Kwarkwata ƙananan ƙwari ce masu rarrafe da ke rayuwa a cikin gashin kai. Alamar da aka fi sanin da akwai kwarkwata ita ita ce jin ƙaiƙayi, musamman a bayan kai da wuya da kusa da kunnuwa. Akwai sinadarin shamfu na musamman na magunguna waɗanda ke ɗauke da wani abu mai suna pyrethrins da aka sarrafa don kashe kwarkwata. Kwarkwata tana shan jini ta hanyar tsotsa daga fatar kai kuma ta sanya ƙwai wanda ake kira (nits) waɗanda ke mannewa da gashin da ya bayyana a saman fata.

Yawancin kwarkwata ba su da lahani ga lafiya gabaɗaya, amma suna cizo, wanda zai iya zama damuwa. Nau’o’in kwarkwata daban-daban ne kuma suna da fasali daban-daban, amma duk suna iya yin cizo mai ƙaiƙayi. Kwarkwata ƙanana ce, ƙwari ne masu launin toka suna da kusan tsayin milli-mita 2-3. Suna rayuwa ne a kan fatar kai, inda suke shan jinin ɗan’adam, kuma suna yin ƙwai a gindin kofar gashi.
Nau’ikan kwarkwata
Akwai nau’ika kwarkwata guda uku:
• Kwarkwatar kai
Wannan nau’i na kwarkwata suna zama ne jikin fatar kai. Sun fi sauƙi gani a gefen wuya da kuma kan kunnuwa.
• Kwarƙwatar jiki
Waɗannan su ne masu yin rayuwa a jikin tufafi da kayan kwanciya, kuma suna hawa kan fata domin zuƙar jini. Kwarkwatar jiki ta fi shafar mutanen da ba sa yin wanka ko wanke tufafi akai-akai.
• Kwarkwatar mara
Su ne waɗanda ke rayuwa a cikin gashin mara. Ana iya samun su a kan gashin jiki mara nauyi, kamar gashin kirji, gira ko gashin ido, amma ba a cika samun hakan ba.
Waɗanda kwarkwata ke shafa
Kwarkwata na iya shafar kowa amma takan faru a tsakanin yara masu shekaru 3 zuwa 11, tare da danginsu. Yara sun fi fuskantar haɗari, yayin da suke cakuɗuwa ta kai-da-kai da sauran yara a lokutan yin wasa tare kuma suna iya yin amfani da abubuwan da ke da alaƙa da gashin kawunansu.
Yaɗuwar kwarkwata
Kwarkwata dai ta zama ruwan dare, tana shafar mutane miliyan 6 zuwa miliyan 12 a kowace shekara. Ta fi zama ruwan dare a tsakanin yaran da suke zuwa makaranta waɗanda suka fi samun kusanci da juna ko raba kayan tsefe-tsafe, goge-goge, huluna da sauran abubuwan da suke taɓa gashi.

Alamomin kwarkwata a kai
Alamar da aka fi sanin cewa da kwarkwata ita ce ƙaiƙayi, musamman a bayan kai da wuya da kuma kusa da kunnuwa, wuraren da kwarkwatar ta fi zama. Alamomin samuwar kwarkwata a ka sun hada da:
- Jin kamar wani abu a cikin gashi yana motsawa
- Cizo da ƙaiƙayi
- Wahalar barci
Yadda kwarkwata ke yaɗuwa
Kwarkwata na yaɗuwa a tsakanin mutane ta hanyar da ƙwarin ke rarrafe daga mutum zuwa mutum a yayin haɗuwa ta kai tsaye ko ta hanyar amfani da abubuwan gyaran gashi da tsifa da huluna da ɗan-kwali, tare da mutumin da ke da kwarkwata a kai. Rashin tsafta bai cika haifar da kwarkwata. Kwarkwata ta fi addaba da daddare, wanda za ta iya hana barci. Yawan ƙaiƙayi na iya zama matsala ga fata, wanda zai iya haifar da kamuwa da cuta
Kwarkwata ba za ta iya tashi ko tsalle ba domin ba ta da fiffike, don haka tana yaɗuwa ta hanyar rarrafe daga mutum zuwa mutum yayin da suka kusanci juna. Haka nan kwarkwata na iya yaɗuwa ta cikin abubuwan kamar tawul, zanen gado da sauran su. Dabbobin gida ba sa kamuwa ko yaɗa kwarkwata ga mutane.
Hanyoyin gano kwarkwata
Hanya ta farko da ake bi don gano kwarkwata ita ce dubawa a gani. Idan aka duba gashin kai da kyau a jikin fatar kai, za a iya ganin ƙananan abubuwa farare da ke manne da ƙofofin gashi, su ne ƙwayayen kwarkwata. Yawanci suna yin kama da alamomin amosani amma ba sa iya karyawa ko girgiza gashin. Kwarkwata na iya motsawa da sauri kuma suna da wahalar gani.
Magance kwarkwata
Magungunan kwarkwata sun haɗa da yin amfani da magunguna na mai ko shamfu ko man shafawa waɗanda ke kashe kwarkwata. Mayukan shamfu masu magani a cikin sun ƙunshi wani sinadarin magani da ake kira pyrethrin ko permethrin wanda ke kashe kwarkwata da ƙwayayenta.
Magungunan kwarkwata suna da tasiri kuma suna yin aiki, sai dai hakan na tabbata ne kawai idan an bi umarnin yadda ake amfani da maganin, tsawon lokacin da ya kamata a bar shi a cikin gashi da kuma sau nawa ya kamata a rika maimaita maganin.
Kwarkwata da ƙwayayenta suna manne a sassan gashi kuma suna iya ba da wahalar cirewa, a wasu lokutan sai an tsefe kai an taje shi da kyau matuƙa sannan a samu ɗan sassaucin azabar su. Bayan amfani da tsife ko kashe su da hannu, akan wanke kai bayan an tsefe da ruwan ɗumi na tsawon mintuna goma.
Yadda za a kawar da kwarkwata
Domin yin amfani da mayukan shamfu da magungunan sabulu wajen magance kwarkwata, a bi waɗannan matakan:
- A tabbatar an karanta bayanin yadda ake amfani da maganin, wanda kan zo a cikin kwalin maganin.
- A yi amfani da maganin ta hanyar shafa shi a dukkan gashin kai ta yadda zai isa ga fatar kai. Kada a shafa maganin ga wani gashin daban a jiki.
- A bi dukkan ƙa’idojin maganin na tsawon lokacin da ya kamata a bar maganin a cikin gashi kafin a wanke shi.
- Bayan an wanke maganin daga gashi, sai a yi amfani da mataji mai tsini don cire matattun kwarkwata da ƙwayayenta.
- A ci gaba da amfani da maganin kamar yadda aka tsara bisa umarni da ƙa’idar maganin wanda likita ke sanarwa.
Tsawon lokacin yin magani
Akan ɗauki dogon lokaci ana amfani da magungunan don kashe kwarkwata da ƙwayayenta daga gashi gabaɗaya. Yakan iya ɗaukar har zuwa makonni uku don rabuwa da ita kwata-kwata.
A kuma tabbatar cewa duk mutanen da ke rayuwa a gida sun bincika kansu kuma sun yi maganin, idan wani daga cikin mutanen gidan yana da kwarkwata, to da idan kowa bai sake ɗauka ba. Don haka a tabbatar kowa ya yi maganinta.
Riga-kafin kamuwa da kwarkwata
- Hanya mafi kyau ta riga-kafin kamuwa da kwarkwata ita ce kada a yi amfani da mataji ɗaya ko tawul ko hula tare da wasu mutanen, kuma a ƙaurace wa yin cuɗanya tare da wanda ke da kwarkwata.
- A guji haɗa kai-da-kai lokacin wasanni
- Kada a yi amfani da huluna ko abubuwan da ake sawa a kai tare da wasu.
Kwarkwata ba ta yaɗa cuta
Kwarkwata ba za ta iya yaɗa cuta ba ta kai tsaye, amma suna iya sa fatar kai ƙaiƙayi. Yawan ƙaiƙayi na iya haifar da matsala ga fatar, wanda hakan kuma zai iya haifar da cututtuka. Idan ana fama da kwarkwata, kuma an yi magani ba a iya magance ta ba. To sai a tuntuɓi likita domin ba da ƙarin magunguna ko don kiyaye lafiyar lalata fata.
Idan dukkan magungunan da aka yi a gida sun gaza aiki ko kuma idan akwai alamomin kamuwa da cuta, to lallai a garzaya ga asibiti. Alamomin kamuwa da cuta sun hada da:
- Zazzaɓi
- Ciwon da ba zai warke a kai ba
- Jin zafi a kai
- Launin ja ko kumburi a fatar kai
Manazarta
Head lice. (2024, May 1). Cleveland Clinic.
Lillis, C. (2024, February 26). How to identify lice bites. Medical News Today
Clay, T. (1999, July 26). Louse | Description, features, life cycle, species, & Classification. Encyclopedia Britannica.
CDC (n.d.) – DPDX – Pediculosis. CDC