Skip to content

Mutuwa

Kalmar mutuwa baƙuwar kalma ce da aka aro daga harshen Larabci watau “Al Maut.” A harshen Larabci tana nufin ƙarewar rayuwa ko amfanin wani abu. A harshen Hausa kuwa, kalmar tana nufin rasuwa ko ƙarshen ran mutum ko dabba ko duk wani abu mai rai.

Ma’anar mutuwa

Mutuwa ita ce dakatarwar dindindin na duk ayyukan halittu waɗanda ke ɗorewa, hakan na nuna ƙarshen rayuwar mutum ko dabba ko duk wani abu mai rai. Mutuwa wani yanki ne na dabi’a na tsarin rayuwa.

A wata mahangar an bayyana mutawa da, ”Rasa rayuwa ko barin aiki ga abu mai rai ko marar rai, mutum ko dabba ko tsiro ko wata halitta ko kuma wani abu mai amfani ta yadda ake ganin alamun ba zai taɓa dawowa yadda yake a da ba kafin ƙaddarar rasa rayuwar ta auka masa.”

For representation only HT File Photo 1680287238258
Kwararrun likitoci kan tabbatar da mutuwar mutum bayan sun yi gwaje-gwaje da na’ura.

 

Mutuwa ita ce ƙarewar abu mai rayuwa ko lalacewar abu marar rayuwa, ya zama ba za a iya sake wani amfani da shi ba kamar yadda aka saba a da face sai an gyara abin nan, misali mota da sauran injiman na’ura.

Ire-iren sunayen mutuwa

Dangane da sunayen mutuwa na asali a cikin harshen Hausa, kamar rasuwa, raguwa, fakuwa, ƙaura, kasawa, wucewa, shukuwa, rigaya, ya kau, ƙarewa, dogon kwana/barci da sauransu sai a duba wannan shafin da aka ambata.

Akan yi amfani da kalmomi da dama waɗanda kan maye gurbin sunan mutuwa. Kuma dukkan kalmomin sukan jiɓinci rasa rayuwar mutane ne ko dabba.Kaɗan daga cikin kalmomin da suke wakiltar sunan mutuwa ga Hausawa sun haɗa da:

  • Rasuwa
  • Raguwa
  • Fakuwa
  • Ƙaura
  • Kasawa
  • Tafiya
  • Dogon Barci/kwana
  • Wucewa
  • Shukuwa
  • Rigaya
  • Ya kau
  • Ƙarewa
  • Shurewa
  • Rai ya yi halinsa
  • Babu shi
  • Kwanta dama
  • Wafati
  • Halaka
  • Ya sa kai
  • Ya shuri bokiti

Alamomin fitar rai

Akwai fitattun alamomin da ake aminta da cewa idan sun bayyana ga mutumin da yake fama da jinyar rashin lafiya,to ana kyautata mai zaton zama kusa da barin duniya. Waɗannan alamomin kuwa sun haɗa da:

  • Tsananin sanyin jiki ko zafin jiki
  • Farin ido ko rashin ƙiftawarsu
  • Buɗewar baki
  • Rufewar idanu
  • Karyewar harshe na rashin iya magana mai ma’ana
  • Shaƙuwa
  • Yi wa ‘ya’ya da dangi wata muhimmiyar magana (wasiyya)
  • Sandarewar jiki ko gaɓa.

Tabbatar da faruwar mutuwa

Akwai hanyoyi da hikimar tantance faruwar mutuwa gabanin su yanke hukunci an mutu ko bayar da sanarwar mutuwa tun zamani mai tsawo. Hikimar hakan shi ne domin a kaucewa binne mutum da sauran rayuwarsa domin akwai abin da ake kira doguwar suma, inda mutum ya suma kamar ya mutu ne daga baya a ga yana numfashi. Dangane da haka, daga cikin dabarun gane rai ya yi halinsa an mutu sun haɗa da:

  • Fesa ruwa a jikin maras lafiya, yin hakan zai sanya idan yana da sauran rayuwa a gay a motsa,
  • Motsa babbar yatsar ƙafarsa
    Bugun hannu a ƙasa kusa ga kansa, a nan za a bugi hannu aƙalla sau uku.
  • Za a kira sunansa a gani ko za ya motsa.
  • Akan zuba yashi a ƙirjinsa a gani ko zai motsa.
  • Tabbatarwar masana: Ƙwararrun likitoci suna bayyana ƙarshen rayuwar mutum bayan sun yi bincike da gwaje-gwajen ilimi.

Idan duk an yi waɗannan dabarun aka ga bai motsa ba to daga nan za a yanke hukuncin ransa ya fita sai a dangana. Daga nan sai faɗar mutuwa ga dangi da abokan arziki.

Dalilin mutuwa

Dalilai da dama kan iya haifar da mutuwa ga abu mai rai, ko dai dalilin afukuwar haɗari ko kuma wani rauni ko ciwo ko wata lalura bayyananiya ko kuma ɓoyyayiya ko kuma mutuwa haka kawai ta kai tsaye wanda kan iya faruwa da komai.

Mutuwa ta kai tsaye

Mutuwa ta kai tsaye ita ce mutuwar da abu zai iya yi ba tare da wani dalili ba, idan mutum ne lafiyarsa ƙalau sai a wayi gari ya mutu, haka ma idan dabba ce. Idan kuma abin amfani ne ana iya wayar gari ya daina aiki kwata-kwata wanda babu wani busababbi na faruwar hakan.

Mutuwa yayin ciwo

Ita ce mutuwar da ka iya faruwa yayin lalura ko kuma ciwo ko kuma wani haɗari. Misali,

Barkewar annobar: Sanadiyyar barkewar cututtuka ko annoba na haifar da mace-mace, misali Corona ta yi sanadin mutuwar mutane da dama. Haka nan mutane da yawa kan iya rasuwa a dalilin annobawar kwalara wato amai da gudawa.

Tsufa

Shekaru na tsufa na nufin yanayi lokacin da mutum zai iya tsira daga dukkan masifu, amma daga ƙarshe ya mutu saboda abubuwan da suka shafi tsufa. Ƙwayoyin dabbobi da na tsirai suna haihuwa kuma suna aiki a duk tsawon lokacin kasancewar yanayin, amma tsarin tsufa yana sa su daina aiki.

Misali, a ƙasar Burtaniya, kashi tara cikin goma na yawan mace-macen da ake samu a kowace rana ya danganta da tsufa, yayin da a faɗin duniya yake ɗauke da kashi biyu bisa uku na mutuwar mutane 150,000 da ke faruwa a kullum (Hayflick & Moody, 2003) .

Mafi yawan dabbobin da suka tsira daga haɗarin waje don gudanar da rayuwarsu suna mutuwa saboda tsufa, wanda aka sani da ilimin rayuwa kamar “tsufa”.

Bishiya idan ta tsufa ta kan daina bayar da yabanya mai kyau da armashi, ko kuma ‘ya’yanta su daina zaƙi idan mai ‘ya’ya ce, idan kuma ba ta ‘ya’ya yanayin itacenta kansa yana sauyawa ya bushe ko kuma ya yi wani irin baƙi-baƙi daga cikin alamun tsufa a tare da bishiya akwai soma fitar da ƙaro, wani abu mai danko ko fari ko baƙi. Duk wannan misali ne na yadda wasu dalilai ko sababbai na mutuwa.

Haɗari

Haɗari iftila’i ne da kan faru wanda kan iya sanadiyar mutuwar mutane har lahira, wannan hadari kan haɗa da haɗarin abin hawa,ko gobara ko ruftawar gini.

Kisan kai

Kisan kai hanya ce ta rasa rayuwa, mutum kan iya kashe kansa da kansa sakamakon wasu dalilai misali kuncin rayuwa kan sa wasu su rataye kansu, wasu kuma dalilin soyayya sukan hallaka kansu. Baya ga haka wani mutumin kan kashe wani bisa dalilai da suka haɗa da kiyayya ko zama gaba ko takaddama a kan wani abu.

Abin da mutuwa take haifarwa

A zamantakewar mutane, yanayin mutuwa da sanin mutane cewa za su mutu ya ɗaɗe a matsayin abin damuwa a al’umma a addinance da gargajiyance. Wannan ya haɗa da imani a kan cewa za a tashi bayan mutuwa ko kuma ba za a tashi ba.

Jana’iza

Abin da ake yi bayan mamaci ya rasu ya haɗa da jana’iza da kuma tunawa da mamacin. Ana sanya gawar mamaci a cikin makara ko akwatin gawa sai a kai shi a binne a maƙabarta ya danganta ne da al’ada. A turance ana yi masa addu’a da Rest in Peace” wato ka huta cikin aminci, a Hausance, ana cewa Allah Ya jiƙan mamaci. Daga nan akan iya samun ‘yan koke-koke ga makusantan mamacin da kuma wasu daga cikin maƙota.

Zaman makoki

Abu ne da ake yin sa yayin da aka yi mutuwa, zama ne na karbar gaisuwa da taya waɗanda suka yi rashin jimami. Ba a taɓa yin zaman makoki idan ba mutuwa aka yi ba don haka mutuwa na ɗaya daga cikin dalilan haifar da shi.

Ƙara imani

Ta fuskar ɗan’adamtaka mutuwa na ƙarawa ɗan’adam imani, ka ga wanda kake tare da shi yau da kai aka yi masa wanka, aka haɗa shi aka kuma dauke ke shi zuwa maƙabarta, wannan abin kan haifar da tsoro da kuma rauni sosai a zuciyar ɗan’adam.

Al’adun mutuwa kafin Musulunci

Waɗannan wasu fitattun al’adu ne da Hausawa kan yi game da sha’anin mutuwa tun kafin zuwan musulunci a ƙasar Hausa. Waɗannan al’adun kuwa sun haɗa da:

  • Amfani da ƙwarya wajen wanka tare da kife su da zarar an gama. Ba za buɗe ba sai ranar uku ga mutuwar.
  • A cika ƙwaryar da hatsi da kayan mamaci na sawa a ba wa mai wankan gawa, sai kuma a ba wa matar mamaci sanda ta riƙa yawo da ita wai ko da zai dawo mata ta doke shi.
  • Zubar da ruwan randa zarar an yi mutuwa tare da kife randunan da zummar cewa wai ba za a yi amfani da ruwan ba, tun da ba a san da wacce mutuwa ta wanke wuƙarta da shi ba. In ma da rijiya a gidan akan yi ƙoƙarin kwarfe ruwan mai tarin
    yawa a zubar, don cewar watakila da wannan ruwan mutuwar ta wanke wuƙar.
  • Sanya wa yara toka a zagaye musu ido, idan ba a sami toka ba sai a zagaya musu bakin tukunya wai don kar su yi mafarki da wannan mamacin.
  • Sanya ko ɗora faifai ko dutse ko kuma takobi a kan cikin mamacin da daddare, da zimmar cewa wannan shi zai hana cikin ya kumbura kafin wayewar gari.
  • Hausawa sukan binne mamaci da tun a ranar da ya mutu, sai fa idan tsakiyar dare ne akan bari sai da safe a bizne gawar. Kodayake akwai ra’ayin cewa wasu maguzawan Hausawa sukan bar gawa har bayan kwana uku.
  • Akasarin Hausawa sukan binne gawa ne tun ranar da aka yi rasuwa, wannan al’adar kuwa ana gudanar da ita ne tun gabanin bayyanar musulunci ga Hausawa.
  • Yanayin haƙar ramin da za a binne gawa kuwa akwance ne akan sanya gawar. Kuma akan sanya mutum da kayan aikinsa kamar warki ko makamantansa a cikin ƙabari, idan kuma mace ce akan sanya ta da kayan aikin gida da ta saba amfani da su.
  • Ƙananan yara kuwa sai a shafa masu shuni a fuska wai idan sun je su ba mutuwa tsoro kada ta sake dawowa ta ɗauki wani.

Bayan zuwan musulunci sai abin ya sauya, inda kafin a binne mamaci sai an yi masa wanka an sanya masa turare da kuma sutura. A yi masa sallah sannan a kai shi ƙabarinsa.

Manazarta

Abdullahi I.S.S “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa. Kundin Digiri na uku UDUS, 2008

Erhardt, C. L. (1958). WHAT IS “THE CAUSE OF DEATH”? Journal of the American Medical Association, 168(2), 161.

Metcalf, Peter; Huntington, Richard (1991). Celebrations of Death: The Anthropology of Mortuary Ritual. New York: Cambridge Press

Nuwer, R. (2023, November 17). The Biggest Questions: What is death? MIT Technology Review.

 

Tarihin Wallafa Maƙalar

An sabunta 30 December, 2025

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×