Skip to content

Gudummawa

Ƙamusun Hausa ya bayar da ma’anar gudummuwa da cewa: “Taimako na aiki ko kuɗi ko abinci ko sutura ko wani abu”. Gudummuwa tana bayani ne kan taimakon da ake yi ga wani yayin da yake wata hidima ko ya shiga wani halin matsi da takura ko wata hasara ko rashi na dukiya ko kaya. Al’adar gudummuwa ta shiga kusan kowane al’amari na rayuwar Hausawa. Da wuya a ce ga wani abu na arziki wanda mutum zai yi, a rasa mai kawo masa gudummuwa ta kuɗi ko kayan aiki ko a taya shi gudanar da wannan abu da wani taimako da zai ji daɗi.

Ire-iren gudummuwa

A dunƙule, an raba gudummuwa zuwa gida huɗu ta fuskar ma’anar da ta ƙunsa kamar haka:

Gudummuwar kuɗi

Kasancewar kuɗi abu ne da aka aminta da su a ko’ina domin yin sayayya, akan yi gudummuwa ta taimako da su. Taimako ta hanyar amfani da kuɗi ya zo wurin Hausawa daga baya ne, saboda babu kuɗi sai lokacin da mai jan kunne ya zo ƙasar Hausa. Kafin wannan lokaci sai dai a yi abin da ake kira “Ba ni Gishiri in ba ka Manda”. Kuɗi suna da sauƙin sha’ani ganin cewa suna iya sayen kayan da za a kai a matsayin taimako ko gudummawa ga wani. Daga lokacin da kuɗi suka samu a wurin Hausawa, taimako idan ya taso akan yi amfani da su wurin bai wa mutuum ya yi hidimarsa da su, ko kuma ya bayar a yi masa wasu ayyukan da suka shafi hidimar ko ya yi wata biyan bukatar da su.

Don haka, a halin yanzu kuɗi suna cikin abubuwan da Hausawa suke yin taimako da su ganin cewa da su ake mallakar kusan duk wani abu da ake nema ta hanyar ƙarfin tuwo. Ana bayar da gudummuwar kuɗi ga ‘yan’uwa da abokan arziki, da dangi da sauran mabukata saboda rayuwar wannan zamani ta dogara da su.

Gudummuwar sutura

Sutura a nan tana nufin abin da mutum zai rufe tsiraicinsa da shi. To sai dai a yanzu suturun da ake amfani da su na zamani ne waɗanda suke rufe jiki. Hausawa suna da ɗabi’ar bayar da gudummuwar sutura musamman wanda zai yi aure saboda ya haɗa kayan lefe. Ga mace idan ta haihu, akan yi mata gudummuwa da turamen zannuwa domin ta samu abin yin goyo da wanda za ta yi bikin suna da shi. Haka kuma, suturar jariri tana daga cikin abin da ake bayar da gudummuwa da ita ga wadda ta haihu saboda a suturta jariri.

A zamantakewar Hausawa, wanda hasarar gobara ta same shi, ‘yan’uwa da abokai suna kawo masa gudummuwa. Idan aka cire abinci da za a ba shi, sutura tana biye saboda muhimmancin da take da shi. Baya ga haka, waɗanda suka yi sabuwar sutura sukan bayar da wasu daga cikin waɗanda suke sanyawa a matsayin taimako ga wasu ‘yan’uwa ko almajirai. A lokacin sallar azumi ko layya, (ƙaramar sallah ko babba) ana samun masu bai wa ‘yan’uwansu gudummuwa ta sababbin sutura domin su yi bikin salla kamar yadda kowa zai yi.

A halin da ake ciki, ana samun masu sayen farin alawayyo mai yawa a matsayin gudummuwa, da zarar an yi mutuwa za a karɓa ba sai an saya ba. Wannan ya nuna cewa suturar da ake sanya wa mutane in sun mutu mafi yawa taimako ake samu daga jama’a. Galibi al’umma ko masu hali ke sayen mai yawa wanda za a riƙa karɓa kyauta a duk lokacin da bukatarsa ta taso. Waɗannan misalai sun nuna cewa sutura tana da gurbi na musamman, kuma ana bayar da ita a matsayin gudummuwa cikin matakai daban-daban a rayuwar Hausawa.

Gudummuwar kayan aiki

A duk lokacin da aka tashi aurar da yarinya budurwa, dangi da sauran abokan arziki sukan aika wa iyayen yarinya da gudummuwa bakin gwargwado. Daga cikin ire-iren abin da ake bayar da gudummuwar akwai kayan aiki na gida kamar su ƙore da matankaɗi da kwanuka da dai sauransu. Sauran ɓangarorin rayuwa su ma ana samun wuraren da ake bayar da taimako da kayan aiki.

Gudummuwar abinci

Duk wata hidima da ta shafi matakan rayuwa (wato aure da haihuwa da mutuwa) ana samun taimakon abinci ɗanye ko dafaffe wanda ‘yan’uwa da abokan arziki za su aiko. Haka kuma, a lokacin da wani zai yi walima ta saukar karatu ko tarewa sabon gida, akan sami masu yi masa gudummuwa da abinci. Wanda iftila’in gobara ko ruwa suka afka masa, yana samun gudummuwar abinci daga jama’a. Bisa al’adar Hausawa, idan suka haɗu da ‘yan’uwa ko abokai matafiya akan ba su taimako na abinci domin yin guzuri.

Gudummuwar aiki

A wasu lokuta akan sami yanayin da mutum zai yi wani aiki don ya yi ceto ko ya taimaka a kan wani yanayi da aka shiga. Misali idan mutum ko wata dabba ta faɗa rijiya, jama’a suka yi ƙoƙari wajen ceto su, to sun yi wani aiki ke nan a matsayin gudummuwa. Haka ma idan ya kasance mutun ya riga ya shuke gonarsa sai wata lalura ta rashin lafiya ta kama shi ko kuma wani abu ya faru ya bar gari ko kuma ya yi wani laifi aka ɗaure shi, to jama’a sukan ba da gudummuwa a aikace don a nome ganar a kula da ita don kada iyalinsa su yi hasarar abincin.

Muhimmancin gudummawa

Gudummawa a matsayin nau’i na taimakon juna tana da alfanu da muhimmanci a tsakanin mutane a rayuwa ta yau da kullum, wasu daga cikin alfanun gudunmawa sun haɗa da:

Samar da haɗin kai tsakanin al’umma sanadiyyar abin da ake ba da gudunmawar da shi. Wanda aka bawa lallai zai yi ƙoƙarin ganin cewa shi ma ya mayar ko ya bayar da makamanciyarta ga wasu domin ya ji daɗi lokcin da aka ba shi.

Gudunmawa tana hana wasu mutanen cin bashi ko shiga halin ni’yasu. Misali, wanda ke shirin yin wata sabga ta biki sawa’un bikin suna ko na aure, lallai yakan bukaci kuɗaɗe sosai a hannunsa, wanda zai nema ko da hanyar cin bashi ne. Idan kuwa ‘yan uwa da abokan arziki suka ba shi gudummawa, to zai rage wani abin. Ko da zai ci bashin zai zama kaɗan.

Gina soyayya da kauna a zukatan jama’a, a yayin da mai ba da gudunmawa ya bayar ga mai karɓa, lallai wanda aka taimaka yakan ji farinciki da ƙaunar wanda ya taimake shi.

Gudunmawa tana kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mutane. Idan mutum yana bukatar wani abu da yake ganin kamar ya fi karfinsa, hankalinsa zai iya tashi har ya yi wani mutum tunanin. A yayin da aka ba shi gudunmawa wajen tabbatar da wannan abin yakan samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Manazarta

C.N.H.N (2006) Ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y. Da Wasu. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×