Skip to content

Jimina

Jimina wata nau’in babban tsuntsu ne da ake samu asali a Afirka. Ita ce nau’in tsuntsu mafi girma a duniya, tana girma har kusan tsayin ƙafa 9. Kazalika kasancewar ta tsuntsu mafi girma, ta ma  fi sauran tsuntsaye nauyi. Jimina tana iya yin nauyin kilogiram 145, wanda kusan daidai yake da nauyin manyan mutane biyu da suka girma sosai suka cika siffofin girma.

Jimina suna ƙarar da mafi yawan lokutansu su bibiyu, kashi 16 cikin 100 ne kawai na jimina suke tarayya fiye da bibiyu.

Jiminai tana da dogayen ƙafafu, jikinta a zagaye yake, sannan tana da siririn wuya mai tsananin tsayi. Mazan jimina suna da baƙin gashi, yayin da matan suke da gashi launin ruwan kasa. Duk da yanayin girmansu, amma ɗan ƙaramin kai suke da shi.

Idanuwansu su ne mafi girman a dukkan dabbobin da ke rayuwa a doron ƙasa, suna da faɗin inci 2 a ma’aunin diamita. Haɗe da tsayinsu, idanun jimina suna ba su damar ganin mafarauta daga nesa sosai. Jimina ita ce kawai nau’in tsuntsu wanda ke da yatsu biyu a kan kowace ƙafa. Sauran nau’in tsuntsaye suna da yatsu uku ko huɗu a kowace ƙafa.

Nau’ikan jimina

Akwai nau’ikan jimina guda biyu: jimina ta gama-gari da jimina ta Somaliya.

Jimina gama-gari

Wannan nau’in jimina tana samuwa ne a Arewacin Afirka. Ita ce nau’in jimina mafi girma kuma tana da gashi mai launin ruwan hoda da jaja-jaja a wuyanta da kafafunta. Jiminar gama-gari ita ce ta fi yaɗuwa a cikin dukkan nau’in jimina.

Jiminar Somaliya

Ana samun wannan nau’in jimina a Habasha, Kenya da kamar yadda sunan ke nunawa har da Somaliya. Ba kamar jiminar gama-gari ba, jiminar Somaliya tana da launin shuɗi a wuyanta da cinyoyinta. A lokacin yin barbara launin shuɗi yakan zama mai haske a jikin mazajen.

Muhallin jimina

Jiminai jinsin dabbobi ne ma yin ƙaura daga wannan muhalli zuwa wani, yawanci suna tafiye-tafiye akai-akai maimakon zama a wuri ɗaya. Muhallin zaman jimina ya ƙunshi zafi da yanayin bushewa akasari kuma jeji ne. Sun fi son wurare buɗaɗɗu, tare da ‘yan bishiyoyi ƙalilan. Wannan yana ba su damar iya gani da hango nesa ta kowane ɓangare.

Haka nan ana iya samun jimina a cikin gandun daji da sararin ciyayi a wasu wurare. An yi imanin cewa jimina ta taɓa kewaye duk faɗin Afirka, Asiya da sassan Larabawa. Duk da haka, sakamakon farauta da faɗaɗar mutane, kewayensu ya ragu a Afirka kaɗai.

Jimina tana jin daɗin wanka da yin iyo. Don haka, mazaunin jimina dole ne ya kasance kusa da ingantaccen ruwa mai yawa. Wasu jimina suna su zama kaɗai, yayin da wasu ke rayuwa cikin rukuni-rukuni ko manyan sansanoni

Abincin jimina

Jimina nau’in dabbobi ne omnivores, ma’ana suna cin nama da tsirrai don yin rayuwa. Duk da cewa abincinsu ya ƙunshi tsirrai, amma wasu daga cikin abincin da aka fi so na jimina sun haɗa da ‘ya’yan itace, berries, tsaba, ganye, furanni da shrubs.

Lokacin da suke cikin yanayin buƙatar nama, suna cin kwaɗi, ƙananan dabbobi masu rarrafe da kunkuru. Suna kuma da ɗanɗana ƙwari, musamman fara. Jimina suna amfani da damarsu, suna cin abincin da ya fi samu maimakon yin zaɓi. Don haka ne ma wani lokaci suke cin ragowar abincin manyan dabbobi.

Jimina na ɗaya daga cikin nau’in tsuntsaye masu tsawon rayuwa, suna iya rayuwa har tsawon shekaru 62.

A yayin da aka kama jimina aka ajiye domin kiwo, yawanci ana ciyar da ita da ‘ya’yan itace, kayan lambu, ciyawa da sauran su. Abin sha’awa, jiminai suna haɗiyar tsakuwa don taimaka musu su niƙa abincinsu. Ba su da hakora, don haka hadiye tsakuwa yana da mahimmanci wajen taimaka musu narkar da abincinsu. Abincin jimina yana da wadataccen danshi, don haka suna iya yin kwanaki da yawa ba tare da shan ruwa kai tsaye ba. Kusan kashi 45% na cikin jimina na iya ƙunsar tsakuwa da yashi a kowane lokaci.

Shin ko jimina na iya tashi?

Duk da kasancewar ta tsuntsuwa,
jimina ba za su iya tashi ba. Su dai jimina wani nau’in tsuntsaye ne marasa tashi da ake kira a cikin daular dabbobi ratites. Sauran ratites gama-gari sun haɗa da emus, cassowaries da kiwis. Jimina ba za su iya tashi ba saboda dalilai da yawa:

  • Na farko, suna da nauyi ta yadda ko da mafi ƙarfi na fuka-fuki zai iya hana su tashi a cikin iska.
  • Abu na biyu, ba a tsara tsarin kashinsu don tashi ba. Suna da ƙashin ciki, wanda baya barin su yin amfani da fuka-fukansu kamar yadda yawancin tsuntsaye suke yi.
  • Na ƙarshe, duk da girmansu, jimina suna da fuka-fukai masu rauni fiye da yawancin tsuntsaye. Tsawon fuka-fukansu yana da girma sosai, yana da kusan mita 2. Duk da haka amma ba su da ƙarfin da zai ba su damar tashi.

Saboda haka dole ne a lura cewa fuka-fukan jimina ba su da amfani sosai. Amma a zahiri, suna da mahimmanci wajen taimaka musu ne yayin da suke gudu cikin sauri domin samun daidaito. Suna kuma taimaka musu wajen dakatawa yayin gudun, juyawa da motsa jiki yadda ya kamata a lokacin da suke guje wa mafarauta.

Akwai hasashe da yawa game da dalilin da ya sa wasu tsuntsaye suka rikiɗe ba sa iya tashi. Masana kimiyya da yawa suna tunanin cewa tsuntsayen sun rasa ikon yin tashi sakamakon yawaita yin jima’i da cin abinci. Wata ka’idar kuma ta nuna cewa an tilasta wa tsuntsayen ne su zauna a ƙasa saboda tsananin yanayi a sararin samaniya.

Yanayin saurin Jimina

An halicci jimina da ɗabi’ar gudu. Tana da sauri, tare da baiwar iya tserewa yawancin dabbobi a muhallansu. Tare da siririyar ƙafafu masu ƙarfi, jimina na iya gudun da ya kai har mil 60 a cikin sa’a ɗaya.

Koda ba a lokacin da suke yin cikakken gudu ba, suna iya gudun matsakaicin nisan kusan mil 45 a kowace sa’a. Lokacin da suke buƙatar ƙara gudu, za su iya kula da gudun kusan mil 30 a kowace sa’a. A kowane tayin takun da jimina ta yi zai iya zama tsayin ƙafa 12. Jimina su ne tsuntsaye mafi sauri a duniya, kuma mafi sauri dabba mai kafafu biyu.

Abokan gabar jimina

Kasancewar jimina a Afirka, dole ne su fuskanci harin namun daji iri-iri a kowane lokaci. Wasu daga cikin manyan abokan gaba na jimina sun haɗa da, zakuna da damisa da kuraye. Ƙananun jimina suna da rauni ga ɗimbin makiya. Tsuntsaye irin su warthogs, jackals da mongoose duk an san su da farautar matasan jimina.

Jimina na samar da ƙwai mafi girma fiye da kowane tsuntsu. Ƙwan na cike da sinadaran gina jiki sosai kuma tushen kuzari ne. A sakamakon haka, mafarauta na yawan neman su. Haka nan akwai wani nau’in ungulu da ke jifar ƙwayayen jimina da duwatsu don su fashe.

Duk da cewa ana ganin jimina a matsayin ganima ga dabbobi da yawa a duk faɗin Afirka, ba sa samu cikin sauƙi. Za su iya tsere wa yawancin mafarauta cikin sauƙi kuma su kama ɗaya daga cikin mafiya ƙarfi a cikin dabbobi. Jimina suna da ƙarfi sosai har sukan iya kashe manyan zakuna yayin da suke kare kansu.

Shin jimina tana binne kanta don tsoro?

Jiminai ba sa binne kawunansu a cikin yashi lokacin da suka tsorata. An yi imani da cewa wannan saɓanin bayanin ya fito ne daga rashin fahimtar cewa jimina suna sanya kawunansu a cikin rairayi ne don nemo duwatsun da za su hadiye.

Duk da yawan jimina ya ragu sosai a cikin shekaru 200 da suka gabata, har yanzu tana mamaye da kusan mil 3,800,000.

Jiminai suna raguwa lokacin da mafarauta suke kusa. Wannan kuma na iya bayyana dalilin da ya sa mutane suka yarda cewa jiminai suna nutsar da kawunansu cikin yashi. Wata ka’ida kuma ita ce, lokacin da jimina suka sanya kawunansu a cikin gida don jujjuya ƙwai, ana iya yin kuskuren fahimtar dalilin binne kawunansu.

Takaitattun bayanai game da Jimina

  • Jimina tana da ciki har kashi uku.
  • Baya ga yin amfani da fuka-fukansu  wajen samun daidaito yayin, haka nan kuma suna amfani da su wajen samar da inuwa ga jariransu da yin kwarkwasa lokacin jima’i.
  • A lokacin jima’i, mazajen jimina suna faɗa da juna ta hanyar gwara kawunansu da abokan hamayyarsu.
  • Lokacin da jimina suke yin jima’i, namiji zai jawo hankalin mace ta hanyar yin jima’i mai rikitarwa.
  • Wasu nau’ikan jimina suna yin tarayya su biyu har abada, suna kulla dangantaka ta kud da kud da juna.
  • Ƙwan jimina guda ɗaya ya kai ƙwan kaji dozin biyu a nauyi.
  • Ana kiwon jimina a duk faɗin duniya. Ana sayar da gashin fuka-fukan su don yin kayan ado, kuma ana ci namansu sosai.
  • A wasu lokuta jimina suna tafiya kiwo tare da sauran dabbobin kiwo. Abokan tafiyarsu yawanci sun haɗa da jakin dawa da tururuwa.
  • Jimina suna ƙarar da mafi yawan lokutansu su bibiyu, kashi 16 cikin 100 ne kawai na jimina suke tarayya fiye da bibiyu.
  • Mazajen jimina suna da turakarsu da suke zama su kaɗai, kuma tana iya bambanta daga murabba’in kilomita 2 zuwa 20.
  • Kamar yadda jimina suka more da ƙarfin gani, haka kuma suna da kyakkyawan kunnen jin sauti.
  • Ƙafafun jimina suna iya motsawa gaba ne kawai, wato ba sa iya yin tafiya ta baya.
  • Jimina na ɗaya daga cikin nau’in tsuntsaye masu tsawon rayuwa, suna iya rayuwa har tsawon shekaru 62.
  • Dabbar da za a iya kwatantawa da gudun jimina ita ce barewa. Dalilin haka ya sa barewa ce ke iya yin nasarar farautar jimina.
  • Duk da yawan jimina ya ragu sosai a cikin shekaru 200 da suka gabata, har yanzu tana mamaye da kusan mil 3,800,000.

Manazarta

Dickson, S. (2024, August 16). A guide to different Ostrich species: unique characteristics and commercial significance. Superior Ostrich.

HowStuffWorks. (2024, May 28). Ostrich Facts. HowStuffWorks

NATURE, PBS. (2021, September 27). Ostrich Fact Sheet | Blog | Nature | PBS. Nature.

The Editors of Encyclopaedia Britannica. (2025a, January 3). Ostrich | Habitat, Food, & Facts. Encyclopedia Britannica.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×