Skip to content

Dandalin sada zumunta

Kowace kwanan duniya fasaha sai daɗa bunƙasa take yi, wannan kuwa na faruwa ne saboda hazaƙar bil’adama daya samo dandalin sada zumunta don samar wa kai sauƙi cikin harkokin yau da kullum.

Takaitaccen tarihin dandalin sada zumunta

An samu ra’ayoyi mabambanta dangane da samuwar asalin dandalin sadarwa na Intanet. Amma masana kamar su Hafner da lyon (1996;116) sun bayyana cewa dandalin sadarwa na Intanet ya samu ne a kasar Rasha, hakan kuma ya faru ne a sanadiyyar yaki da kasar Rashar ta fafata a wancan lokaci. Sun kuma yunkura yin haka ne da niyyar samun saukin isar da sakonni wa dakarunsu a filin daga. Kumbon sako na farko da kasar Rashar ta soma cillawa cikin sararin samaniya a kokarin cim ma wannan buri nata shi ne ”Sputnik”.

A dayan bangaren kuma a ƙoƙarin nuna bajintarta na samar da kumbon da ya fi na farko da kasar Rasha ta cilla, kasar Amurka, ta cilla wani kumbon sako da ake kira (ARPA) da zai rika samar mata da bayanai dangane da tsaro cikin karamin lokaci wanda kuma ya sha ban-ban da na kasar Rasha a cikin shekara ta 1958, karkashin Hukumar Rundunan Tsaronta.

The top 5 social media platforms you should focus on
Wasu daga cikin muhimman shafukan sada zumunta a yau.

Berners wani masani ne mai kuma bincike da ya bayyana cewa, a shekara ta 1983, kasar Amurka, ta fadada harkar sadarwa inda kumbon sako na “ARPA” ta samu sauyin suna zuwa “ARPANET” duk wannan dai a kokarin samar wa soji da farar hula damar isar da sako ba tare da cikas ba. A shekara ta 1990, ne kafar samar da bayanai ta “ARPANET” ta zama ta amfanin farar hula don gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Kim shi kuma ya bayyana cewa a shekara ta 1995, ne kafar samar da bayanai ta Intanet ta shiga sahun saura da suka hada da Usenet da Fidonet da  kuma Mintel, amma ta fi sauran tasiri nesa ba kusa.

Harkar sadarwa ta dandalin abota na Intanet ta ci gaba a kasar Rasha a shekara ta 1989, wannan dandalin sadarwa da ake kira Vkonte na da tasiri kwarai ba a kasar Rasha kadai ba hatta sauran kasashen Turai sun yi na’am da dandalin, ganin ya samar da damar yin mu’amala da yaruka iri daban-daban. A yanzu dai wannan dandali na da mambobi fiye da miliyan 239.

Haka ma kasar Amurka ta yi rawar gani wajen samar da dandalin sada zumunta da suka samu karbuwa sosai kamar su; Facebook da Mark Zuckerberg wani dalibi a Jami’ar Harvard ya kirkiro a shekara ta 2004 don sada zumunta. Bayan wannan dandali na Facebook akwai kuma dandalin sada zumunta kamar haka:

  • Dandalin X (Twitter).
  • Dandalin Google.
  • Dandalin Pinterest.
  • Dandalin Instagram.
  • Dandalin Youtube.
  • Dandalin 2go
  • WhatsApp da dai sauran su.

Ma’anar dandalin sada zumunta

Dandalin sada zumunta wata sabuwar duniya ce da ba mu gama sanin hakikaninta ba, duniya ce mai cike da annashuwa da raha da saukin sadarwa da saukin rayuwa da saukin mu’amala da saukin sadarwa da saukin abota da hanyoyin samun fadakarwa da gabatar da harkokin rayuwa ce a wani tsari mai kama da hakika, kai ba kama ba ne rayuwa ta hakika ce.

Dandalin Facebook

Dandali ne da ya faro a shekara ta 2004 daga Mark Zuckerberg, wani dalibi a  Jami’ar Harvard da ke Amurka, daga shekara ta 2004  zuwa  shekara ta 2007, dandalin ya samu karbuwa matuka a wajen daliban makarantun sakandare da kwaleji da kuma sauran Jama’a. A yanzu yana da mambobi masu rijista a duniya sama da biliyan 1.2, kashi 25 cikin masu amfani da shafin Facebook ba su damu  da kariya ba, kuma a duk wata a kalla mutum miliyan 800 ne ke shiga dandalin Facebook, mutum miliyan 488 ne kuma ke mu’amala da shafin Facebook ta wayar salula. Sama da kashi 23 kan shiga shafin ne sau biyar a duk yini, haka ma akan shigar da hotuna sama da miliyan 250 a duk rana. Kashi 80 cikin 100 na masu neman hajojin kasuwanci sun fi son samunsu ta hanyar dandalin Faceebook, kashi 43 cikin masu mu’amala da shafukan Facebook maza ne, a yayin da sauran kashi 57 din mata ne.

Alfanun dandalin sada zumunta kan rayuwar matasa

Bunkasar kimiyyar sadarwa da fasahar sarrafa bayanai, daidai da karshen karnin da ya gabata, wannan sabuwar duniyar tsarin sadarwa ta Internet, wanda a farkon lamari ta faro da ‘yan kwanfyutocin da ba su shige dari ba, amma a halin yanzu akwai sama da biliyan uku masu dauke da bayanai da muke aikawa tsakaninmu. Samuwar fasahar Intanet da yadda bunkasarta ta kasance abu ne mai cike da mamaki ga duk wanda ya san asalin lamarin, amma bai kai irin mamakin da ke dauke da sabuwar duniyar da ta tsiro a cikinta bayan ‘yan shekaru kasa da goma da suka shige ba.

Jonah A (2013) ya bayyane cewa akwai matasa da yawa a dandalin Faceebook, tsakanin ‘yan mata da samari da tsofaffi da zawarawa da gwagware da tuzurai duk sun yi rijista kuma suna sada zumunci iya gwargwado. Babban abin da ya sawwake yaduwarsu a wannan dandali kuwa dalilai ne guda biyu.

  • Abu na farko shi ne samuwar wayar salula a hannun jama’a, wanda ya zama gama gari da duniya baki daya.
  • Abu na biyu shi ne saukin mu’amala wanda ya sa duk wanda ya shiga sau biyu ba ya bukatar wani darasi kuma.

Daga cikin amfanin da matasa ke samu a dandalin Facebook da sauran dandalin sada zumunta sun hada da:

  • Akwai yin abota da samar da sanayya mai amfani da amfanarwa, da fahintar rayuwa ta hanyar kallon yadda wasu ke tafiyar da rayuwarsu a duniyar da suke.
  • Akwai kuma samartaka tsakanin’yan mata da samari da koyon addini da siyasa da raha da fadakarwa da hayaniya iri- iri.

Kuma, akwai majalisu da matasa suka kafa, masu amfani sosai, akwai zaurukan tattaunawa na musamman masu alfanu kwarai da gaske.
Akwai kuma shafukan gwaraza da suka bude don koyi da su da kuma karantarwarsu, haka ma akwai zaurukan zumunta na musamman, wasu daga cikinsu sun hada da:-

  • Zauren sahabban manzon Allah, inda matasa na koyon harkokin addini daga masana addinin musulunci don samun ilimin addinin ganin ilimin addinin na da tasiri a rayuwar kowani mutum.
    Dandalin tambayoyin addinin musulunci da zauren sunna da sauransu.
  • Akwai dandalin marubuta da ke hada kan marubuta don kara wa juna sani dangane da sabbin dabarun rubutu don dasawa daidai da zamani a fagen rubuce-rubuce. Duk wannan adadi, tsakure ne cikin daruruwan shafuka da zaurukan da matasa suka bude kuma suke aiwatar da sadarwa a tsakanisu a wannan dandali.

Wannan dandali ya bai wa matasa wata sabuwar hanyar fadakarwa da karantarwa da tunatarwa da kuma gayyata, wannan tsari ya samar da wata hanya ta gayyatar biki, ko suna ko taro ko duk wani sha’ni na yau da kullum

A bangaren siyasa ma haka abin yake, kowa na bayyana ra’ayinsa yadda yake so ba tare da tsangwama ba, wannan kadan ne daga cikin amfanonin da matas ke samu a wannan dandali.

Dandalin na taimaka wa matasa su yi kyakkyawar sani wa aboka da suke mu’amala da addininsu da alkiblar rayuwarsu. Wanda hakan kan ba su haske na yadda za su ci gaba da mu’amala da su ba tare da wasu munanan halayyan abokan nasu ya yi tasiri a kan rayuwarsu ba.

Bugu da kari idan matasa da ke da kunyar gaske sun shiga hulda a dandalin sada zumunta sukan yi nasarar shawo kan wannan matsala ta kunya daga mu’amala da suke yi da abokai, ganin wani zai iya bayyana irin halin da yake ciki a shafin dandalin, hakan zai sa ya samu amsa daga duk wadanda suke abota da shi a dandalin, ta haka wasu matasa da dama sun sami mafita daga matsaloli da suka addabi rayuwarsu.

Matsalolin shafukan sada zumunta

Duk da cewa shafukan sada zumunta sun kawo fa’idoji da dama da haɗin kai, haka nan kuma suna da ƙalubale da rashin amfani. A nan ga wasu manyan illolin shafukan sada zumunta:

Shashantarwa

Amfani da dandalin sada zumunta a lokutan aiki ko lokutan karatu yana shashantar da wasu mutanen ga barin ayyukansu masu muhimmanci. Wasu mutanen kan shafe awanni da dama a shafukan sada zumunta daga nan zuwa can ba tare da sun sani ba, yayin da a hannu guda kuwa suna da muhimman ayyuka ko karatu.

Yaɗa jita-jira

Yada labarai na karya, farfaganda da bayanan da ba a tantance ba marasa tushe na iya batar da sahihan bayanai. Kafafen sada zumunta na zanani sun zama wani dandali na yada labaran ƙanzon kurege, wannan yana haifar da shakku ga sahihancin labarai da bayanai ko da kuwa na gaskiya ne.

Satar bayanai

Muusayar bayanan sirri da satar bayanai yana kawo nakasu ga sirrin masu amfani da shafukan, wannan matsala takan haifar da zamba da damfara.

Cin zarafi da tsangwama

Shafukan sada zumunta wurare ne da suka yi shura wajen cin zarafi mutane da cin mutuncinsu ciki har da mashahuran mutane da suka haɗa da Malamai, shuwagabanni Masana da sauran su. Wannan mummunar dabi’a tana da sauƙin aiwatarwa a shafukan sada zumunta duba da cewa waje ne da aka ba wa koda da dama ya shiga.

Haifar da damuwa

Bincike ya nuna cewa amfani da kafafen sada zumunta na da nasaba da dalilan da ke kawo cutar damuwa, musamman a tsakanin matasa. Matasan da kan shafe lokaci mai tsayi a shafukan sada zumunta sukan ci-karo da abubuwan ɓacin rai wanda kan jefa su cikin matsanancin yanayin damuwa.

Yaɗa zamba

Labaran karya, hare-haren masu kutse da tsare-tsare na iya yaɗuwa cikin sauƙi ta hanyoyin da ke haifar da zambar kuɗi. Mutane da dama sun faɗa tarkon irin wadannan miyagu masu aikata wannan baƙar ta’ada.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page