Facebook kafar yanar gizon sadarwar zamantakewa ce inda masu amfani da kafar za su iya yin sharhi, raba hotuna har da labarai ko wasu abubuwan ban sha’awa da taɗi kai tsaye, da kallon bidiyo na gajeren lokaci. Ana iya samun damar raba abubuwa a bainar jama’a, ko kuma ana iya raba su tsakanin zaɓaɓɓun rukunin abokai ko dangi ko ma tare da mutum ɗaya kacal.
Samuwar Facebook
Facebook ya fara ne a cikin watan Fabrairu na shekarar 2004, a matsayin cibiyar sadarwar zamantakewar makaranta a Jami’ar Harvard. Mark Zuckerberg ne ya kirkiro shi tare da Edward Saverin, duka ɗaliban kwalejin ne. Sai a shekara ta 2006 Facebook ya buɗe wa duk wanda ya kai shekaru 13 ko sama da haka damar mallakar gurbi a cikin manhajar. Cikin sauri, Facebook ya wuce MySpace a matsayin cibiyar sadarwar da ta fi shahara a duniya.
Ana iya danganta nasarar da Facebook ya samu ne saboda yadda ya iya jan hankalin mutane da kasuwanci da kuma yadda yake iya mu’amala da shafukan yanar gizo ta hanyar samar da mashiga guda ɗaya da ke aiki a cikin shafuka da dama.
Me yasa Facebook ke da farin jini?
Facebook yana da sauƙin amfani kuma yana ba da dama ga kowa. Ko da mafi ƙanƙantar masu tunani, za su iya shiga su fara yin rubutu a kan Facebook. Ko da yake ya fara ne a matsayin hanyar ci gaba da tuntuɓa ko sake haɗuwa da abokan da aka daɗe da haɗu ba, cikin sauri ya zama mai farin jini ga kasuwanci da isar da tallace-tallace kai tsaye ga mutane.
Facebook ya sauƙaƙa raba hotuna, saƙonnin rubutu, bidiyo. Shafin yana nishadantarwa kuma tasha ta yau da kullun ga masu amfani da yawa.
Ba kamar wasu shafukan sada zumunta ba, Facebook baya barin abin da bai dace ba. Lokacin da masu amfani suka yi ƙetare iyaka, kuma aka ba da rahoton, za a dakatar da su daga amfani da shafin. Misali, ba da jimawa ba mutane sun kai rahoton shafin sada zumunta na mawaƙi Dauda Kahutu, wanda ya wallafa wata waƙarsa da ake zargin ta harzuƙa mutane, a daidai lokacin da ake kukan tsadar rayuwa. A nan take kamfanin Facebook ya karɓi koken kuma ya garƙame shafin.
Facebook yana ba da tsarin adana sirri wanda za a iya daidaita shi, ta yadda masu amfani za su iya kare bayanansu daga isa ga mutane.
A shekarar 2023, Facebook ya samu ribar dala biliyan 39A. An saukar da Facebook sama da sau biliyan biyar.
Abubuwan ban sha’awa
Ga kadan daga cikin abubuwan da suka sa Facebook ya shahara sosai:
- Facebook yana ba da damar kiyaye jerin abokai kuma zaɓi saitunan keɓantawa don daidaita wanda zai iya ganin abin da kuka saka.
- Facebook yana ba da damar ɗora hotuna da adana kundin hotuna waɗanda za a iya rabawa tare da abokai.
- Facebook yana ba da damar yin taɗi ta onlayin da damar yin tsokaci a kan shafukan bayanin abokai don ci gaba da tuntuɓa, raba bayanai da sauran su.
- Facebook yana goyan bayan shafukan rukuni, shafukan magoya baya, da shafukan kasuwanci waɗanda ke amfani da Facebook don tallar hajarsu.
- Cibiyar haɓakawa ta Facebook tana ba da ayyuka na ci gaba da damarmakin samun kuɗi.
- Ana iya watsa bidiyo kai tsaye ta amfani da Facebook Live.
- Yin taɗi tare da abokai na Facebook da ‘yan uwa, ko nuna hotunan Facebook kai tsaye tare da na’urar Portal ta Facebook.
Mallakar gurbi a Facebook
Domin kasancewa cikin maziyarta biliyan 2 da ba za su iya nisantar Facebook ba, yi rajista don samun gurbi a Facebook kyauta, kuma a cike bayanai da hotuna, sannan a nemo mutanen da aka sani don fara abota.
Kurkukun Facebook
Gidan kurkukun Facebook shi ne lokacin da masu amfani suka rasa damar yin tsokaci da turawa a kan Facebook na ɗan lokaci, wato suka gaza samun damar yin amfani da shafin. Wani lokaci, gidan yarin Facebook na iya zama asusun mai amfani an dakatar da shi na dindindin ko kuma na har abada.
Facebook Lite
Facebook Lite manhajar Facebook ce ta wayoyin Android. Yana amfani da ƙasa da bayanai fiye da na yau da kullum wato na asali, kuma an tsara shi da farko don tsofaffin fasahohin sadarwa na 3G da 2G. Wannan sigar app ɗin ita ce mafi kyau ga masu amfani da tsofaffin wayoyi da fakitin sabis.
Mark Zuckerberg, wanda ya mamaye duniya lokacin da ya kafa Facebook, ya sanar a hukumance cewa katafaren dandalin sada zumunta za su canza suna.
Canjin ya zo ne ta hanyar sake fasalin, yayin da suke neman nisantar da kamfanin daga takaddamar da ta kunno kai a cikin ‘yan shekarun nan.
Meta shi ne sabon kamfanin da aka kirkira a cikin 2021 don mamaye Facebook da sauran kayayyaki da sabis na kamfanin, kamar Instagram, WhatsApp, Oculus, da sauransu.
Zuckerberg ya yi bayanai masu yawa game da wannan sauyi, ya yi ikirarin cewa yana son kamfanin ya yi aiki don ya zama ɗaya tamkar da dubu. Ga wani ɓangare na abin da yake cewa.
“Bayan lokaci, ina fatan ana ganin mu a matsayin kamfani mai ban sha’awa kuma ina so in daidaita aikinmu da ainihin mu akan abin da muke ginawa.
“Yanzu muna duba da bayar da rahoto kan kasuwancinmu a matsayin sassa biyu daban-daban, ɗaya don danginmu na apps, ɗaya kuma don aikinmu a kan tsari na gaba.
“Kuma a matsayin wani ɓangare na wannan, lokaci ya yi da za mu ɗauki sabon tambarin kamfani don haɗa duk abin da muke yi, don nuna ko su wane ne mu da abin da muke fatan ginawa.”
“Na yi imani cewa metaverse shi ne babi na gaba don intanet.”
Bambancin Facebook da Meta
- Babban bambanci shi ne Facebook yanzu kamfani ne na reshe a ƙarƙashin babbar inuwar Meta.
- Facebook ya kasance babban dandalin sada zumunta, yayin da Meta shi ne babban kamfanin wanda ke sarrafa Facebook da sauran manyan kayayyaki da tsare-tsaren kamfanin, kamar aikin Metaverse.
- An zaɓi Meta a matsayin sabon sunan kamfanin don nuna fifikon ƙungiyar kan haɓaka “metaverse” – ƙayyadaddun bayanai na intanet wanda kamfanin ke hasashe a matsayin babban dandamalin kwamfuta na gaba.
- Yayin da Facebook ya kasance sanannen aikace-aikacen kafofin watsa labarun, Meta shi ne babban haɗin gwiwar fasaha wanda ke kula da Facebook da sauran sassan kamfanin da ke aiki a kan fasaha da gogewa masu alaƙa.
Manazarta
Business of Apps. (2024, April 18). Facebook Revenue and Usage Statistics (2024)Business of Apps.
Statista. (2024, May 21). Facebook: quarterly number of MAU (monthly active users) worldwide 2008-2023. .
The Guardian. (n.d.). Facebook