Gusau Institute cibiyar nazari da bincike ce da ke jihar Kaduna, Najeriya, wacce aka kafa domin inganta zaman lafiya, tsaro, da ci gaba a nahiyar Afrika. An kafa cibiyar ne bisa ga hangen cewa Afrika na buƙatar cibiyar falsafa da koyarwa mai inganci, wacce ke da hangen duniya amma kuma tana da fahimtar yanayin Afrika.

Ayyukan cibiyar Gusau Institute
Daga cikin ayyukanta, Gusau Institute tana shirya tarukan ƙarawa juna sani da tattaunawa kan batutuwa kamar tsaro. Misali, a watan Fabrairu na 2025, cibiyar ta shirya taron tattaunawa a Abuja kan makomar ECOWAS, wanda ya samu halartar manyan shugabanni ciki har da tsohon shugaban ƙasar Najeriya Janar Yakubu Gowon da wasu tsofaffin shugabannin ƙasashen yammacin Afrika.
Bugu da ƙari, Gusau Institute tana gudanar da gasar rubuce-rubuce ga marubutan Hausa, wacce aka fi sani da “Gasar Gusau Institute”.
Cibiyar tana da ƙasaitaccen dakin karatu da bincike mai suna Aliyu Mohammed Research Library, wanda ke da tarin littattafai da kayan tarihi masu muhimmanci ga masu bincike da masu sha’awar ilimi.
Gusau Institute tana taka muhimmiyar rawa wajen haɓɓaka ilimi, tsaro, da shugabanci a Najeriya da ma Afrika baki ɗaya, ta hanyar shirye-shiryenta na ilimi da tattaunawa mai amfani.
Gasar Gusau Institute
Gasar Gusau Institute wata gasa ce da aka samar a tsakanin marubuta, ake kuma gudanar da ita duk shekara ta hanyar zaɓar mutane uku da suka fi cancanta domin ba su shaidar girmamawa da kuma ɗan abin da zai ƙara musu ƙarfin guiwa da karsashin rubutu. Bayan mutane uku akan ware mutane goma a ba su shaidar girmamawa (certificate).
Wannan gasa tana ba marubuta dama su nuna basirarsu, inda ake zaɓar marubuta uku mafiya ƙwarewa don ba su lambar yabo da kuma ƙarfafa gwiwa. Haka kuma, ana karrama wasu marubuta goma ta hanyar ba su takardar shaidar girmamawa. An kafa wannan gasa ne domin haɓɓaka rubuce-rubuce a cikin harshen Hausa da kuma tallafawa marubuta masu tasowa.
Waye yake ɗaukar nauyin gasar?
Mai girma General Aliyu Muhammad Gusau shi ne ya asasar da yin gasar tare da wasu magoya baya da suke aiki ƙarƙashin ɗakin karatunsa dake jihar Kaduna wato Gusau Institute.
Janar Aliyu Mohammed Gusau tsohon soja ne kuma gogaggen jigo a harkar tsaro da siyasar Najeriya. An haife shi a ranar 18 ga Mayu, 1943, a garin Gusau, Jihar Zamfara.
Ayyukansa
- Ya shiga Nigerian Defence Academy (NDA) a 1964 kuma aka ba shi muƙamin Second Lieutenant a 1967.
- Ya taka rawa a Yaƙin Basasar Najeriya (Nigerian Civil War) bayan kammala horonsa.
- Ya zama Kwamandan Rundunar Soja ta 9 a Abeokuta daga 1976 zuwa 1978.
- Ya riƙe muƙamin Daraktan Leken Asiri na Sojoji (Director of Military Intelligence) daga 1979 zuwa 1983.
- Ya taka rawar gani a juyin mulkin da ya kawowa Janar Muhammadu Buhari mulki a 1983.
- A 1993, ya zama Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Ƙasa (Chief of Army Staff) na ɗan gajeren lokaci.
- Ya yi aiki a matsayin Mai Ba da Shawara Kan Harkokin Tsaro (National Security Adviser) a gwamnatocin Obasanjo, Yar’adua, da Jonathan.
- A 2014, ya zama Ministan Tsaro a ƙarƙashin shugabancin Goodluck Jonathan.
- Ya kasance memba a jam’iyyar PDP kuma yana da muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya tun daga lokacin mulkin soja har zuwa dawowar mulkin farar hula a 1999.
- A ranar 18 ga Mayu, 2023, ya cika shekaru 80 a duniya.
- Janar Aliyu Gusau na ɗaya daga cikin mutane mafi tasiri a tsaron Najeriya, inda ya kwashe sama da shekaru 40 yana aiki a ɓangaren soji da tsaro.
Dalilin kafa gasar
An samar da gasar ne domin tabbatar da kawo ci gaban rubutu da marubuta ta fuskar kawo wata gasa da za ta kawo goggaya domin bayyana baiwar da kowa ne marubuci yake da ita a fagen rubutu.
Bambancin gasar Gusau
Abubuwa da yawa sun bambanta gasar Gusau da sauran gasanni, wanda har wasu da yawa suke ganin cewar gasar Gusau ta fi ta BBC Hikayata. Domin ita gasar BBC labari ne gajere, kuma kalmomi kaɗan. Idan rabo da sa’a suka yi tasiri wanda bai taɓa cin gasa ba ma zai iya cin BBC Hikayata. Hakan ya faru sau ba adadi.

Dalilin haka ne da yawa suka yarda cewa, gasar Gusau sai jajjirtacen marubuci kuma mai bincike yayin gudanar da rubutunsa tare da tsantsar hikima ne yake iya haye matakan gasar. Kuma ba irin sauran gassanni ba ce masu ɗauke da kalmomi kaɗan da za ka je wani ya rubuta maka ka haye kamar yadda wasu suke yi.
Alfanun gasar
Gasar Gusau Institute tana da mahimman fa’idodi ga marubuta da al’ummar Hausa gaba ɗaya. Ga wasu daga cikin amfaninta:
- Gasar tana bai wa marubuta masu tasowa dama su nuna basirarsu a rubuce.
- Tana ƙarfafa musu guiwar don ci gaba da rubuce-rubuce da inganta fasahar su.
- Gasar tana ƙarfafa rubuce-rubuce a cikin harshen Hausa, wanda ke taimakawa wajen adana al’adu da bunƙasa adabi.
- Hakan yana ƙarfafawa marubuta guiwa kan su mayar da hankali kan rubuce-rubuce masu inganci da ma’ana.
- Marubuta da suka cancanta suna samun kyaututtuka, lambar yabo, da damar wallafa rubutunsu.
- Ana bai wa marubuta mafi hazaƙa lambar yabo da takardar shaidar girmamawa.
- Gasar tana taimaka wa marubuta su inganta rubuce-rubucensu ta hanyar ba su shawara da horo daga ƙwararru. Wannan yana haɓaka ƙwarewar wajen rubutu da kuma tsara labari.
- Rubuce-rubucen da ake gabatarwa a gasar yawanci suna ƙarfafa al’adun Hausa da tarihi. Haka kuma yana shafar abin da ya shafi kimiya da kuma fasahar sadarwa. Wannan yana taimakawa wajen yaɗa ilimi da al’adu ga ‘yan zamani.
- Gasar na taimakawa wajen samar da sababbin marubuta da littattafai masu kyau da kuma inganci.
- Marubuta suna samun damar haɗuwa da takwarorinsu da masana don musayar ra’ayi da ilimi. Wanda hakan kan buɗe ƙofofi da dama ga marubuta a harkar adabi da wallafe-wallafe.
- Gasar Gusau Institute babbar dama ce ga marubuta Hausa domin su nuna basirarsu, su sami tallafi, da kuma taimakawa wajen ci gaban adabin Hausa.
Jerin gwarazan gasar da labaransu 2018-2024
Shekarar 2018
- Bello Hamisu Ida mataki na ɗaya da labarinsa mai suna (Sabo Da Maza)
- Danladi Haruna mataki na biyu da labarinsa mai suna (Ɓarayin Zamani)
- Nura Sada Nasimat mataki na uku da labarinsa mai suna (Inuwar Wani)
Shekarar 2019
- Abdullahi Hassan Yarima mataki na ɗaya da labarinsa mai suna (Tamanin Da Tara)
- Zaharaddin Kalla mataki na biyu da labarinsa mai suna (Murucin Kan Dutse)
- Ado Abubakar Bala mataki na uku da labarinsa mai suna (Husufin Farin Ciki)
Shekarar 2020
- Jibrin Adamu Rano mataki na ɗaya da labarinsa mai suna (Da Ma Sun Faɗa Min)
- Lantana Ja’afar mataki na biyu da labarinta mai suna (Illar Almajiranci)
- Zulahat Sani Kagara mataki na uku da labarinta mai suna (Ɗan Waye)?
Shekarar 2021
- Hassana Suleiman Isma’il Matazu mataki na farko da labarinta mai suna (Fitsarin Fako)
- Ibrahim Yahaya Shehu mataki na biyu da labarinsa mai suna (Ɓaddabami)
- Mubarak Idris Abubakar mataki na uku da labarinsa mai suna (Rumfar Kara)
Shekarar 2022
- Bilkisu Muhammad Garkuwa matakin farko da labarinta mai suna (Ƙaddarar Rayuwa)
- Hajara Ahmad Maidoya mataki na biyu da labarinta mai suna (Ɗanyen Kasko)
- Muttaƙa A Hasaan mataki na uku da labarinsa mai suna (Ɗaukar Jinka)
Shekarar 2023
- Hauwa Shehu matakin farko da labarinta mai suna (Harin Gajimare)
- Ruƙayya Ibrahim mataki na biyu da labarinta mai suna (Wata Duniya)
- Fatima Sani mataki na uku da labarinta mai suna (Amanatun Amana)
Shekarar 2024
- Rufa’i Abubakar Adam matakin farko da labarinsa mai suna (Marubuciya)
- Ummi Abba Muhammad mataki na biyu da labarinta mai suna (Abinda Ka Shuka)
- Zainab Abdullahi mataki na uku da labarinta mai suna (Wasa Da Rayuwa)
Jigogin Labaran 2018-2024
2018
- 1-Boko Haram
- 2-Cyber Security
- 3-Safara
2019
- 1-Jarida (Investigation)
- 2-Shugabanci/Samun yancin ƙasar Najeriya
- 3-Gajerun Labarai
2020
- 1-Aljanu/Mafiya
- 2-Illar Almajiranci
- 3-Rashin Ilmi
2021
- 1-Garkuwa Da Mutane
- 2-Tsaro/Kishin ƙasa
- 3-Rikicin Ƙabilanci
2022
- 1-Mata Maza/Zabiya
- 2-Mata Maza
- 3-Rikicin Ƙabilanci
2023
- 1-Cyber Security
- 2-Sama Jannati
- 3-Fyaɗe
2024
- 1-Bincike/Rubutu
- 2-Kwaɗayi Son Zuciya
- 3-Matsalar Tsaro
Manazarta
U. Karofi. (2025, January 1). Abin da ya bambanta Gasar Marubuta ta Gusau Institute da sauran. Manhaja – Blueprint Hausa Version.
Wikipedia contributors. (2025, January 18). Aliyu Mohammed Gusau. Wikipedia.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.