Skip to content

Kawaici

Kawaici na nufin kawar da kai. Kawar da kai kuma a Hausance shi ne idan aka yi wa mutum laifi ka ƙi yin magana kuma ba tare da kana jin haushin wanda ya yi maka laifn ba. Misali, kamar a ce mutum ya zo gabanka ya aikata wani abu da ya san baka so, a nan sai ka yi kamar baka gan shi ba. Sannan kuma ya zama baka ji haushinsa ba, baka kuma ƙudurce cewa sai ka rama a gaba ba. Wannan shi ne kawaici. Shi ma wannan hali haƙuri ne yake haifar da shi.

Wasu masanan kuma sun bayyana kawaici da alkunya ko kau-da-kai ko haƙuri ko shiru-shiru. Malam Bahaushe yana ɗaukar kawai da mutum ya hana ransa abin da yake so a gaban wasu mutane na musamman. Haka kuma yana iya zama kawaici mutum ya ƙi yin abin da ya kamata ya yi a gaban wasu ko ga wasu ko da kuwa hakan zai cuta masa.

Tausayi da son mutane ko kuma gudun ɓacin ran mutane yake sa wasu ƙin aikata abin da ya kamata su aikata. Bahaushe yana kallon wannan tunani a matsayin abin sha’awa. A tunaninsa hana kai wani ya amfani ba wata matsala ba ce. Wannan ya sa yake ƙyamar mutane masu halin ɗan tsako wanda da ya samu sai ya guji danginsa. Ɓangaren al’amurran da suka shafi kawar da kai kuma, irin wannan ɗabi’a ta tabbatar da rayuwar Hausawa na son zaman lafiya a koyaushe da mutane wanda suka ce ya fi zama ɗan sarki.

Abubuwan da kawaici ya ƙunsa

Akwai misalai da yawa da za a iya bayarwa waɗanda za su ƙara fayyace abin ɗabi’ar kawaici ta ƙusa baya ga ma’anonin da suka gabata. Ga wasu misalai kaɗan daga ciki musamman don su wakilci sassa daban-daban na abin da Hausawa suke nufi da kawaici.

  • Rashin nuna damuwa idan an yibwa mutun laifi don kawai kada ran wani ya ɓaci.
  • Rashin yin magana ko surutu a inda mutum yake ganin bai dace ba ko a gaban wasu mutane na musamman.
  • Kasa bayyana ra’ayi ga abin da mutum ke so musamman a gaban wasu mutane.
  • Haƙura da abin da mutum ya kamata ya samu idan wasu sun nuna ra’ayinsu bisa tunanin ba zai ishi kowa ba ko kuma su sun fi cancanta su samu.
  • Ƙin cin ko shan wani abu da mutum ke so don tunanin wani makusancin mutum ya fi ka son shi.
  • Haƙuri da kawar da kai idan a ci hakkin mutum saboda a zauna lafiya ko don kada ran wanda ya ci hakki ya ɓaci.
  • Ba wa mutane dama su fara gabatar da ra’ayinsu a kan abin da mutun ke matuƙar so ko da a ƙatrshe shi zai rasa ko kuma ya sami mara inganci.
  • Shiga cikin ƙunci don kawai wani ya ji daɗi.
  • Ƙanƙan da kai da rashin nuna iyawa a gaban wasu mutane.

Mutanen da ke yin kawaici

Hausawa ba su da wani rukuni na mutane da suke yin kawaici. ɗabi’a ce da ke shiga jinin mutane sannu a hankali su tashi da ita har su tsufa da ita. A wasu lokuta, irin kyakkyawar tarbiyar da mutum ya samu na rashin kwaɗayi ko rashin son fitina shi ke masa jagoranci wajan zama mai kawaici.

Sakamakon kawaici

Kasancewar kawaici kyakkyawar ɗabi’a ga Bahaushe, akwai abubuwa da yawa masu fa’ida da ke tattare da mutanen da suka mallake ta. Daga ciki akwai:

  • Kasancewar mutum ya ɗabi’antu da kawaici yana sa ya samu wata alfarma daga mutanen da za su ta sha’awar ɗabi’arsa da tausaya masa. Daga cikin irin wannan alfarmar akwai aure da ragowa da shugabanci da dai sauransu.
  • Kawaici yana sa mutum kauce wa shiga cikin duk wata fitina. Da ma rashin kunya ko rashin kau da kai ko rashin haƙuri su ke haddasa shiga cikin fitina. to da zarar babu su an zauna lafiya.
  • Idan mutum yana da kawaici, zai kasance mai ƙima a idon mutane saboda ya kawar da kansa daga kwaɗayi ko sa ido a kan abin mutane. Mutum na zama abin sha’awa ga mutane.
  • Mutum mai kawaici yana samun kyakyawar shaida daga mutane. A duk lokacin da aka zo binciken wani zargi ko laifi, to yakan samu shaida mai kyau na rashin samun hannunsa a lamarin ta la’akari da ɗabi’arsa ta kawaici. Galibi akan ce, ‘mun san halin wane ba zai iya aikata haka ba.’

Illolin kawaici

Kamar yadda kawaici yake da amfani ga mai ita da ma al’uma gaba ɗaya, to akwai wasu illoli da ke tattare da ita musamman idan ta yi yawa. Ga kaɗan daga ciki:

  • Kawaici na sa mutum ya ƙi cin wani abu da rai ke so bisa tunanin wani makusanci shi ma yana so.
  • Kawaici idan ya yi yawa yana tauye wa kai da zuri’a ’yanci. Mutum yakan bar abin da bai kamata ya bari ba ta yadda har zuri’arsa sai sun cutu. Wannan ke sa wasu ke kallonsa da wauta.
  • Tsananin kawaici yana tauye wa mutum damar da al’ada da addini suka ba shi na gudanar da wasu al’amurra, kamar kasa yin mu’amala da wasu mutane da ba a haramta wa mutum ba. Misali, irin kawaicin da akan samu na kasa mu’amala ta kai tsaye da ’ya’yan da aka haifa.

Manazarta

A. I. da Gusau, S. M. (ed) (2010). Al’adu da ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El–Abbas Printers & Media Concept.

Aminu, M. (1978). Ma’anonin Ɗabi’un Hausawa. Kano: Aminu Zinariya Recording & Publishing Co.

Haushi, B. M. B. (n.d.). Hausa da Hausanci a Karni na 21 – Kalubale da Madosa.

Sa’id, B. da Wasu (ed) (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Yahaya, I. Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press PLC.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×