Skip to content

Maganin gargajiya

Yana da matuƙar wuya a ce ga lokacin ɗana’adam ya fara amfani da magani domin warkar da cututtuka. Wannan dalili ne ya sa da wuya ace ga yadda maggagni ya samo asali, amma duk da haka nan masana aladu da ilmin magani su kawo wasu bayanai wadanda suke ganin daga nan ne magani ya samo asali. Da farko za a farad a asalin ita kanta Kalmar magani.

images 2021 02 03T203101.5560
Magungunan gargajiya magunguna ne da suka wanzu tun tali-tali.

Asalin kalmar magani

Adamu, (1985) ya ce kalmar “magani” kamar yadda bincike ya bayyana, ba kalma ce mai cin gashin kanta ba, ta samo asali ne a sakamakon irin furucin da Hausawa suke yi a lokacin da suke kokarin kawar da wata cuta wadda basu bukata. A wannan hasashe an bayyana cewa, Kalmar Magani ta samo asali ne a sakamakon hada Kalmar “Ma” da “yi” da “Ma” da kuma Kalmar “gani”.

Ma’anar magani

Magani na daukar matsayin duk wani abu da ɗan’adam kan yi don samun warkarwa da kariya da buƙata da ɗaukaka a rayuwarsa ta yau da kullum. Don kuwa ɓangaren rayuwar ɗan’adam duk tafiya take wajen fafatikar neman maganin warkewa daga cutuka da kwantar da damuwar zuciya in ya samu sai kuma ya shiga neman maganin ɗaukaka da kariya daga abokan hamayya. Haka kuma rayuwar ɗan’adam take tafiya kullum. In ya yi maganin wannan yana buƙatar maganin wancan.

An bayyana cewa, a lokacin da Bahaushe ya kamu da wata cuta wadda bai bukata, a kokarinsa na maganinta, say a debo sake-sake da ganyaye da sauyoyin itaciwa da hakukuwa da saurar abubuwa da ban da ban, wan da wasu zairinga jikawa yana sha ko ya shafa ko ya ringayin wanka da su domin kokarin ganin sun taimaka ya samu sauki ko ya warke daga wannan cuta da takama shin a fadar Hausawa alokacin da yake wannan kokarine sai yace mu hada wannan mu gani, sannu a hankali sai a ka gajarta wannan jumla ta koma, mai magani harde ta koma kalmomi biyu, magani, wanda daga baya aka hade su ta koma, magani, wanda a yau take nufin hanyar warkar da dukkan wata cuta ta fili ko ta buye da kuma nuna buya da bajinta ta hanyaryin tsatsube-tsatsube da surkulle da safe-safe da sihirce-sihirce.

Dabarar yin magani

Idan kuma muka koma asalin hanyar dad a dan Adam ya samo dabarar yin magani dun warkar da cuta da kuma kare kansa daga kamuwa daga wasu cututtuka, shima akwai bayanai da harsashe da ban da ban wadanda manazarta da masana aladu da ilimin magani suka kawo.

Hanya ta farko wanda aka bayyana a matsayin wanda dan Adam ya sami wannan hikma, itace ta jarraba abubuwa da Allah Madaukaki ya yalwata a kusa da shi. An karat a bayyana cewa, a kwai abubuwa da dama wadanda suka hada da itatuwa da tsirrai da sinadarai a ko’ina kuma ayalwace cikin wannan Duniya tamu, wadanda ta hanyar gwadasu ne alokacin da aka fuskanci wata matsala ta rashin lafiya dan Adam ya sami hanyar warkar da cututtuka iri daban daban wanda suke damun sa. Masu irin wannan ra’ayi na ganin ta wannan hanya ce magani ya samon asali harya kai matsayin da yake a yau, (Musa 1986).

14eb041ce523b9d0add7ccad405fba3a 2
Akwai ɗimbin nau’ikan magungunan gargajiya.

Hasashi na biyu ya bayyana cewa, magani ya samo asali daga tsuntsaye da dabbobi da kwari na gida da na daji. A wannan ra’ayi anaganin magani ya samo asali ne a sakamakon ire-iren hakukuwa da tsirrai wadanda tsutsaye da dabbobi suke ci. Wai alokacin da wadannan halittu suke lafiya a kwai nau’o’in abincin da suke ci, haka kuma alokacin dab a su da lafiya a kwai ire-iren hakukuwa da itatuwan da suke ci. Wadanda suka kawo wannan ra’ayi sun bayyana cewa, ta wannan hanyace dan Adam ya gano ire-iren hakukuwa da tsirrai wadanda idan akayi amfani da su za’a sami waraka da wasu cituttuka (Musa 1985).

Wani hasashe kuma na bayyana cewa, magani idan ya samo asali ne a sakamakon baiwa da Allah madaukaki ya ba wasu mutane akan sanin magungunan cututtuka iri daban daban. Masu irin wannan ra’ayi na bayyana cewa, ire-iren wadannan mutane ne kan sami irin wannan baiwa ce a lokacin da wani ciwo ya kamasu. A irin wannan lokaci ne Allah madauki, cikin ikon sa yake sanar da su ire-iren hakukuwa da tsirrai da suka dace suyi amfani da su da kuma yadda zasuyi amfani da su domin samun waraka daga wannan cuta (Musa 1986).

Idan muka nazarci wadannan hasashe na asalin magani, a’iya cewa ra’ayi na uku yafi daukar hankali, don kuwa tun farko an bayyana cewa, Allah shi Ya halicci mutum, Ya kuma halicci magani da cuta, sannan kuma ya sanar da mutum magungunan cututtuka iri daban-daban amma waraka a hannunSa take.

Ire-iren magungunan gargajiya

Waɗannan magunguna na gargajiya an kasa su zuwa gida huɗu kamar haka:

  • Magungunan warkarwa
  • Magungunan kariyar kai
  • Magungunan cutarwa
  • Magungunan biyan buƙatun rayuwa

Magungunan waraka daga cuta

Magungunan neman waraka su ne magungunan da masassaƙa kan bayar domin kawar da wata cuta da ke addabar wani a cikin al’umma. Cutukan jiki suna da yawa akwai waɗanda ido ke iya gani, a taɓa a ji su, a kuma ga alamominsu. Kamar irin su ƙurji da gwaiwa da maƙoƙo da ɗankankare da ciwon daji da sauransu.

Maganin firgitar yara

Wannan yana nufin firgece-firgice ko zabure-zaburen da yara kan yi idan zazzaɓin masassara ya yi musu yawa a jiki. A nan masassaƙa kan samo “godar zomo” (wani haki ne) sai a haɗa shi da itacen tsiriri a dafa a rinƙa ba yara masu wannan lalurar, cikin ikon Allah za a samu waraka.

Maganin maƙero

Idan an samu mai wannan lalurar maƙero, masassaƙa kan samo ɓawon ƙirya a ƙona shi a haɗa da man kaɗe ko man shanu a rinƙa shafawa inda cutar take a jikin mutum.

Maganin basir

Idan aka samu mai irin wannan lalurar, masassaƙa kan samo sassaƙen itacen maɗaci a dafa ko a daka ana kunu da shi ana ba mai lalurar yana
sha, da izinin Allah ana samun waraka daga cutar basir.

Maganin baska

Idan aka samu mai wannan lalurar, masassaƙa kan samo itacen baushe da ƙirya a haɗa wuri ɗaya a ginɗa, a rinƙa ba mai wannan lalurar yana sha kuma yana wanka da ruwan.

Maganin shawara

A nan ma idan aka samu mai wannan cutar, masassaƙa kan samo itacen lado da hano a yi tsimi da su ko a shanya idan sun bushe sai a daka garinsu a rinƙa sanyawa a kunu ko fura ana ba mai lalurar ciwon shawara. Cikin ikon Allah zai samu waraka.

Maganin ciwon ciki da zafin jiki da ciwon jiki

Cutar ciwon ciki wata lalura ce da ke addabar ɗan’adam musamman al’ummar Hausawa daga lokaci zuwa lokaci. Idan wannan lalurar ta addabi mutum, masassaƙa sukan bayar da wasu magunguna domin kawar da cutar ko rage mata raɗaɗi. Daga cikin nau’ukan magungunan da suke samarwa sun haɗa da wanda sukan ce nemo sassaƙen itacen giyayya da sassaƙen rawaya.

Maganin ƙaba/gwaiwar ciki

A mafi yawan lokuta ana samun ɗaiɗaikun mutane masu fama da wannan lalurar a cikin al’ummar Hausawa, idan haka ta kasance masassaƙa sukan bayar da taimakon maganinsa a tsakanin al’umma. Akan nemo ganyen itacen kaɗe da ɗoruwa da jan-yaro, sai a haɗa su wuri ɗaya a dafa har sai sun dafu sosai a rinƙa yin kunu da ruwan maganin ana bai wa mai lalurar yana sha.

Maganin ciwon daji

Ciwon daji ko sankara yana da nau’uka daban-daban da ke addabar al’umma musamman a ƙasar Hausa. A wannan fuskar ma, masassaƙa a ƙasar Hausa sun bayar da gagarumar gudummawarsu wurin kawar ko rage raɗaɗin wannan cutar a tsakanin al’umma. Daga cikin nau’ukan magungunan da sukan bayar sun haɗa da na samo sassaƙen itacen kurya a shanya, bayan ya bushe sai a daka sassaƙen a tankaɗe a rinƙa sanya garin maganin ana sha a cikin kunu, sannan a kwaɓa sashen maganin da ruwa ana shafawa inda lalurar take.

Maganin miyagun mafarkai

Wani lokaci za a tarar idan mutum yana barci sai ya rinƙa yin wasu miyagun mafarkai masu ban tsoro da firgitarwa. Idan aka samu mai irin wannan lalurar masassaƙa sukan bayar da taimako da ya jiɓanci wannan lalurar domin kawar da cutar ko kwantar da ita. Sukan ce a samo ganyen gwandar daji ƙunshi uku a dafa shi a sanya jar kanwa kaɗan sai a riƙa yin kunu da shi ana sha da safe har tsawon kwanaki uku. Masassaƙa sun nuna cewa, idan aka yi wannan, da ikon Allah mai lalurar zai samu waraka.

Magungunan biyan buƙatun rayuwa

Buƙata ba wata cuta ce ta zahiri da ke kama ɗan’adam ba, sai dai yana da wasu ƙudurce-ƙudurce da buƙata da yake ganin idan bai fake ga magani ba, da wuya ya same su. Masassaƙa kamar sauran al’umma, zuciyoyinsu damfare suke da guri daban-daban na rayuwa. Waɗannan gurace-gurace suna iya kasancewa masu kyau ko akasin haka, don haka, rayuwar al’umma cike take da buƙatoci mabanbanta. Daga cikin buƙatocin zuciya akwai na samun dukiya ko haihuwa ko mulki ko soyayya ko aure ko kariyar kai da dai makamantansu. A wannan turba, masassaƙa a ƙasar Hausa sun taimaka wajen samar da nau’ukan waɗannan magunguna daga cikinsu kuwa akwai:

Maganin neman aure

Ganin cewa aure wani abu ne mai muhimmanci ga rayuwar Hausawa, wannan ya sa kusan kowane Bahaushe yana tinƙaho da aure a matsayin wani tubali na wayantar al’umma. Duba daga wannan manufa ya sa Bahaushe yake iyakar yinsa domin ganin ya yi aure. A ƙoƙarin cimma wannan buƙata na aure, wani lokaci akan ci karo da wasu matsaloli na rashin karkatar ra’ayin wadda ake so a aura zuwa ga maneminta musamman idan akwai wani abokin hamayya. Masassaƙa a wannan bigiren sun tanadi nau’ukan magunguna daban-daban domin cimma burin zuciyar mai neman auren.

Maganin inganta soyayya

Kafin a yi aure ana buƙatar giniwar soyayya a tsakanin saurayi da budurwa, domin wannan soyayya ita ce tubalin ginuwar aure. Wani lokaci ana samun rashin soyayya a tsakanin saurayi da budurwa. A ƙoƙarin inganta wannan soyayya, masassaƙa a ƙasar Hausa sun tanadi wasu magunguna na musamman da suke bayarwa ta wannan fuskar. Daga cikin magungunan da suke bayarwa sukan buƙaci a nemi waɗansu ‘yan ƙolallai da ke liƙe ga itacen farin ɓaure, su waɗannan yan ƙolallai za a ɓallo bakwai (7). Bayan an ɓallo su, a lokacin da za a je wurin budurwa sai a sanya ƙololan cikin baki ana taunawa, idan saurayi ya isa wurin budurwar sai ya kira sunanta, idan ta amsa sai ya haɗiye yawun maganin da ke cikin bakinsa na waɗannan ƙolallai da yake taunawa. A haka zai yi ta ƙoƙarin haɗiye yawun bakinsa da maganin a ciki idan ya ji magana mai daɗi. Idan kuwa a cikin hirarsu ta yi masa magana marar daɗi sai ya zubar da yawun maganin da ke cikin bakinsa kada ya haɗiye.

Maganin neman haihuwa

Samun haihuwa yana daga cikin mihimman dalilin yin aure a cikin kowace al’umma. Wani lokaci Allah cikin ikonSa Yana jarabtar wasu ma’aurata da rashin samun haihuwa. Idan aka samu ma’urata da ke fama da wannan lalurar, a ƙoƙarin biya musu buƙata masassaƙa sukan bayar da wasu magunguna domin samun haihuwa. Sukan ce a tashi tun da safe a je gindin itacen kuka a ce: ‘Na zo neman biyan buƙata, ku taimake ni ga zakkar ku nan”, sai a ajiye fararen goro guda tara (9) jayayen goro su ma guda tara (9) cikin sabuwar ƙwarya. Daga nan sai a sassaƙo itacen ta gabas da yamma da kudu da arewa a bai wa mai buƙata ta dafa shi sosai a riƙa yin kunu da ruwan maganin ana sha.

Magungunan kariyar kai

Hausawa na cewa “Riga-kafi ya fi magani”. Duba da wannan karin magana na Hausawa, wannan yana nuna akwai buƙatar yin riga-kafin wasu cututtuka tun kafin su addabi mutum, kuma yin wannan yana
taimakawa wajen inganta sha’anin kiwon lafiya a cikin al’umma. Don haka al’ummar Hausawa sun tanadi wasu magunguna domin kariyar kai daga abubuwa wasu cututtuka da kan iya addabar al’umma. Su waɗannan magunguna ana bayar da su ne kafin aukuwar wata cuta a cikin al’umma.

Maganin kariyar kai da iskoki

Ganin cewa sana’ar sassaƙa sana’a ce da ta jiɓanci shiga daji domin saro itacen da za a yi amfani da su a lokacin aiwatar da sana’ar ta sassaƙe-sassaƙen abubuwa masu yawa na amfanin al’umma. A wani lokaci masassaƙan kan ci karo da itatuwa masu iskoki waɗanda kan iya cutar da su. Sanin wannan ya sa masassaƙa suka tanadi wasu magunguna na musamman domin kariyar kansu daga cutarwar waɗannan iskoki.

Maganin kariyar gamo da iskoki

Kamar yadda Allah Ya halicci mutane, haka ma Ya halicci Iskoki a cikin duniya. Bahaushe ya yi imanin cewa, su waɗannan Iskoki ba a ganinsu, kuma galibi suna cutarwa ga ɗan’adam. Shi kuwa ɗan’adam a ƙoƙarin fafatukar neman abinci da biyan wasu buƙatocin rayuwa na yau da kullum yana iya gamo da waɗannan Iskoki da za su iya cutar da shi. Domin kaucewa cutarwasu idan suka haɗu, sai masassaƙa suka tanadi wasu magunguna na musamman.

Magungunan Gargajiya0
Magungunan gargajiya suna samar da waraka daga cututtuka daban-daban.

Maganin kariyar kai daga jifa

Masassaƙa kamar sauran al’ummomi, mutane ne da ke cuɗanya da al’ummomi daban-daban ta fuskar sana’arsu. Wannan cuɗanya kuwa a
tsakanin al’umma tana iya haifar da zamantakewa mai armashi ko akasin haka. Idan kuwa aka yi rashin sa’a zamantakewar ta yi ƙamari, wadda kan iya haddasa gaba da ƙiyayya da hamayya a tsakanin junansu ko wasu ɗaiɗaikun jama’a.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page