Skip to content

Paparoma Francis

Paparoma Francis shi ne Paparoma na 266, a jerin paparomomin da suka shugabanci kiristoci mabiya ɗarikar Katolika. Tun daga lokacin da ya hau muƙamin baranda na St. Peter’s Basilica a shekarar 2013, sanye da fararen kaya masu sauki tare da neman addu’o’in jama’a, ya tabbatar wa duniya cewa, ba zai yi zaman sarauta kamar sauran waɗanda suka gabace shi ba.

f409fc e99f5893b671494189ba11f2d44bacafmv2
Marigayi shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Paparoma Francis ke nan.

Francis Bergoglio, Fafaroma na farko daga Amurka, wanda ya ƙare rayuwarsa ga gwagwarmayar tallafa wa talakawa, ya kasance mai kira ga adalci a zamantakewa, da kuma watsi da tarkon iko da aka saba danganta fadar Paparoma da shi.

Haihuwarsa

An haifi Jorge Mario Bergoglio Francis a babban birnin Argentina, wato Buenos Aires a ranar 17 ga Disamba, 1936. Iyayensa sun kasance ‘yan gudun hijira ne daga ƙasar Italiya zuwa Kudancin Amurka.

Karatunsa

Karatunsa na digirin farko a fannin ilmin sinadarai ne, kuma wannan bai hana shi da’awa da wa’azi koyaushe ba, su ne ayyukansa. Ya shahara da su kuma ya tsaya tsayin daka a kan wannan lokacin ba yake matashi. A cikin shekarar 1958 ya shiga Jesuit novitiate a cikin garinsu.

Har wa yau ya sami digiri na biyu a fannin falsafa a shekarar 1963, kuma ya koyar da wannan fanni a kwalejoji da dama a duk faɗin ƙasar Argentina tsawon shekaru goma. Ba da daɗewa ba kuma ya yi digiri a fannin tauhidin kiristanci. An naɗa shi a matsayin firist a shekara ta 1969, kuma ya ci gaba da taka rawarsa a cibiyoyi daban-daban na Jesuit a Argentina.

Karatun digirinsa na uku a Jamus ya yi shi, amma a wancan lokacin ƙarin buƙatu da aikace-aikacen ofishinsa ya sa aka tilasta masa komawa Kudancin Amurka kafin ya kammala karatun nasa.

Halayen jin ƙansa ga talakawa

Komawarsa cikin birnin Buenos Aires, ba da daɗewa ba ya yi suna tare da shahara saboda yadda yake aiki tare da shiga cikin sabgogin matalautan birni. Ya kasance matashin firist (mai wa’azi) da ya zama mai fafutuka wajen ƙwaton hakkin waɗanda aka danne, yana tsayuwa tsayin daka wajen samar da daidaito tare da jaddada muhimmancin tawali’u.

Francis ya yi jagoranci ba da iko ko tursasawa ba, ya yi ne tare da ishara, yafiya ga fursunoni, rungumar waɗanda aka ware, da kuma nuna Ikilisiya a kai a kai ga tattaunawa, sasantawa da tawali’u.

Ayyukansa na da’awa

Ayyukansa a ƙauyukan birnin sun kasance hidima ga waɗanda ba su da muhalli da waɗanda ke fama da wata jarabawar rayuwa, wannan ta sa aka yi masa lakabi da Bishop na Slums. Ƙalubale kuma sun riƙa taso masa yayin da mafi yawan ra’ayoyinsa na ci gaba ne da kuma ra’ayoyinsa na ƙin amincewa da wasu ƙa’idojin addini, wanda ya sa ya zama abokin gaba ga wasu a muƙaman coci.

A ranar 20 ga Mayu 1992 Paparoma John Paul II ya nada shi Bishop na cocin Auca da kuma mataimakin Buenos Aires. Har ila yau ya samu cigaba tare da ɗaga likkafarsa zuwa babban Bishop da primate na Argentina a cikin shekarar 1998.

A matsayin babban Bishop, Francis ya nemi rage matsalar cin hanci da rashawa a cikin cocin Argentina, kuma ya ƙara yawan ayyukan agaji a cikin yankunan birni, asibitoci da gidajen gyaran hali. Ya kuma ba da uzuri a madadin ƙungiyar gamayya da ta gaza yin magana game da mulkin kama-karya a lokacin yaƙin Dirty War da aka yi a ƙasar Argentina.

A cikin 2001, Paparoma John Paul II ya ɗaukaka Francis zuwa Cardinal, wannan cigaba ya ƙara faɗaɗa tasirinsa, sai dai hakan ya kasance wani abu baƙo a tsarin ikon birnin Vatican.

Zaɓarsa a matsayin Paparoma

Rantsar da Francis a matsayin Cardinal ba shi da wani tasiri game salon rayuwar mai tawali’u. Dagewar da ya yi na zama a gidaje matsakaita da rashin son cin gajiyar damammakin ofis ɗin nasa ya ƙara tabbatar masa da sunansa a matsayin mai son gaskiya, dabi’a mai kyau ta musamman.

Bayan rasuwar John Paul II a shekara ta 2005, mutane da yawa sun ɗauki Francis a matsayin ɗaya daga cikin papapili, ko kuma waɗancan Cardinal da ke da ainihin damar zaɓen Paparoma na gaba. A cikin taron, Cardinal Joseph Ratzinger a ƙarshe ya sami nasara kuma ya zama Paparoma Benedict XVI. Bayan shekaru takwas, kuma lokaci ne na Francis.

Paparoma Benedict ya zama Fafaroma na farko da ya sauka daga mukamin Fafaroma a cikin kusan shekaru 600 lokacin da ya yi murabus saboda rashin lafiya a ranar 11 ga Fabrairu, 2013, wanda ya haifar da sabon taron domin sanin wanda zai gaji kujerar St. Peter. A wannan karon ba za a yi musun cewa Francis ba ne, wanda aka zaɓa cikin sauri a rana ta biyu ta taron bayan kuri’u biyar.

Francis Bergoglio ya zama ba kawai Paparoma na farko da wannan sunan ba har ma da Paparoma na farko daga Kudancin Amurka da kuma Yesuit na farko da ya ɗauki wannan nauyin.

Bayan zamansa Paparoma

Hatta hawansa kan karagar muƙamin Paparoma, Francis bai canja dabi’unsa ba. Ba shi ra’ayin ƙawa ko bikin sharholiya da ake saba yi a Vatican, ko kuma zama gidaje masu alfarma, Francis ya zaɓi ya zauna a yanki mafi ƙasƙanci a gidan wani baƙo Domus Sanctae Marthae.

Ɗaya daga cikin halayen Paparoma Francis shi ne ya rage mai da hankali kan matsayi da ikon duniya, abin da ya ayyana a matsayin aikinsa shi ne ”limancin coci da kuma hidimar yin da’awa. Francis ya kasance ɗaya daga cikin fafaromomin da aka fi samun dama a lokacinsu, ana yawan gani a bainar jama’a kuma yana farincikin yin hulɗa da talakawa.

Manufofin da nagartarsa

Paparoma Francis ya fi damuwa da batutuwan adalci na zamantakewa da al’amuran da suka dace fiye da mafi kyawun abubuwan koyarwa.

Kusan daga farkon wa’adinsa Francis ya fusata muryoyin masu ra’ayin mazan jiya a cikin darikar Katolika tare da bayyana ra’ayinsa game da rashin daidaito a duniya, da matsalolin kasuwanci mara shinge da kuma jajircewarsa na yin magana kan illolin sauyin yanayi, kamar yadda babban magatakardarsa na Laudato Si ya bayyana.

Babban mai adawa da hukuncin kisa, Francis ya yi tir da yadda al’ummomin ‘yan ci-rani ke yi a yammacin ƙasar da kuma musgunawa ‘yan asalin ƙasar. Karyata shakkun allurar riga-kafi da ya yi a lokacin annobar Covid-19 da fallasa buƙatar samun kudin shiga ga mahukuntan duniya ya ƙara ɗaukaka sunansa a tsakanin masu sassaucin ra’ayi.

An ba da wani abu na tukuici ga al’ummar LGTBQ su ma, duk da cewa rangwame game da wannan ya gaza cimma burin yawancin masu fafutuka. Haka kuma game da haƙƙin haifuwa na mata, wanda Francis ya sake tabbatar da ra’ayin ƙin zubar da ciki da cocin Katolika ta yi, da kuma matsayin mata a wajensa.

Babu shakka watarana za a riƙa tunawa da Francis a matsayin murya mai gyarawa da sassaucin ra’ayi a cikin cocin Katolika, kuma wanda ya kawo wa addinin sabon ra’ayi a kan matakin duniya, musamman a cikin kare hakkin ‘yan gudun hijira da muhalli, biyu daga cikin muhimman batutuwa masu zafi na wannan zamanin.

Rashin lafiyarsa

A cikin watanninsa na ƙarshe, yayin da bikin Jubilee a Roma, duniya ta shiga damuwa tare da duba ga yadda lafiyar Paparoma ke raguwa.

An kwantar da shi a asibitin Gemelli na birnin Rome bisa kamuwa da cutar numfashi a farkon watan Maris ɗin da ya gabata. Francis ya ci gaba da ganawa da amintattunsa cikin tsanaki da tausayi, har ma daga gadon asibitin da yake kwance, ya riƙa gode wa waɗanda ke kula da marasa lafiya tare da yaba wa duk waɗanda suke taimakawa.

Rasuwarsa

Bayyanar Paparoma Francis ta ƙarshe da ya yi a bainar jama’a shi ne a dandalin St. Peter’s da ke birnin Vatican a ranar Lahadin bikin Easter, 20 ga watan Afrilu, 2025, inda ya yi jawabinsa na Easter na karshe tare da yin kira da a tsagaita wuta a Gaza.

960px Procesija pok. papa Franjo 5
Dubban mutane ne suka yi cincirindon ɗaukar akwatin gawar Paparoma Francis.

Ya mutu a daidai misalin ƙarfe 07:35 agogon ƙasar (UTC+02:00), a ranar Litinin ɗin bikin Easter, 21 Afrilu 2025, yana da shekara 88, a gidansa na Domus Sanctae Marthae. Mutuwar tasa, wanda Cardinal Kevin Farrell ya sanar a tashar talabijin ta Vatican da kuma a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo, ta faru ne sakamakon shanyewar kwakwalwa, wanda ya kai ga suma da kuma bugun zuciya da ba za a iya tashi ba. An yi jana’izarsa a ranar 26 ga Afrilu 2025.

Wurin da aka binne Francis

Wasiyyar Francis, mai kwanan wata 29 ga Yuni 2022, ya maimaita fatansa na binne shi a Basilica na Santa Maria Maggiore a Rome. Bayan mutuwarsa, an binne shi a can bisa ga alkawarinsa, inda ya zama Paparoma na farko da aka shiga cikin Santa Maria Maggiore tun Clement IX a shekara ta 1669.

Albashin Paparoma Francis

A cewar Marca, muƙamin Paparoma a hukumance yana zuwa tare da albashin da ya kai kusan $ 32,000 kowane wata. Paparoma Francis, ya ƙi karɓar wannan albashi. Ya riƙa bayar da su gudummawa, ko kuma ya ba wa gidauniya ko kuma ya rarraba wa ’yan uwa, haka yake yi tun lokacin da ya zama Paparoma na 266 a shekarar 2013. Bisa ka’idojinsa na Jesuit, Paparoma Francis bai taɓa karɓar kuɗi daga Coci ba kafin ya zama Paparoma, Vatican ta tabbatar a 2001.

Adadin dukiyar Paparoma Francis

Marca ta yi ikirarin cewa yawan dukiyar Paparoma Francis ta kai dala miliyan 16, duk da cewa ya ƙi karɓar albashi. Ana yawan yaba masa saboda gudanar da rayuwa mai sauƙi. Paparoma ya yi ƙoƙari sosai wajen daƙile tukuicin kuɗaɗe da ake aika masa tare da rage abubuwan jin daɗin rayuwarsa a matsayinsa na jagoran Vatican, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin addini masu arziki a duniya.

Yawan dukiyar Paparoma Francis ta yi ƙasa da yadda mutum zai yi tsammani idan aka yi la’akari da matsayinsa. A haƙiƙanin gaskiya, Francis yana da ƙarancin arziki fiye da yadda sauran fafaromomi suka tara a tsawon lokacin da suke ofis.

Manazarta

Kukreti, S. (2025, April 21). Pope Francis’ net worth revealed: Know about his salary, perks and assets. Hindustan Times.

Ostberg, René, Stefon, & Matt. (2025, May 7). Francis | Biography, Pope, Laudato Si’, Roman Catholic Church, & Facts. Encyclopedia Britannica.

Suarez Sang, L., & Matranga, A. (2025, April 26). Pope Francis left a last will and testament before his death. Read the full text. CBS News.

Vatican News. (2025, May 4). The Popemobile of Peace: Pope Francis’ final gift to Gaza. Vatican News.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×