Skip to content

Hadin kai

Haɗin kai na nufin wata dabara ce da al’umma kan aiwatar tun a zamanin da domin su gudanar da abin da mutum ɗaya ba zai iya aiwatar da shi ba kai tsaye. Wannan na nuni da cewa, haɗin kai wata dabara ce da al’ummar Hausawa ke yi don tafiyar da lamurransu cikin taimakon juna da yarda da amincewa domin samun ci gaba ko gudun fitina a tsakaninsu. Dabarar haɗin kai a cikin al’umma wata hanya ce ta tafiya a ƙungiyance don a samu biyan buƙata cikin sauri ba tare da an wahala ba. Kowane mutum yana da hikima da ta sha bamban da ta ɗan’uwansa. Wannan ya sanya idan an haɗa hikimomin mutane daban-daban ake samun biyan buƙata da mafita, kuma a yi aiki mai inganci.

Al’adun haɗin kai na hausawa

Hausawa suna da waɗansu al’adu da aka daɗe ana aiwatar da su tare domin samar da haɗin kai. Matasa su ne ƙashin bayan kowace al’umma da suke da hankali da tunani da ƙarfin aiwatar da aiki tare. Matasa suna da hanyoyi da yawa a cikin ɓangarori da dama da suke haɗa-kai a tafiyar da rayuwar yau da kullum. Akwai hanyoyin da yawa da Hausawa suke bi wajen aiwatar da wannan ɗabi’a ta haɗin kai, daga ciki akwai:

Tafiye-tafiyen fatauci

Wannan wani salon yin ciniki ne daga wani wuri zuwa wani. Wato dabara ce da wasu Hausawa suke yi ta sayar da hajojinsu daga wuri zuwa wuri suna bin ranakun cin kasuwa. Hausawa suna gudanar da wannan al’adar kasuwancin ne ta hanyar haɗa mutane da yawa a yi ta tafiya tare. Ana kiran waɗannan mutane ‘yan kasuwar ayarin fatake. Shugabansu kuma shi ne madugu. Wannan tafiya ce ta haɗin kai ta yadda akan taimaki juna a ɗebe wa juna kewa, da kuma kauce wa wata ƙaddara da hatsari da kan iya faɗa wa mutum ɗaya. Tafiyar nan da ake yi cikin taro akan samu mutane daban-daban da suke da ƙwarewa a cikin kasuwancin. Don haka idan aka sauka gari kowa zai sauke abin da ya zo da shi, masu saye za su zo suna saya. Duk wanda yake sabo cikin al’amarin za a koyar da shi yadda zai sayar da kayansa, da kuma nuna masa waɗanda yake son saye ya kai nasa gari, har ma a yi masa ciniki. Sannan idan ayari zai tashi, sai an tabbatar da kowa yana nan, don kar a tafi a bar shi bai san hanya ba, ya faɗa cikin haɗari.

Al’adar kaciya/shayi

Iyayen yara sukan sa lokacin yin kaciya, a sanar da wanzami. idan lokaci ya yi sai a haɗa masa yaran anguwa, wuri ɗaya don yin kaciya. Mafi yawa an fi yin wannan kaciya a lokacin sanyi, domin lokacin rauni ya fi sauƙin warkewa. Kuma ana samun cikin unguwa mutum ɗaya mai wadata da zai ɗauki nauyin yin kaciyar a gidansa, inda yaran za su zauna a gidansa ya ci gaba da yi musu hidima, har su fita. Wannan haɗuwa tana ƙara ƙulla dankon zumunta tsakanin iyaye saboda kyautatawar da aka yi musu. Su ma waɗannan yaran, tara su da aka wuri ɗaya yakan samar da haɗin kansu na lokaci mai tsawo. Za su ci gaba da wasa tare, su girma da ruhin taimakon juna.

Taron zaman makoki

Zaman makoki shi ne zaman da Hausawa suke yi na wasu ’yan kwanaki ana karɓar gaisuwa idan wani ya rasu. Akwai haɗin kai sosai wajen zaman makoki, idan aka yi rasuwa, mutanen unguwa na kusa da na nesa da abokan juna za a tafi tare a yi wa waɗanda aka yi wa rasuwar gaisuwa. Waɗansu ma za su zauna tare da waɗanda aka yi wa rashi don nuna kulawarsu da ɗebe musu kewar rashin har a share makoki. Haka kuma za a riƙa yi wa waɗanda aka yi wa rasuwar hidima ta yin aikin
gida kasancewar suna cikin alhini, a kuma riƙa dafa abinci ana kawowa gidajen ‘yan uwa da maƙwabtansa. Wannan zama da ake yi da hidindimun da ake gudanarwa kyakkywar ɗabi’a ce ta haɗin kai da ta yi tasiri a al’umar Hausawa kuma ake amfana da ita.

Aikin gayya

Aikin gayya aiki ne da ake yi wuri ɗaya a cikin taron mutane don yin aikin da mutum ɗaya ba zai iya yi ba. Yin wannan aikin na sauƙaƙa wa masu aiwatar da shi, su yi shi cikin sauƙi babu takura. Ayyuka na al’umma mafi yawa ana haɗuwa a yi su tare don samun ci gaba. Irin wannan aikin yana haifar da haɗin kai a cikin al’umma. A wurin gudanar da aikin gayya akan sami haɗin tsakanin waɗanda suka aiwatar da aiki da kuma tsakanin masu aiki da waɗanda suka amfana kai tsaye da aikin.

Cin abinci tare (ciyayya)

Wannan al’ada ta cin abinci tare, al’ada ce da ta haɗin kai da ta daɗe a cikin al’ummar Hausawa. Wannan al’adar, magidanta da matasa da ƙananan yara suna aiwatar da ita. Tun yara suna ƙanana ake kwaɗaitar da su cin abinci cikin taro domin koyar da su haɗin kai. Aka nuna musu yin hakan na sanya albarka a cikin abincin. Yara sukan taso da wannan al’ada har su zama magidanta. A wannan matakin za su riƙa kai abincin kowane gida a wajen da suke zama don su ci tare. Wannan al’adar tana matuƙar taimaka wa waɗanda ba su da shi, ko ba su da halin a girka mai kyau a gidajensu.

Wasannin dandali

Wasannin dandali, wasanni ne da yara maza da mata ke yi yawanci da maraice ko da dare a dandali, suna nuna al’adunsu da kuma mota jiki. Wasannin suna da matuƙar muhimmanci wajen haɗin kansu tun suna ƙanana domin za su saba da juna kasancewar suna wasa a wuri ɗaya. Wannan wasa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin-kan yara. Daga irin waɗannan wasanni ake tashi a matsayin abokai.

Watanda

Wannan wani tsari ne da mutane da yawa suke tara kuɗi su sayi dabba guda ɗaya su yanka, su rarraba naman a tsakaninsu. Wannan al’ada da ke fito da ɗabi’ar haɗin kai an fi aiwatar da ita ne a lokacin bikin sallah. Magidanta na unguwa ko wurin aiki ɗaya su ke haɗa kudi a sayi dabba, yawanci sa a yanka don raba nama. Ana kasa naman gwargwadon kuɗin da mutun ya bayar. Idan an yanke dabbar za a fasalta nama, ta yadda za a jefa wa kowa rabonsa na daga cikin sassan wannan dabba. Sai magidantan su kai gidajensu a ƙara da kaji ga masu halin yin haka, don yin abincin sallah. Maƙasudin gudanar da wannan al’ada shi ne a yalwata iyali da nama a lokacin wannan biki na salla. To amma a ilmance za a fahimci wani nau’i salo ne na haɗin kai da ke samar da saukin rayuwa a al’umar Hausawa.

Al’adar ajo

Ana aiwatar da ajo ne a wajen bikin aure a hidimar bukukuwan da suka
shafi ango. ’Yan’uwan ango da abokansa suke haɗuwa da dare su gayyaci mawaƙa, a samu wajen da za a yi bikin kamar dandali. Dalilin yin wannan biki, shi ne don a bai wa ango gudummuwa ta kuɗi da abinci da duk abin da ake iya bayarwa a matsayin gudummuwa. A wajen ana yin naɗi na muƙarraban da za su kula da ba da gudummuwa da gudanar da bikin. Duk wanda ya bayar da tashi gudummuwa za a rubuta ko a sanar da angon. Idan an gama haɗawa za a damƙawa ango. Wannan taruwa da aka yi haɗin kai ne da ke tabbatar da taikamakon juna a al’umar Hausawa.

Noman gandu

Noman gandu aiki ne na haɗin kai da taimakekeniya, inda za a taru lokaci ɗaya a yi aiki nome gonar gado. Iyaye na yin wannan dabara saboda haɗin kan ‘ya’yansu, ya kasance suna taruwa a lokaci ɗaya su yi aiki mai yawa na noma ba tare da sun wahala ba. A irin wannan yanayi za a ga duk zuri’ar suna haɗuwa don su samar da abin da za su ci ba tare da nuna bambanci ko fifiko ko ƙyamar juna ba. Gidajen Hausawa da suka tashi da wannan ɗabi’ar za a ga suna da haɗin kai matuƙa a tsakanin su.

Masu yin haɗin kai a cikin al’umma

Kowane rukuni daga cikin al’umma suna yin haɗin kai. Ana samun haɗin- kai tsakanin dattijai wajen samar da ci gaban al’umma. Ana samu tsakanin shuwagabanni da talakawansu. Ana samu a cikin matasa maza masu tasowa. Ana yin haɗin kai tsakanin mata manya da matasa, sai dai ya danganci al’amarin da aka yi haɗin kai dominsa. Haɗin kai har a cikin gida tsakanin kishiyoyi ana yinsa don samun kwanciyar hankali ga mai gida da tafiyar da iyali yadda ya kamata. Wato dai lamarin haɗin kai a al’umar Hausawa ba abu ba ne da ya keɓanta da wani rukuni na jama’a ba. Ya shafi kowa da kowa.

Manazarta

Ginga, S. A (2018) Hanyoyin Haɗin-kan Matasa na Gargajiya da Tasirin Zamani. Kundin digiri na ɗaya, Jami’ar Jihar Sakkwato.

Muhammad, M. S. (1997). “Zumuncin Bahaushe” Kundin Digirin B. A. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

S. M. (ed) (2010). Al’adu d ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El–Abbas Printers & Media Concept.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×