Masana da ƙwararru a harkar lafiya da ta shafi mata masu juna biyu da al’aura sun bayyana ma’anar naƙuda a matsayin wani ciwon mara da ke tasowa a hankali ga mata masu ciki wanda zai iya sanadiyyar haihuwar ciki da duk abin da ke cikin mahaifa ta hanyar farji bayan cikin ya shafe wa’adin da zai iya rayuwa a wajen mahaifa.

Matakan naƙuda
An kasa naƙuda zuwa mataki uku kamar haka:
- Matakin farko: Wannan shi ne a lokacin da bakin mahaifa ya fara budewa domin haihuwa har zuwa lokacin da zai buɗe gabaɗaya.
- Mataki na biyu: Wannan matakin yana farawa ne bayan bakin mahaifa ya gama budewa gabaɗaya zuwa lokacin da za a haifi jaririn.
- Mataki na uku: Wannan shi kuma yana farawa ne bayan haihuwar jariri zuwa lokacin da aka fitar da uwar mahaifa.
Manyan alamomin naƙuda
Ciwon mara
Mafi akasarin mata ciwon mara shi ne alamar nakuda ta farko da ke nuna cewa nakuda ta fara. Ciwon mara na nakuda yana kama da irin ciwon marar da mata ke yi a lokacin al’ada, amma shi ciwon mara na nakuda yana tasowa ne sannu – sannu sannan ya cigaba da yawaita kuma yana yin tsanani har sai mace ta haihu. Mata suna kwatanta shi da murɗawa da matsewar mara mai zuwa yana kwantawa da kansa.
Ciwon mara na nakuda yana iya kama har bayan mace, sai ta ji kamar an riƙe mata baya, haka kuma wani lokacin yana sauka a ƙafafu. Ciwon marar nakuda yana tasowa da kansa kuma idan ya taso ba abin da mace za ta iya yi ta kwantar dashi, sai dai yana iya kwantawa da kansa bayan ya dauki wani dan lokaci kafin daga baya kuma ya sake tasowa. A haka zai ci gaba yana yawaita da tsananta har sai an haihu.
Fitar majina da jini kaɗan daga farji
A lokacin da ciwon mara ya fara ko kuma kafin ya fara, mace za ta iya ganin wani abu kamar majina mai dauke da jini kaɗan yana fita ta gabanta. Wannan yana cikin manyan alamomin naƙuda, zubar irin wannan abu yana nuna cewa bakin mahaifa ya fara budewa kuma naƙuda ta fara shiga matakin farko saboda wannan majina tana fitowa ne daga bakin mahaifa. Sai dai jinin da ke cikin majinar ba shi da yawa, wani lokacin ma ba a ganin jinin. Saboda haka idan jini ya ɓalle da yawa ko kuma jini kawai, to gaggauta zuwa asibiti domin wannan na daga cikin manyan alamomin naƙuda mai matsala.
Buɗewar bakin mahaifa
A lokacin da nakuda ta fara, bakin mahaifa yakan fara buɗewa sannan ya takura ya shige a cikin mahaifar domin baiwa kan jariri hanyar fitowa. Wannan ita ce babbar alamar da ke nuna cewa mace ta fara naƙuda. Sai dai bayan zubar majina mai haɗe da jini, ba wata alama da mace za ta gane bakin mahaifa ya fara buɗewa. Gane wannan sai mace ta je asibiti idan likita ko unguzoma sun sanya yatsa a gabanta.
Fashewar faya
Faya wata siririyar fata (tantani) ce da take dauke da ruwan zaƙi wanda yaro yake iyo a cikinsa. Faya da kuma ruwan da ke cikinta sun zama kamar wani tafki a cikin mahaifa da yaro yake iyo a ciki. Wannan ruwan ya samo asali ne daga fitsarin da jariri ke yi a lokacin da yake a cikin mahaifa. Fashewar faya tana ɗaya daga cikin manyan alamomin naƙuda. Lokacin da faya ke fashewa ya danganta daga wata mace zuwa wata mace ko ma daga wani ciki zuwa wani ciki. Wata fayar ma ba za ta fashe da kanta ba sai an fasa ta a asibiti. Wannan shi ya sa watarana idan an haihu a gida ana iya haihuwar jariri a cikin jikkar faya sai an fasa an fitar da shi, amna wannan bai faye faruwa ba.
A lokacin da faya ta fashe mace za ta ga ruwa mai yawa ya ɓalle mata har ya jika jikinta, tufafinta da kuma wajen da take. Hakan kuma wani lokacin faya takan fashe a hankali ta yadda mace ba za ta ga ruwan dayawa ya zubo mata ba.
Doguwar naƙuda
Doguwar naƙuda na nufin yanayin naƙudar da ke tafiya a hankali, wato yanayin da ke ɗaukar dogon lokaci ana fama da ciwon naƙuda ba tare da an haihu ba. Wannan yanayi yana iya faruwa a matakin farko ko na biyu na naƙudar. Mai juna biyu na iya kasancewa cikin naƙuda na tsawon sa’o’i da yawa ba tare da matsawa mataki na gaba ba. Manufar kulawa da mai juna-biyu a lokacin haihuwa ita ce domin tabbatar da jariri da uwar suna cikin koshin lafiya da kuma haihu lafiya.
Tsawon lokacin doguwar naƙuda
Doguwar naƙuda kan ɗauki sa’o’i 25 ko fiye ga masu haihuwar farko. Doguwar naƙuda kan iya kasancewa sa’o’i 20 ko fiye ga waɗanda suka taɓa haihuwa aƙalla jariri ɗaya a baya. Sabanin haka, naƙudar da aka saba gani ga mata na ɗaukar awanni 12 zuwa 24 kafin haihuwar fari da kuma awa 8 zuwa 10 ga waɗanda suka taɓa haihuwa.
Abubuwan da ke faruwa lokacin doguwar naƙuda
A yayin doguwar naƙuda ana iya fuskantar:
- Budewar mahaifa: Cervix, wani ɓangare na mahaifa, yana fara buɗewa, amma yana tsayawa kafin ya yi faɗin da ake buƙata zuwa santimita 10.
- Daina motsawar jariri,: Cervix zai gama budewa gabaɗaya, amma jaririn zai daina motsawa zuwa bakin mahaifa.
Yawaitar doguwar naƙuda
Doguwar naƙuda ba ta cika faruwa ba, tana shafar kusan kashi 8% ne na matan da ke haihuwa. Haka kuma tana haifar da kusan kashi ɗaya bisa uku na haihuwa ta hanyar cesarean (C-sections).
Matsalolin doguwar naƙuda
Rashin matsawa daga mataki na farko ko jinkiri a yayin naƙuda yana haifar da rikicewa, doguwar naƙuda a mataki na biyu ta fi tsanani saboda tana ƙara haɗarin:
- Kamuwa da cutar sanyi
- Zubar da jini bayan haihuwa
- Rashin jin daɗin mu’amalar aure
- Gocewar ƙashin pelvic
- Fashewar mahaifa, ba sosai hakan kan faru ba.
Doguwar naƙuda na iya haifar da buƙatar sauya hanyoyin haihuwa daban-daban. Misali, likita na iya buƙatar yin amfani da kayan aikin likitanci, kamar vacuum or forceps, don taimakawa wajen haihuwa. Naƙuda mai tsayi na ƙara yuwuwar yin tiyata C-section.
Haɗarin doguwar naƙuda ga jariri
Nakuda mai tsayi na iya ƙara haɗari ga jariri kamar haka:
- Kamuwa da cutar sanyi, yawanci tana yaɗuwa daga iyaye zuwa jariri
- Ciwon ciki da raguwar bugun zuciya
- Rashin ko ƙarancin iskar oxygen
Dalilan doguwar naƙuda
- Matakin farko na naƙuda shi ne lokacin da naƙuda na asali har zuwa lokacin buɗewar mahaifa. Mataki na biyu shi ne lokacin da mahaifa ta gama buɗewa har sai an haifi jariri.
- A lokacin mataki na farko na nakuda, mahaifa tana noƙewa. Daɗewa a noƙen na iya tsawaita lokacin naƙuda. Abin da ke haifar da wannan shi ne noƙewar mahaifa. Wasu lokuta, wasu magungunan da ake amfani da su a lokacin nakuda (irin su morphine, idan an yi amfani da su da wuri a yayin naƙuda) na iya rage jinkirin haihuwa.
A mataki na biyu na naƙuda, don bayyana tsawon lokacin da ake ɗauka, ana la’akari da, idan lokacin ya wuce sama da sa’o’i uku zuwa hudu ga mata masu haihuwar farko, ko sa’o’i biyu zuwa uku ga matan da suka haihu a baya. A lokacin mataki na biyu, nakuda mai tsawo na iya faruwa idan:
- Jaririn ya yi girma da yawa.
- Ƙofar mahaifa ta yi ƙanƙanta.
- Ƙashin ƙugu ya yi ƙanƙanta da yawa ta yadda jaririn ba zai iya sauka ƙasa ba.
- Tsokar mahaifa ba ta da ƙarfi sosai.
Bincike ya kuma danganta doguwar naƙuda da wasu abubuwan tunani yayin naƙudar kamar damuwa da tsoro.
Alamomin doguwar naƙuda
Mafi yawancin alamomin nakuda suna faruwa ne kafin shigar naƙuda matakin farko da kuma a lokacin da naƙuda ke zangon matakin farko.
Babbar alamar naƙuda mai tsawo ita ce cinye lokaci mai tsawo a kowane mataki ba tare da wani ci gaba ba. Idan mai juna biyu ta kasance cikin naƙuda fiye da sa’o’i 25 (ga mai haihuwar fari) ko sa’o’i 20 (ga wacce ta taɓa haihuwa a baya), naƙudarsu tana tsawaita.
Gwaje-gwajen doguwar naƙuda
Likita zai iya bincikawa idan mai juna-biyu ta gaza ci gaba a yanayin naƙudarta ta hanyar duba sashen mahaifa (cervix) domin ganin ko ya buɗe. A mataki na farko, mahaifa ya kamata ta yi faɗi zuwa santimita 10. Da zarar mai juna biyu ta isa mataki na biyu, jaririn ya kamata ya motsa zuwa ƙasa ta hanyar haihuwa. Idan ba a haifi jariri ba bayan jimullar sa’o’i 20 na naƙuda, to akwai yiyuwar kasancewa cikin doguwar naƙuda.
Hanyoyin kula da mai doguwar naƙuda
Idan mai juna-biyu ta kasance cikin doguwar naƙuda a matakin farko, abin ake bukata shi ne a samu natsuwa don taimakawa wajen faɗaɗar mahaifa. Likita na iya ba da shawarwari kamar haka:
- Matsa kan nono, idan ya dace don taimakawa jiki ya saki ƙarin sinadarin oxytocin, wanda ke ƙarfafa motsawar mahaifa.
- Magunguna, irin su oxytocin (Pitocin) ko wasu magunguna da kan taimaka wajen budewar mahaifa.
- Yin wanka domin samun hutu.
A lokacin mataki na biyu na naƙuda, likita zai iya ba da shawarar:
- Canja wuri akai-akai ko yin yawo.
- Samun hutu.
- Yin amfani da magani kamar oxytocin.
Manazarta
Qc, J. M. (2024, September 27). Prolonged labour Effects on a baby: Complications and risks | BILA. Birth Injury Lawyers Alliance.
Cleveland Clinic. (2025, March 19). Prolonged labor (Failure to progress). Cleveland Clinic.
Whnp-Bc, L. S. M. B. (2018, June 27). Ten common labor complications. Medical News
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.