
4-Askewar gashi
5-Shaƙewar murya ko ɗaukewarta baki ɗaya.
Waɗanda ke kamuwa da cutar Ƙyanda
Kowa na iya kamuwa da cutar ƙyanda babba da yaro matuƙar dai ba a yi riga-kafi ba, sai dai cutar ta fi tasiri tsakanin yara ƙanana.
Ana iya yin cutar ƙyanda sau biyu?
Abu ne dake iya faruwa sai dai kuma ba lallai ba ne, matukar dai an yi riga-kafin da ya kamata.
Waɗanda cutar ta fi wahalarwa
Cutar na iya wahalar da duk wanda ta kama sai dai kuma bincike ya tabbatar ta fi wahalar da waɗannan matakin shekarun,
• Yara ‘yan shekaru 5
• Mutanen da suka haura shekara 20.
• Mata masu ciki
• Mutanen da ba su da sinadaren kariya mai ƙarfi a jikinsu, kamar masu fama da Cuta mai karya garkuwar jiki ko kansar jini.
Kariya
Hanyoyin kariya daga wannan cuta kan fara tun daga lokacin da aka haifi yaro. Idan aka ba jariri nonon uwa zalla har wata shida ba ko ruwa, to garkuwar jikinsa za ta fi ta sauran yara ƙarfi, ta yadda ba zai riƙa cutuka sosai ba.
Sai kuma allurar riga-kafin ita ƙwayar cutar da ake yi a wata tara. Yawanci waɗanda suke yin ciwon ba a yi musu allurar riga-kafin ba.
Sauran hanyoyin kariya sun haɗa da saurin kai mai ciwon asibiti da ware masa wurin kwanciya daban da na sauran yaran gida don kada ya yada musu.
Samar masa soson wanka nasa na daban don kada ruwan majina ko na ƙurajen jikinsa su sa kwayoyin cutar a jikin soson. Sai kuma yawan wanke hannayen yaran gidan da sabulu. Ko makaranta mai ciwon bai kamata ya je ba tsawon ’yan wadannan kwanakin da yake ciwon, don kada ya yada ta.
Riga-kafin Allurar MMR
Wannan maganin ya haɗu da riga-kafin kyanda-mumps-rubella tare da maganin kaji (varicella). Masana kiwon lafiya suna ba da shawarar yin allurai biyu na riga-kafin MMR ga yara. Ana yin allurar farko lokacin da yara suka kai watanni 12 zuwa 15. Yawancin lokaci suna buƙatar allura ta biyu lokacin da suke da shekaru 4 ko 5. Idan ba a yi wa yaro riga-kafin ba, har yanzu ana iya hana cutar kyanda ta hanyar karbar maganin a cikin kwanaki uku da kamuwa da cutar.
Manazarta
BBC News Hausa. (2024, January 25). Alamomin kamuwa da cutar ƙyanda. BBC Hausa News.
DeStefano, F. (2003). Vaccinations and risk of central nervous system demyelinating diseases in adults Archives of Neurology, 60(4), 504.
Professional, C. C. M. (n.d.-a). Measles. Cleveland Clinic.
World Health Organization: WHO. (2024, April 16) Measles. World Health Organization