Skip to content

Kurkunu

Cutar kurkunu wacce ake kira a Turance da Guinea worm ko Dracunculiasis, cuta ce da ba kasafai ake watsi da ita ba a yankuna masu zafi wadda ke shafar al’ummomin ƙauyuka da matalauta masu ƙaramin ƙarfi a sassan Afirka. Mutane suna kamuwa da cutar bayan sun sha gurɓataccen ruwa ko cin kifin da ba a dafa shi sosai ba ko kuma wasu dabbobin ruwa. Bayan kamar shekara guda, ƙwayar tsutsar da ke yaɗa cutar takan ratsa fata, ta haifar da ƙaiƙayi, alamar konewa, sau da yawa a kan ƙafafu ko ƙafafu.

mogos 34 wide f11ccfdd741d398c485aa4f73b3399bc948ac02a
Ma’aikacin lafiya ne ke fitar da tsutsar da ke haifar da cutar kurkunu daga ƙafar wani mutum a yakin Sudan.

Ciwon da yanayin ke haifarwa na iya zama mai rauni, kuma da yawa takan bar masu ɗauke da ita da naƙasu na tsawon rayuwarsu. Abin farinciki a nan shi ne, yadda al’umma ke ƙoƙari a duk faɗin duniya na ganin an kawar da cutar.

Alamomin cutar kurkunu

Mutanen da suka kamu da kurkunu ba sa bayyanar da wata alama sai kusan shekara guda bayan kamuwa da cutar a karon farko. Sai lokacin da ƙwayar tsutsa ta kusa fitowa daga fatar jiki, mutane suke fara jin ciwo. Alamomin cutar kurkunu na iya haɗawa da:

  • Zazzaɓi
  • Tashin zuciya da amai
  • Zawo
  • Ƙarancin numfashi
  • Ƙonewa, ƙaiƙayi, zafi, da kumburi a inda ƙwayar cutar ke cikin jiki (sau da yawa ƙafafu da ƙafafu)
  • Kumburi a inda tsutsar ko ƙwayar cutar ke lalata fata

Cutar kurkunu ba ta fiye kaiwa ga mutuwa ba, amma tana iya haifar da matsaloli masu tsanani, nakasar rayuwa, da kashe kuɗaɗen jinya ga waɗanda abin ya shafa. Ciwon da ke tattare da shi sau da yawa yana da tsanani, yana da wuya mutane su yi aiki, zuwa makaranta, ko kula da kansu ko wasu. Wannan yana ɗaukar matsakaicin lokaci na tsawon makonni 8.5, kodayake naƙasa ta rayuwa ta zama gama-gari.

Idan babu ingantaccen magani, raunukan da ƙwayar tsutsa ke haifarwa na iya kamuwa da ƙwayoyin bakteriya, wanda ke haifar da sepsis, maɓuɓɓugar cututtuka, da ƙwayoyin cuta masu illa ga sassan jiki da gaɓoɓi. A wasu lokuta, waɗannan cututtuka sukan zama masu haɗari ga rayuwa.

Yadda ake kamuwa da cutar kurkunu

Cutar kurkunu tana faruwa ne ta hanyar wata ƙwayar halittar tsutsa mai suna Dracunculus medinensis, wadda aka fi sani da Guinea worm. Yadda tsutsar ke shiga cikin jiki da kuma sa mutane rashin lafiya abu ne mai rikitarwa, kuma duk yana farawa a cikin ruwa.

Waɗannan ƙananan halittun ruwa (wanda aka fi sani da copepods ko water fleas) suna rayuwa a cikin ruwa marar kyau kuma suna cin ita tsutsar da ake kira Guinea worm larvae. Idan suka ci tsutar, larvae ɗin za su fuskanci canje-canje wanda bayan makonni biyu sun zama masu cutarwa ga lafiya.

Lokacin da mutane suka sha ruwan da ya gurɓata da wannan ƙwayoyin cutar, su (ƙwayoyin cutar) sukan sakin tsutsa a cikin sashin narkewar abinci na jikin ɗan’adam. A can, suna bi ta cikin wanda ya kamu da cutar t sashen hanji, daga ƙarshe su kai ga tantanin da ke ƙarƙashin fata (skin tissues).

Bugu da kari, an gano cewa mutane na iya kamuwa da cutar kurkunu ta hanyar cin wasu dabbobin ruwa (kifaye ko kwaɗi). Waɗannan kifaye ko kwaɗi cutar ba ta shafar su amma suna iya ɗaukar cutar su yaɗa.

Larvae na zama a cikin jiki na kusan shekara guda yayin da suke girma su zama tsutsotsi manya. Manya matan tsutsotsin na iya girma zuwa kusan inci 24-39 (kimanin santimita 60-100) a tsayi. Bayan saduwar jima’i, tsutsar takan ɗauki hanyar zuwa fata, tana haifar da rashin jin daɗi na jiki.

Kumburi mai ƙaiƙayi da alamar konewa na iya zama mai tsanani ta yadda mutane ke gaggawar nutsar da sashin da ya kamu da cutar a cikin ruwa don samun sauƙi. A duk lokacin da haka ta faru, babbar tsutsa ta mace takan fasa fata don fitar da tsutsotsin da ba su balaga ba su koma cikin ruwa mai daɗi, don sake zagayowa gabadaya. Bayan kamar mako biyu zuwa uku, macen ta ƙare fitar da tsutsa, kuma a ƙarshe ta mutu ta lalata fatar wajen idan ba a cire ba.

Cutar dai ta fi faruwa ne a lokutan damina, tana yawan ɓullowa a lokacin damina ko rani, ya danganta da wurin, kuma ba ta yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.

Gwajin cutar kurkunu

Ana gano cutar kurkunu ne ta hanyar gwajin jiki mai sauƙi. Ma’aikatan kiwon lafiya sukan binciki fata, ƙwayayen. tsutsotsi da ke haɗuwa a cikin kumburin da zarar wurin da abin ya shafa ya nutse a ruwa. A halin yanzu babu wani gwajin gano cutar da za a iya gano waɗanda suka kamu da cutar kafin bayyanar cututtuka.

Maganin cutar kurkunu

Kamar yawancin cutuka a yankuna masu zafi da aka yi watsi da su, babu magani ko takamaiman maganin magance cutar kurkunu. Magunguna irin su de-worming da aka yi amfani da su don wasu cutuka na halittun parasitic ba sa aiki don magance cutkan kurkunu ba ko hana bayyanar alamomin cutar. Madadin haka, kulawa yawanci ta ƙunshi cire ƙwayoyin tsutsar ta hanyoyi kamar haka:

  • Ana nutsar da sashin jikin da ya kamu da cutar a cikin ruwa don lallasa tsutsar ta kara lekawa daga raunin.
  • Ana tsaftace raunin da yankin da ke kewaye da shi don hana yaɗuwar cutar.
  • Ana buƙatar kyakkyawar kulawa don kada a watsa cutar, a nannaɗe ƙwayoyin tsutsar da aka fitar a cikin tsumma. Wannan yana hana su komawa cikin jiki.
  • Akan maimaita wannan tsari kowace rana na tsawon kwanaki ko makonni har sai an fitar da tsutsotsin daga ƙarshe.
  • Ana iya ba da magunguna irin su ibuprofen don rage kumburi da kuma rage raɗaɗin da ke ciki. Haka nan ana iya shafa man shafawa na maganin ƙwayoyin cuta a wuraren da abin ya shafa don hana yaɗuwar cutar.

Hanyoyin riga-kafi

Babu wani maganin allurar riga-kafi game da cutar kurkunu, amma ana iya kawar da cutar gabaɗaya ta hanyar tabbatar da tsaftataccen ruwan sha tare da daƙile manya tsutsotsin da ke haifar da yaɗuwar cutar.

Hanya mafi kyau ta riga-kafin kamuwa da cutar ita ce shan ruwa kawai daga wuraren da ba su gurɓata ba, kamar rijiyoyin da aka haƙa da hannu da rijiyoyin burtsatse. Yawancin al’ummomi da cutar kurkunu ta shafa, ba su da tsaftataccen ruwan sha. A irin waɗannan lokuta, kowane ruwan da ake amfani da shi don sha ko dafa abinci ya kamata a tace shi.

Kwayoyin da ke ɗauke da cutar kurkunu sun yi ƙanƙanta ainin, ba za a iya ganin su ba sai tare da taimakon gilashin ƙara girman abu, amma suna da girman da za a iya cire su cikin sauƙi daga ruwa ta amfani da hanyar tacewa.

1130 shutterstock 1722895630
Nau’in tsutsar da ke haifar da cutar kurkunu.

Haka nan za a iya maganin cutar daga maɓuɓɓugar ruwa ta hanyar amfani da sinadarin magani kashe copepods. Domin kare kayan ruwan sha, waɗanda ke da ƙuraje ko kuma aka cirewa  tsutsotsi a wani yanki na jikinsu ya kamata su nisanta daga wuraren da ake ajiye ruwan sha.

Abubuwan da za a kula da su

Kifi da sauran halittun ruwa da ke fitowa daga wuraren da za a iya gurɓata ruwansu su ma ana buƙatar a dafa su sosai kafin a ci. Wani lokaci waɗannan dabbobin suna cin halittun copepods masu kamuwa da cutar. Dafa namansu sosai zai kashe tsutsotsin da ke ɓoye a ciki. Dabbobin gida, irin su karnuka, bai kamata a ba su kifin da ba a dafa ba.

Mutane na iya kamuwa da cutar kurkunu sau da yawa a tsawon rayuwarsu. Al’ummomin da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar dole ne su ci gaba da yin taka-tsantsan har sai an kawar da ƙwayoyin cutar a hukumance daga doron ƙasa.

Gangamin kawar da cutar daga doron ƙasa

Cutar kurkunu ta shafe dubban shekaru a duniya, amma yanzu tana gab da ɓacewa. An sami rahotan bullar cutar har guda 30 a cikin shekarar 2017, ta ragu da kashi 99.9% daga sama da  miliyan 3 a shekarar 1986. Har ila yau, a cikin shekarar 2023, an sami wani rahoton bullar cutar har guda 14 a cikin mutane. A waccan shekarar, an gano cutar a ƙasashe ƙalilan kawai waɗanda suka haɗa da: Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chadi, Mali, da Sudan ta Kudu.

Wannan raguwar yaɗuwar cutar ya samo asali ne saboda ƙoƙarin da Cibiyar Carter da sauran abokan hulɗa na duniya suka jagoranta a cikin shekarun 1980. Tun daga wannan lokacin ne hukumomin gwamnatoci da masu zaman kansu a faɗin duniya suka fara gudanar da bincike na gano wuraren da cutar ta fi ƙamari, da ilmantar da al’umma kan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar, tare da samar da sinadaran tacewa da magungunan kashe ƙwari don inganta ruwan sha. Hukumar lafiya ta duniya da ƙasashen da cutar ta kurkunu ta shafa sun ƙuduri aniyar kawar da ita nan da shekara ta 2030.

Abu ɗaya da kan kawo cikas game da cutar shi ne kamuwa da wasu dabbobin da ke dawwamar da rayuwar tsutsa a wuraren da ruwan sha yake. Kurkunu tana shafar karnuka, alal misali, kamar mutane, karnuka sukan shigar da cutar ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwa, tsutsar takan girma har ta yaɗu su zama tsutsotsi manya a jikin karnuka, sannan daga karshe, ta bazu cikin fata don sakin sabbin ƙwayaye a cikin ruwa, inda za su ci gaba da yaɗuwa zuwa mutane.

Cutar kurkunu cuta ce da ke da alaƙa d talauci. Tana shafar marasa galihun da ba su da tsaftataccen ruwan sha da isasshiyar kulawar lafiya, da rashin daidaito da kuma illar da ke tattare da rayuwa, tana hana mutane yin aiki ko zuwa makaranta, haka zalika, tana ci gaba da dawwama a cikin matalauta.

Manazarta

Ayawa, L. (2018, January 20). Ana Daf Da Kawo Karshen Cutar Kurkunu A Africa. VOA Hausa News.

Hökelek, M., MD PhD. (n.d.). Nematode infections: background, pathophysiology, epidemiology. Medscape

World Health Organization: WHO. (2025, January 30). Dracunculiasis (Guinea-worm disease). WHO

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×