Skip to content

Kayan mata

Kayan mata, hakin maye ko kayan da’a kamar yanda wasu ke kiransu, jerin magunguna ne daga nau’in tsirrai, itace, ganyeyyaki, yayan itatuwa, bawon itace da kuma jijiyoyi har da sassan dabbobi irin su Ayu, tantabara, zakara da sauran su. Ana sarrafa su ne ta hanyoyi daban daban. Mata na amfani da su hakin maye din ne don kara karfin sha’awa da ni’ima a tsakanin su da mazajensu.

Wasu na amfani da su kayan ne don kar a karo musu kishiya ko kuma don mazajensu kar su bi matan banza a waje, wanda wasu ke ganin suna juya mazajensu son ransu a dalilin amfani da wadannan kaya.

Yanayin al’ada ta Arewacin kasarmu yasa ba kasafai ake tattauna maudu’i da ya danganci irin wannan bangaren ba, sai dai ya zama wajibi a cire kunya wajen ganin an ilmantar da mata yanda za su yi amfani da wadannan kayan ba tare da sun cutar da kansu ba sun kuma cutar da mazajensu saboda akwai karancin sani a kan wannan fannin wanda da dama ke fadawa ga halaka.

Su dai wadannan kaya an raba amfanin su ne zuwa fannoni da dama, a bangare guda kuma ana ba su sunaye ma bambanta daidai da irin aikin da suke yi a jikin mace ko namiji. Wasu akan ce dasu uku bala’i, idona idonka, kudi gida ko mota da dai makamantan su.

A wannan zamanin da muke ciki yawaitar wadannan kayayyaki sun yi yawa a kasuwanni, wanda musamman idan ka shiga kasuwa akwai jerin shaguna reras wadanda ake saida wadannan kaya, wani fannin kuma mata ke siyarwa a cikin gidajensu yayin wata hidima ko taro na mata.

A lokuttan baya an fi samun hakin maye a yankin SOKEZA wato Sokoto, Kebbi da Zamfara, har ta kai mata kan yi dar-dar a duk lokacin da aka ce wacce mijinsu zai auro daga wannan yankin take.

 A wannan zamanin da muke ciki akwai yawaitar masu saida wadannan kaya musamman ma shigowar kafafen sadarwa inda za a samu shafuka da aka bude musamman don sayar da wadannan kayan da’a.

Mafi a kasari wadanda suka fi sayar da kayan mata sune; matan aure, zawarawa, maza a shaguna da kuma kalilan daga cikin yan mata.

Wadannan kaya na da nasu alfanun idan an yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Duba da zamani abin sai ya sauya zani, ya zamo shirka ta shigo cikin wadannan kaya.

Binciken da hukumar (Nigerian Journal of Basic and Clinical Sciences) su ka gabatar a Kano, sun tabbatar da cewa a bincikensu kaso hamsin da uku da digo tara (53.9%) na amfani da kayan mata dan karin ni’ima. Sai dai ta wani bangaren kuma an samu kaso talatin da bakwai da digo uku (37.3%) wadanda suka samu matsaloli a sakamakon amfani da wadannan kayan da’a, inda wasu daga ciki ke fama da ciwon mara, zubar ruwa masu wari da kuma kaikayin gaba.

Dama dai wadannan kaya an kasa su ne a kan yanayin amfanin su. Akwai na sha, na wanka, na turara gaban mace da kuma wanda suke kira da dan matsi wanda a turance a ke kira da (insertives).

 Da yawan mata ba su duba yanayin magungunan da kuma hannun wa suka saya, su dai matukar an ce wannan kayan mata ne to shikenan bukatarsu ta biya.

Wanda a yanzu masu kayan mata sun fi kowa ciniki saboda yawaitar masu bukatar kayan wanda idan da za a kulla ruwa a ce maganin mata ne babu ko shakka mata za su yi rububin saya.

Matsala ce babba da ta tunkaro Arewacin Nijeriya duba da yanda iyaye su ka fi maida hankali wajen dinkirawa yarinya budurwa da zata yi aure kayan mata. A bayyane ana nuna mata babu komi a cikin aure face saduwa tsakanin mace da namiji wanda suna cikin ababen da ke jawo matuwar aure a yau.

Yarinya ba ta san komi ba face kwanciya da miji saboda ita ce turbar da aka dora ta a kai kafin tayi aure.

Masana kimiya akan ‘Natural Products’ sun tabbatar da cewa da yawan maza da ke fama da lalurar mutuwar barin jiki ko yawan kasala ya samo asali ne a sakamakon kayan mata, wato aphrodisiac, da mata ke sha ko su zuba ma mijin a abinci ko abin sha saboda yana kara ma shi karfi da kuma dadewa a lokacin saduwa fiye da lokacin da yake yi na asali wanda hakan ke illatar da kuma raunatar da sexual hormones din sa. Da hankali wannan gubar na taruwa a jikinsa har ta zama illa a gare shi.

Su ma matan suna samun nasu illolin musamman ma masu amfani da kayan mata da ake cewa su yi matsi da shi a gaban su, hakan babbar illa ce ga wurin. Saboda sensitive wuri ne da bayan tsabtataccen ruwa baya bukatar komi, a bu kadan ka iya sa hayayyafar kwayoyin cuta na halitta saboda danshin da wajen ke da shi. Daga nan ne mafi yawa ke kamuwa da cutar daji ta mahaifa, ciwon sanyi da sauran cututtuka da ke da alaka da wajen.

Likitocin da ma’aikatan lafiya na korafin yanda suke samun matsaloli na mata da su ka danganci illolin amfani da kayan mata da ake yi. Wasu har ya kan jawo musu da warin gaba sakamakon cushe-cushe da suke yi marasa dalili, wadanda basu san yanda a ka hada su ba da yanayin tsabtar su.

A mafi yawan lokutta likitoci sun fi bada shawarar amfani da ganyayyaki da kuma yayan itatuwa in dai ni’ima ake nema ba tare da cutarwa ba, musamman irin su rake, kankana, zogale, madara da kayan dake gina jiki.

Cin abinci mai tsabta da inganci da ya kunshi duka sinadaran da ake bukata a abinci (balanced diet) sukan taimaka wajen karawa mace ni’ima, su kuma karawa namiji karfi.

Ga sakamakon zantawar sirri da na yi da mata daban daban a kan yanda suke ganin tasirin kayan mata da kuma illolin da yayi ma wasu daga ciki.

“Gab da bikina a ke ta hada mun magunguna iri-iri, wata mata a ka dauko daga Sokoto ita ke kula da ni na tsawon wata daya. Tana ba ni na sha da madara, da zuma da na yin turare da makamantan su. Yanzu haka shekara ta hudu da aure babu haihuwa saboda wata matsananciyar ciwon mara dake damu na wadda kafin in yi aure ban taba experiencing hakan ba. Bincike ya tabbatar da ina fama da infection ina dai kan magunguna har yanzu “.

“Ni duk lokacin da zan yi amfani da kayan mata na kan duba yanda a ka yi su sannan ba kowane nake sha ba, don ba zan ce ban sha ba amma gaskiya sai na tantance wanda ke da kyau ba zai kawo mana illa ba”.

“Na taba amfani da kayan da’a sau daya wanda ya jawo mun amai da gudawa ba sassauci. Tun daga lokacin ko ba ni aka yi kyauta sai na bayar da shi. Nafi gane ma amfani da kayan marmari, sannan ina hadawa da kaina in sha. Nafi gamsuwa fiye da tunaninki. Ko lafiya ma nafi samu,saboda abubuwa ne da jiki ke bukatar su”.

A gefe guda kuma na ji ta bikin wata baiwar Allah da ke sana’ar hada kayan mata.

“A gaskiya na kan yi kokari wajen ganin na tsabtace kayana. Sannan ina amfani da itatuwa masu amfani wadanda aka san amfaninsu a irin wannan fanni. Magungunan kadai nake hadawa, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Da wuya in ji wata ta kawo koken cewa ba ta samu gamsuwa ba. Sannan na kan kauracewa bin malaman tsibbu kamar yadda wasu masu magungunan ke yi. A na hada na mallake miji gaba daya”.

“Na je har Nijar neman maganin mata a lokacin da mijina ke neman aure. Akwai wata mata da ke bada maganin da sai da aka tsaga fatata sai ta zuba maganin ta goge shi kuma wannan jini yake bi, mijin ki bai kara jin dadin wata mace bayan ke. Na san bai da kyau hakan amma ba yanda zan yi bana son abinda zai rabi mijina. Shi ya sa duk inda naji ana bada maganin mata na mallakar miji ina zuwa. Sai dai Allah ya yafe mana”.

A kowane bangare mun ji yanda wasu ke amfani da shi kuma su dace, wasu kuma a dalilin hakan ya jawo musu matsala.

Na ji ta bakin mai hadawa da ta bayyana cewa akwai wadanda ake yi musu dauke da sihiri. Inda ta dayan bangaren kuma mun ji wadda da kanta ta bayyana yadda ta yi amfani da irin wadanda ko a addinance an yi hani da irin su.

Ya kamata mata su farga su gyara wannan dabi’arsu ta amfani da kowane irin magani don neman karin ni’ima da kuma mallakar miji. Wanda mafi akasari suna tsoron kishiya ne ko a ce mijinsu na neman mata a waje.

Maza na bada ta su gudunmuwar wajen yawaitar masu sayar da kayan mata. Za mu ji ta bakin mazan, da kuma shin ko hakan na gamsar da su ko kuwa a’a? Ku biyo ni a Makala ta gaba.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×