Skip to content

Fatalwa

Kalmar “Fatalwa” tana nufin wani irin haske ko wata inuwa, ko kuma alama da mutum ke iya gani, wanda ba na gaske ba ne, kamar wahami ko mafarki da ido biyu. Ma’ana ta cikin tunaninsa ko kuma zuciyarsa. A wasu lokuta, ana iya danganta shi da al’amuran ruhanai ko abubuwan da suka shafi bokanci.

3d33f1b8a9950efd
Fatalwa na iya bayyana a siffofi daban-daban.

Fatalwa za ta iya kasancewa wani makwafi ne na rayuwar kowa ne ɗan Adam da ka iya bayyana bayan mutuwarsa. Bi sa wasu dalilai. Wannan zai iya tabbatar da cewa kowa ma a duniya yana da fatalwar kansa da kansa. Hausawa sun yi imani da samuwar fatalwa, wadda ba mutum ba ce cikakke, kuma ba dabba ko gunki ba ce. A al’adarsu, fatalwa na iya kasancewa ƙasusuwan mutum kawai, ba tare da fata, tsoka, ko jijiya ba.

Haka kuma a wata mahangar a al’adar Hausawa, fatalwa wata halitta ce da ake jin tana da alaƙa da mutane da suka mutu, amma ba mutum ba ce gabaɗaya. Akwai imani cewa fatalwa na iya bayyana a dalilai daban-daban kamar son rai, ƙiyayya, buri, ko tasirin wani wuri da aka yarda yana da iskoki matattu. Hausawa na ɗaukar fatalwa a matsayin abu mai ban tsoro, wanda ke iya cutarwa ko firgita mutane. Duk da haka, akwai lokuta da ake ganin fatalwa tana bayyana saboda ƙauna, kamar rakiyar masoyi ko nuna buri da ba a samu ba a rayuwa.

6044759262942070562 UHD
Hausawa sun yi imani da wanzuwar fatalwa.

Ana danganta fatalwa da ruhi, tsafi, ko al’adu masu alaƙa da rayuwa bayan mutuwa a cikin addinin gargajiya. Kodayake addini irin na Musulunci ya yi tasiri kan imani irin wannan, har yanzu akwai wasu da ke ci gaba da jin tsoron fatalwa a wasu sassan daban-daban. Yayin da wasu ma har yanzu ba su yarda da wanzuwarta ba.

Siffofin fatalwa

Fatalwa tana da siffa ta musamman wadda ta bambanta da mutum na zahiri. Ga wasu daga cikin siffofinta:

  • Ƙasusuwa: Fatalwa ba ta da fata, tsoka, ko jijiya, sai kaso kawai. Wannan yana sa ta zama abin firgitawa.
  • Siffar Mutum: Duk da da cewa fatalwa kaso ne kawai, tana iya kama da mutum ta tsayinta da kuma girmanta.
  • Rashin magana: Fatalwa ba ta magana da mutane, sai dai ta yi shiru ko ta firgita mutum.
  • Tafiya babu hayaniya: Fatalwa tana iya tafiya ba tare da an ji sautin tafiyarta ba, wanda ke ƙara wa mutane tsoronta musamman cikin dare.
  • Ana yawan cewa fatalwa tana fitowa da dare ko a wuraren da ba kasafai ake zuwa ba, kamar duwatsu, dazuka, ko kangwaye.

Dalilan samuwar fatalwa

A al’adar Bahaushe ana ganin cewa akwai dalilan da ka iya haifar da samuwar fatalwa ko kuma wanzuwarta a doron ƙasa. Wannan dalilai sun haɗar da:

  • Lokaci: Idan mutum ya mutu ba tare da ya gama rayuwarsa ba, ana tunanin zai iya dawowa a matsayin fatalwa.
  • Ƙiyayya: Maƙiyi na iya zama fatalwa domin ɗaukar fansa idan aka yi masa cuta ko aka hana shi haƙƙinsa ko kuma wani abu makamancin haka.
  • Ƙauna: Soyayya mai tsanani na iya sa a yi fatalwa domin ganin masoyi ko rakiyar mutum a hanya.
  • Buri: Idan mutum ya mutu da burin samun muƙami ko aure, ana cewa zai iya yin fatalwa domin cimma wannan buri na sa.
  • Waibuwa: Iskokin wuri ko matattu da aka hana haƙƙinsu na iya zama fatalwa domin hana wasu cin gajiyar wurinsu.

Illolin da ke tattare da fatalwa

A al’adar Hausawa, ana danganta fatalwa da matsaloli daban-daban da ke shafar rayuwar mutane. Ga wasu daga cikin matsalolin da ake dangantawa da fatalwa:

Firgita mutane

Fatalwa na haifar da tsoro da firgici, musamman ga waɗanda suka yi imani da samuwarta.

Cutarwa ko haukatawa

A wasu labarai, ana cewa fatalwa na iya cutarwa, ta firgita mutum har ta haddasa masa ciwo ko hauka. Domin zai dinga bayanin yana ganinta tare da bayyana yanayin yadda take zuwar masa. Amma kuma wanda yake sanarwa su ba sa ganinta. Daga nan wasu za su soma yi wa mai ganin fatalwar kallon mahauci ko kuma maƙaryaci.

Shafar wurare

A wasu lokuta, ana jin tsoron cewa fatalwa na zaune a wasu wurare, musamman gidajen da aka bari, dazuka, ko ruwan da aka ce yana da ruhika. Wannan kan hana mutane amfani da irin waɗannan wurare saboda tsoro. Ko da ba a taɓa ganinta ido da ido ba.

Ayyukan da fatalawa ke aiwatarwa

A al’adar Hausawa, ana danganta fatalwa da wasu aiyuka da ake ganin suna shafar mutane ta hanyoyi daban-daban. Ga wasu daga cikin ayyukan da ake cewa fatalwa na yi:

  • Ana cewa fatalwa na bayyana a wurare masu duhu da ban tsoro, musamman wurin da ya shafi daji, maƙabarta. Shuri ko kuma kango da wuri mai yawaitar bola.
  • Yana daga cikin aikin fatalwa shi ne: Ɗaukar fansa. Idan mutum ya mutu cikin zalunci ko kuma ana ganin an hana shi hakkinsa, ana cewa zai iya dawowa a matsayin fatalwa don ɗaukar fansa ga wanda ya cutar da shi.
  • A wasu labarai, ana cewa fatalwa na iya bayyana ga masoyi da ya mutu yana ƙaunarsa, ko dai domin ya raka shi hanya ko ya bayyana a mafarkinsa.
  • Idan fatalwa tana zaune a wani gida ko wuri, ana cewa tana hana wasu zama ko cin gajiyar wurin, ta hanyar firgita su ko hana su kwanciyar hankali.
  • A al’adar gargajiya, ana cewa wasu sarakuna da suka mutu suna dawowa a matsayin fatalwa don tsoratar da waɗanda suka gaje su, musamman idan ba su amince da su ba.
  • Ana cewa fatalwa na iya bayyana kamar mutum na gaskiya, sai daga baya a gane cewa ba mutum ba ce, domin ba ta magana ko kuma ba ta yi inuwa ba

Waɗannan ayyukan suna ƙara wa imanin Hausawa ƙarfi, tare da haifar da tsoro da gujewa wuraren da ake zargin akwai fatalwa.

Wuraren da lokacin fatalwa take bayyana

Ana yawan danganta fitowar fatalwa da wasu lokuta da wurare na musamman. Ga wasu daga cikin yanayin da ake cewa fatalwa ta fi fitowa:

Dare

Ana cewa fatalwa na fitowa da dare, musamman daga tsakar dare zuwa asuba. Wannan na sa mutane su guji fita a wannan lokaci, musamman a wuraren da ake zargin akwai fatalwa.

Tsohon wuri

Gidaje da aka daɗe ba a zauna a cikinsu ba, ko kuma inda aka ce wani ya mutu da wata matsala, ana ganin suna iya zama mafakar fatalwa.

Dazuka da Rugage

Wuraren da ba kasafai mutane ke zuwa ba, kamar dazuka da rugage, ana cewa fatalwa na iya bayyana a can, musamman ga manoma ko masu yawon dare.

Ruwa

Ana yawan danganta fatalwa da wuraren ruwa kamar rafuka, ƙoramu, ko tafkuna. Hausawa na cewa wasu ruhohi na rayuwa a cikin ruwa kuma suna iya bayyana a matsayin fatalwa.

Maƙabarta

Ana yawan jin labarai cewa fatalwa na iya bayyana a wuraren jana’iza ko maƙabarta, musamman idan ana zargin wanda aka binne bai samu kwanciyar rai ba.

Fatalwa a mahangar kimiyya

A Kimiyancce fatalwa tana nufin wani abu da yake da alaƙa da kimiyya, wato bincike, gwaje-gwaje, ko bayanai masu tushe a ilimin zamani. Idan muna haɗa su wuri guda, (Fatalwa a kimiyance) hakan zai iya yin nuni ne ga yadda kimiyya take bayani ko bincike kan fatalwa ko kuma shin su na wanzuwa da gaske, ko kuma kawai abubuwa ne da mutane ke hango wa saboda wasu dalilai.

A kimiyance, fatalwa ba ta da wata shaidar da za a iya gwadawa a kimiyya, amma akwai bayanai da bincike da ke ƙoƙarin bayyana dalilan da ke sa mutane su ce sun ga fatalwa. Ga wasu bayanai masu danganta hakan.

Hassashe

Wasu mutanen na iya ganin hotuna ko jin muryoyi ba tare da sun gan su a gaske ba, saboda hassashen da ƙwaƙwalwarsu kan kwao musu. Wannan na iya kasancewa sakamakon gajiya, matsanancin tsoro, ko cututtuka kamar sleep paralysis (cutar matsin bacci). Idan mutum yana cikin damuwa ko fargaba, ƙwakwalwarsa na iya ƙirƙirar hotuna da babu wanzuwarsu a duniya ma baki ɗaya kuma ya dinga zahirantar da su a cikin tunaninsa.

Tasirin yanayi da kuma haske

A wasu wurare, musamman gidajen tarihi ko tsofaffin gine-gine, canjin yanayi na iya haifar da hayaƙi ko iska da ke motsa abubuwa, wanda ke sa mutane su ɗauka cewa fatalwa ce. Akwai wani sinadari da ake kira carbon monoxide (CO) wanda ke fitowa daga tsofaffin dumama-gidaje. Idan ya taru, yana iya sa mutum ya fuskanci halucinoci.

Tsoro da ƙwarewa

Idan aka haifi mutum a cikin al’ummar da suka yi amana da fatalwa, yana iya ganin abubuwa ta yadda al’adarsa ta ko ya masa. Mutanen da suka yi imani da fatalwa sun fi iya hango su fiye da waɗanda ba su da wannan imani.

Fatalwa a mahangar addini

A mahangar addinai da dama, bayanai daban-daban, suna duban fatalwa da ma’anoni da tafsirai masu yawa, kuma yawancin su suna da alaƙa da ruhin matattu ko aljannu. Ga yadda wasu manyan addinai ke fassara fatalwa:

Musulunci

A Musulunci, babu wata fatalwa da take yawo kamar yadda ake tsammani a labaran almara. Duk wani abu da ake kira fatalwa, a fahimtar addini, yana iya kasancewa:

Aljannu

Waɗanda Allah ya halitta daga wuta, kuma suna iya bayyana ga mutane a wasu lokuta.

Ruhin matattu

A Musulunci, an yi bayani cewa idan mutum ya mutu, ruhinsa yana cikin barzahu, ba ya dawowa duniya. Don haka, duk wani abu da ake kira fatalwa, yana iya zama aljani mai kwaikwayon mamaci.

Kiristanci

A Kiristanci, akwai ɓangarori da suka yarda da wanzuwar fatalwa a matsayin ruhin mutanen da suka mutu waɗanda ba su huta ba, ko kuma suna buƙatar addu’a don samun natsuwa.

Wasu ɓangarori na Kiristanci suna yarda cewa wasu fatalwa na iya zama ruhin mugaye da Shaiɗan ke amfani da su don yaudara. A wasu lokuta, ana danganta su da mala’iku ko aljanu, bisa ga yadda suka bayyana.

Addinan Gargajiya

A wasu al’adun Afirka, ana yarda cewa ruhin magabata na iya dawowa su ziyarci ‘yan uwansu, ko don su kare su ko kuma don su nemi haƙƙinsu.

A addinin gargajiyar China, kwai aƙidar “Hungry Ghosts” (fatalwar da ke buƙatar abinci da addu’a), wanda ake yi wa bukukuwa domin samun salama.

Manazarta

Abubakar, M. (1999). Adabin Baka da Rayuwar Hausawa. Northern Nigerian Publishing Company.

Ado, H. (1985). Tasirin Camfe-Camfen Hausawa Cikin Tarbiyyarsu. Ahmadu Bello University Press.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. Oxford University Press.

East, R.M. (1939). Hausa Superstitions and Customs. Niger Press, Kaduna.

Muhammad, A.S. (2001). Tatsuniyoyi da Al’adu na Hausawa. Gaskiya Corporation, Zaria.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page