Keken ɗinki na’ura ce ko kuma wanda ake amfani da shi don ɗinke tufafi da sauran kayan da za a iya ɗinkewa ta hanyar amfani da zaren ɗinki. An ƙirƙiro keken ɗinki tun a lokacin samuwar masana’antu na farko don rage adadin ɗinkunan da ake yi da hannu a masana’antar sarrafa tufafi. Tun da aka ƙirƙiro shi, ya inganta tare da bunƙasa masana’antar tufafi da ta allura.
Bangarorin daban-daban na keken dinki da ayyukansu suna taimaka wa mutane wajen sanin aikin keken ɗinkin. Akwai nau’ikan keken ɗinki iri-iri da ake amfani da su wajen ƙera tufafi daban-daban. Keken dinki yana sarrafa tufafi da tallafawar wasu na’urori a jikinsa kuma yana samar da ingantaccen ɗinki. Yana yana da sassa daban-daban da abubuwan da aka maƙala, kowannensu yana da nasa mahimmanci da amfani. Akwai nau’ikan nau’ikan keken dinki guda biyu wato, keken ɗinkin na amfanin cikin gida da kuma keken dinkin amfanin masana’antu.
Masu amfani da keken ɗinki ya kamata su samu ilimi da ƙwarewa don sarrafa nau’ikan kekunan ɗinki. Yana da kyau su san nau’ikan wannan na’urar ta keken dinki da sassanta da ayyukansu, abubuwan da suke makale da kuma sharuddan da suka shafi ɗinki.
Rabe-raben ɗinkuna
Kafin a kirkiro na’urar da za a iya amfani da ita wajen ɗinki, ana dinka komai da hannu. Yawancin yunƙurin farko da mutane suka yi, sun gwada maimaita wannan hanyar ɗinkin ta hannu amma galibi an gaza samar da abin da ake bukata. Siffar ƙarshe ta kowane tufafi ko abin ɗinkawa ta dogara da yadda aka haɗa ɓangarori daban-daban ta hanyar ɗinki. Duk wani karkace-karkace a jikin ɗinkuna yana haifar da rashin kyau. Don haka, dole ne a yi taka-tsantsan.
Ana iya rarraba ɗinki gabaɗaya zuwa kashi biyu, ɗinkin hannu da ɗinkin inji (na keke). Ana iya yin ɗinkin hannu a yi amfani da shi don dalilai na wucin-gadi ko wasu lokuta, ana iya amfani da shi don wasu dalilai na musamman kamar yin beza, ko saka maɓalli, ko saƙar ɗinkin bargo, da sauransu.
Babban manufar samar da keken ɗinki ita ce a haɗa kyallaye guda biyu ko fiye a ɗinke ta amfani da zare da allura. Keken ɗinki na rage yawan ɗinki da hannu wajen shirya tufa ko wani abu. Kekunan ɗinki suna taimaka wa mutane wajen yin aikin cikin sauri, da kuma yawa akai-akai.
Tarihin ƙirƙirar keken ɗinki
An kirkiro keken ɗinki ne a shekara ta 1790 daga wani mai ƙirƙire-ƙirƙire ɗan ƙasar Ingila, mai suna Thomas Saint, sai dai kuma ya kasa tallata abin da ya ƙirƙiro ɗin ga duniya. Ya ƙera wani abu mai tsini da katako don yin ramuka a jikin tufa mai kauri, domin allura da zare guda ɗaya su shiga ƙarƙashin tufar su riƙa ƙulla zaren ta yadda zai tafi kamar sarƙa. Josef Madersperger ya fara bunƙasa keken dinki a shekarar 1807 inda ya gabatar da shi a shekarar 1814. John Greenough shi ne ya fara ƙera keken ɗinki na farko a Amurka a shekara ta 1842. Elias Howe ya ƙirƙiro keken ɗinki a 1845.
Gano na’urar ɗinki da sauri ya bazu kamar wutar daji, da farko ana sayarwa ga masana’antun tufafi ta yadda za su iya ɗinka tufafi manya a kan sikeli mafi girma. A cikin shekarun 1860s, an samu saurin shaharar kekunan ɗinki a tsakanin rukunin mutane masu matsakaicin hali. Daga baya a shekara ta 1889, aka kera kekunan ɗinki wanda ke amfani da wutar lantarki. Da farko, waɗannan kekunan na amfanin yau da kullun ne waɗanda aka haɗa da wata na’urar lantarki a gefe. Sakamakon cigaban da ya samu na faɗaɗa wutar lantarki a cikin gidaje, waɗannan kekunan ɗinki sun shahara sosai. Sabbin abubuwa na baya-bayan nan sun haɗa da ƙarin damar yin ingantattun sifofin ɗinki. A cikin karni na ashirin da daya, kamfanonin ƙera kekunan ɗinki sun ƙera nau’ikan kekunan da ake amfani da su daban-daban a fasahohin dinki sannan akwai kekunan ɗinki na na’ura mai ƙwaƙwalwa da kekunan yin kwalliya da ado da kuma kekunan ayyuka na musamman duk an ƙera su. Sabbin kekunan ɗinki suna da allon telebijin wato LCD da na’urar microprocessors, da fonts ɗin da aka aka tsara.
Nau’ikan kekunan dinki
Wadannan su ne manyan nau’ikan kekunan ɗinkin.
• Keken ɗinkin amfanin gida
An tsara waɗannan kekunan musamman don mutum ɗaya ya hau dinka riguna ɗaya yayin amfani da nau’in ɗinki ɗaya. An tsara wadannan kekunan ɗinki na zamani ta yadda tufafi ke shiga da fita cikin na’urar a sauƙaƙe ba tare wata matsala ba, an tsara su ta yadda za su hanzarta aikin dinkin da kuma rage bata lokaci da taƙaita gajiya ga mai aiki. Wasu muhimman abubuwan da ake amfani da su na kekunan dinkin gida su ne kamar haka:
- Ana amfani da wannan a cikin gidajen masu sha’awar ɗinki a matsayin sana’a.
- Waɗannan su ne kekunan da mutane da yawa ke amfani da su a ayyuka daban-daban don sarrafa sutura, da kuma ɗinke-ɗinken abubuwa masu sauƙi a gida.
- Ta hanyar sauye-sauye ƙanana, waɗannan kekunan ɗinki na iya yin nau’ikan ɗinki iri-iri.
- Kekunan ɗinkin gida yawanci suna aiki a kan yadudduka marasa nauyi ko kuma aiki marar yawa sosai.
- Waɗannan kekunan ɗinki suna aiki a kan ƙananan tufafi idan aka kwatanta da na kekunan ɗinkin masana’antun sarrafa tufafi.
• Keken ɗinkin masana’antu
Keken dinki na masana’antu nau’i ne na keken ɗinki mai nauyi, ƙarfi da kuma girma. Ana amfani da shi wajen sarrafa tufafi da sauran abubuwa masu alaƙa.
- Ana amfani da keken ɗinkin masana’antu don samar da tufafi da yin ɗinkuna da yawa.
- Waɗannan kekunan ɗinki ne masu nauyi da sauri waɗanda ke ɗinka dubunnan kaya a cikin minti ɗaya.
- Keken ɗinkin masana’antu yana da kyau sosai kuma yana da babbar na’urar da ke juya shi cikin sauri tare da samar da sakar ɗinki mai ban sha’awa..
- Kekunan ɗinkin masana’antu an tsara su ne don yin aiki guda ɗaya na musamman a jikin tufafin.
- Wasu kekunan ɗinkin masana’antu an tsara su don yin aiki mai nauyi fiye da wanda aka saba gani.
- Yawanci, samar da ɗinkuna masu yawa yana buƙatar keken ɗinkin masana’antu, wanda aka ƙera don ɗinka kayan masu nauyi da sauri, kamar fata da kakkauran yadi da dai sauransu.
- Kekunan ɗinkin masana’antu na da sunaye bisa ga aikin da suke yi. Sunayen nau’ikan kekunan ɗinkin masana’antu sun haɗa da pocket setter, buttonhole, da programmable pattern sewers, da sauransu. Misali, keken ɗinkin masana’antu na pocket setter na iya ɗinka aljihu guda 2,000 a cikin awanni takwas na aiki.
- Kekunan ɗinkin masana’antu na musamman na iya samar mafi kyawun ɗinki.
- Kekunan dinki na masana’antu sun fi girma da sauri da rikitarwa, kuma sun bambanta a girmansu da farashi da kuma ayyukansu.
Ire-iren kekunan ɗinki
Akwai nau’ikan keken daban-daban amma galibi, ana la’akari da guda uku kamar yadda aka bayyana daga ƙasa:
- Mechanical sewing machines
- Electronic sewing machines
- Computerised sewing machines
1. Mechanical sewing machine
Wadannan kekunan ɗinkin ba su da tsada kuma su ne nau’in keken ɗinki mafi sauƙi ta fuskar gini. Su ne kekunan ɗinkin da ake aiki da hannu da kuma ƙafa wajen sarrafa su.
• Keken ɗinkin hannu
Keken dinki mai sarrafuwa da hannu na siffofi kamar haka:
- Wannan shi ne mafi sauƙi nau’i na keken ɗinkin amfanin gida wanda ake sarrafa shi da hannu.
- Yana da mariƙa a jikin mawanin keken wanda ake amfani da shi don sarrafa keken.
- Keken dinki mai aiki da hannu mafi akasari ana amfani da shi don dalilai na gida da ayyuka masu sauƙi kamar yadda ba ya aiki da sauri.
- Wannan keken ɗinki ya dace da wuraren da babu wutar lantarki.
• Keken dinkin ƙafa
Keken dinki mai sarrafuwa da ƙafa na siffofi kamar haka:
- Wannan keken ɗinki shi ma daidai yake da a keken dinki mai sarrafuwa da hannu, amma shi ana sarrafa shi ne da ƙafafu, yana teburi tsayayye wanda ke haɗe da keken.
- Yana da igiya da ake daurawa daga jikin mawanin keken zuwa ga abin da ake takawa da ƙafa don tuka keken ko kuma juyawa ta yadda allura za ta riƙa huda tufafi ta ƙulla zare.
- Waɗannan kekunan suna gudu da sauri fiye da waɗanda ake sarrafawa da hannu.
- Shi ma wannan nau’in keken ɗinki ya dace da wuraren da babu wutar lantarki.
- Lokacin da ake gudanar da ɗinki da wannan keke, mutum yana da damar yin amfani da hannayensa guda biyu wajen sarrafa tufafin ta duk yadda yake so. Saboda haka wannan yana hanzarta aikin ɗinki.
2. Keken ɗinki na lantarki
Waɗannan kekunan ɗinki sun zama sanannu a shekarun 1970s. Akwai ƙarin abubuwa da yawa a jikin keken ɗinki na lantarki fiye da wanda ake sarrafawa da hannu ko da ƙafa. Wasu daga cikin siffofin wannan keken ɗinki su haɗa da:
- Waɗannan kekunan dinki suna gudu da sauri fiye da kekunan da ake sarrafa su da hannu.
- A jikin kekunan ɗinkin lantarki, bangaren mawanin keken yana haɗe bel, wanda ke makale da injin lantarki.
- Akwai na’ura (motor) mai juyawa guda daya tana makale da keken dinkin kuma wannan na’ura ita ke sarrafa allura da gudun zare.
3. Keken ɗinki na kwamfuta
Waɗannan kekunan ɗinki suna da sauri sannan kuma suna da takamaiman aikin da ake yi da su. Waɗannan kekunan ɗinki suna kama da na’urorin ɗinki na lantarki. Sai dai shi wannan keken ɗinki na kwamfuta yana aiki tare da taimakon wasu manhajohi (software) daban-daban.
Kekunan dinki na kwamfuta suna ba mai aiki damar daidaita ayyukan daidai da bukatun ɗinki. Keken dinki na aiki yadda ya kamata wajen tsarawa da dinke sassa daban-daban na tufafi kamar hannun riga, aljihu, da sauransu. Waɗannan kekunan ɗinki masu sauri suna da allon talebijin (LED) ko allon LCD ko kuma allon taɓawa. Kekunan suna aiki da yawa kuma suna da tsada.
Manazarta
Akhamzadeh, D. (2023, April 14). The complete history of a sewing machine. goldstartool.com.
Cloé. (n.d.). What are the main types of sewing? The Superprof Blog – UK.
Lo, S. (2022, June 29). Who invented the sewing machine? History, facts & scandals revealed. Contrado Blog.