Skip to content

Ghali Na’Abba

An haifi Ghali Umar Na’Abba a Tundun Nufawa da ke cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958. Mahaifinsa babban malami kuma ɗan kasuwa, wanda ya koya masa kyawawan ɗabi’u da gaskiya da jajircewa da Ikhlasi da sauran nagartattun halayen bisa koyarwar addinin Musulunci.

Marigayi Ghali Umar Na’Abba, tsohon kakakin majalisar dokokin Najeriya 1999-2003

Karatunsa

Ghali Na’Abba ya halarci makarantar firamare ta Jakara a Kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na firamare a shekarar 1969. Daga nan kuma ya halarci kwalejin Rumfa da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na sakandare bayan da rubuta jarabawar Afirka ta Yamma, sannan kuma ya samu gurbin shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya a watan Oktoba, 1976. Ya yi digirin farko a fannin kimiyyar siyasa daga ABU 1979 ɗin. Masanin kimiyyar siyasa ne ya kammala karatun digirinsa na biyu a kan jagoranci da shugabanci na gari a jami’ar Harvard ta Amurka a shekarar 2004.

Harkokin kasuwanci

Bayan kammala karatunsa na jami’a da hidimar ƙasa ta tsawon shekara ɗaya, ya shiga rukunin kamfanonin mahaifinsa a shekarar 1980. Harkokin kasuwancinsa sun haɗa da shigo da kaya daga waje da mallakar masana’antun sarrafa kayayyaki. Ya riƙe muƙamai sosai tun daga kan matsayin sakatare a kamfanin Na’Abba Commercial Trading Company Limited zuwa Manajan Darakta a kamfanin Manifold Limited da darakta a kamfanin Quick Prints Limited da Manajan darakta a kamfanin Hinterland Resources Limited.

Harkokin siyasa

A matsayinsa na ɗalibin kimiyyar siyasa, a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, an zaɓe shi a matsayin mamban kwamitin zartas’rwa na jami’ar ABU reshen jam’iyyar Revolutionary People’s Redemption Party da aka kafa a jamhuriya ta biyu ta hannun hamshakin ɗan siyasar nan, Malam Aminu Kano. Ya zama fitaccen ɗan siyasa a jihar Kano da Najeriya baki daya.

Na’Abba ya koma jam’iyyar PDP ne a shekarar 1998 a lokacin kafuwarta kuma ya zama ɗan takarar jam’iyyar a watan Afrilun 1999 a zaɓen majalisar dokokin tarayya a mazaɓar Kano Municipal. Ya lashe zaɓen da ya wakilci mazaɓar a majalisar wakilai.

Tare da goyon bayan sauran zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai daga shiyyar Kano da Arewa maso Yamma, ya ci gaba da zama shugaban majalisar. Duk da cewa ya samu gagarumin goyon baya daga takwarorinsa da shugabannin jam’iyyar, amma ya amince da Ibrahim Salisu Buhari, wanda daga baya ya zama shugaban majalisar wakilai na farko a jamhuriya ta huɗu.

Daga nan kuma aka naɗa shi shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar. Bayan wa’adin, Buhari na ƙanƙanin lokaci, rigar shugabanci ta faɗa kan Na’Abba yayin da majalisar ta haɗa baki gabaɗaya suka cim ma matsayar da ba a taɓa ganin irin ta ba, suka sanya shi shugaban majalisar.

Marigayi kakakin majalisar dokokin Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, yayin bikin kaddamar da wani aiki lokacin da yake shugaban majalisa.

A watan Afrilun 2003, ya nemi sake tsayawa takara a majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a wani abin da ake ganin kamar makircin siyasa ne da aka shirya masa don hana shi sake komawa matsayin shugaban majalisar saboda farin jininsa a majalisar.

Manufofinsa a matsayin kakakin majalisa

Da aka zabe shi a matsayin kakakin majalisar, Na’Abba ya bayyana kudurori da manufofinsa wanda suka hada da:

  • Kare doka da tsarin mulkin tarayyar Najeriya
  • Tsarawa da aiwatar da ingantaccen tsarin dokokin ƙasa
  • Gudanar da mulki na gaskiya don tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ingantaccen ci gaban ƙasa
  • Ƙaddamar da kyawawan dokoki, kudurori da manufofi don jawo hankalin mutane
  • Ingantacciyar kulawa da asusun jama’a ta hanyar ingantaccen tsarin kasafin kuɗi

Canje-canjen da ya kawo a majalisa

  • Bincike mai zurfi na tsarin kasafin kuɗi, da yin gyare-gyare masu muhimmanci a inda ya cancanta
  • Ƙirƙirar kyakkyawar dangantaka da kafofin watsa labaru da ƙungiyoyin jama’a don tabbatar da ci gaban majalisa
  • Ƙarfafa kwamitocin majalisa da shugabannin kwamitoci da shugabannin hukumomin kan batutuwan manufofi da matakin aiwatar da kasafin kuɗi
  • Haɗin kai da Odita-Janar da Akanta-Janar na tarayya da ministan kuɗi don binciken gwamnati da ɗaukar matakin gaggawa
  • Tattaunawa da mambobi 300 daga cikin 360 don yin watsi da matakin da Shugaba Obasanjo ya dauka kan kudirin doka irin su NDDC, da dai sauransu. Majalisar Na’Abba ce ta kasance majalisa ɗaya tilo da ta iya yin watsi da matakin shugaban ƙasa kan wani ƙudiri.
  • Muhawara akai-akai kan halin da al’umma ke ciki. Muhawarar 2002 ta haifar da wani ƙudiri da majalisar ta yi na fara yunƙurin tsige shugaba Obasanjo sakamakon yin karan tsaye ga dokokin kundin tsarin mulki.
  • A watan Agustan 2002, majalisar ta baiwa shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo wa’adin ko dai ya yi murabus ko kuma a hukunta shi.

Ɓangaren zartarwa na gwamnati, musamman fadar shugaban kasa, ba ta amince da shugabancinsa ba. Don haka, mafi yawan lokutan Na’Abba ya fuskanci kalubale da shirye-shiryen da fadar shugaban ƙasa ta yi na tsige shi, domin ta maye gurbinsa da wani mai sassaucin ra’ayi. Wannan ya yanke alaƙa tsakanin majalisar da fadar shugaban ƙasa.

Marigayi Ghali Umar Na’Abba, tsohon shugaban majalisar dokokin Najeriya.

Lambobin yabo da karramawa

Na’Abba ya samu lambobin yabo da dama daga gwamnati, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin dalibai, kungiyoyin kasuwanci masu zaman kansu, kungiyoyin siyasa da ma hukumomin gwamnatin ƙasashen waje da dai sauransu. Lambobin karramawar sun hada da:

  • Lambar karramawa ta kasa (CFR) da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ba shi a shekarar 2010
  • Honorary Citizen na Kansas City Missouri, Amurka
  • Lambar yabo ta Man of Integrity by Students Union of University of Nigeria, Nsukka,
  • Award of Excellence, don tabbatar da tsarin dimokuradiyya a Najeriya ta Majalisar Abuja Council of Nigeria Union of Journalists (NUJ)
  • Takardar shedar karramawa daga Cibiyar Kula da Ma’aikata ta Najeriya
  • Kyautar Millennium Gold for Youths Development by International Youth Congress
  • Pillar of Nigerian Legislative Award by Law Students Society, University of Jos
  • Da Millennium Daga Kungiyar Matasan Arewa.

Tarurrukan da ya halarta

Ya halarci kuma ya jagoranta har ma da kuma ya gabatar da kasidu a tarurrukan ƙarawa juna sani da tarukan ƙasa da ƙasa kan harkokin siyasa da majalisa da ci gaba da shugabanci na gari. Daga cikinsu akwai;

  • Taron shugabannin majalisun dokokin da aka gudanar a birnin New York a shekara ta 2000
  • Taron masu jawabi a yammacin Afirka da aka gudanar a shekarar 2000 da 2001 a Ouagadougou da Abuja
  • Taro na shekara-shekara na majalisar dokokin Commonwealth da aka gudanar daban-daban a cikin 1999, 2000, 2001 a Trinidad da Tobago, London da Melbourne, Ostiraliya da sauran su.

Mutuwarsa

Ahmed Lawal, mai taimakinsa ne ya fitar da sanarwar mutuwarsa ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a wata tattaunawa ta wayar tarho. Ya ce tsohon kakakin ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba, 27 ga Disamba, 2023, a asibitin kasa da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 65 a duniya. Ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya goma da kuma jikoki uku.

Manazarta

Ali M. Ali. (2023, December 30). Ghali Na’Abba: Salute to an avatar of democracy. Daily Nigerian.

Daily Trust. (2023, December 27). Six things to know about late Speaker Ghali Na’Abba. Daily Trust.

Shehu, I., & Shehu, I. (2023, December 27). OBITUARY: Ghali Na’Abba, ex-reps speaker who was a thorn in Obasanjo’s flesh. TheCable.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×