Pi Network wani kamfanin fasaha ne da ya ƙirƙiro kuɗin crypto mai suna Pi coin, kamfanin ya wanzu da zummar warware ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen cryptocurrency a duniya. A daidai lokacin da takwaransa wato Bitcoin ke buƙatar abubuwa masu tsada da yawan ilimin fasaha domin shiga a dama da mutum, Pi na ba da dama ga masu hada-hadar kuɗaɗen yanar gizo su samu tare da sarrafa crypto ta hanyar amfani da wayar hannu. Wannan na nufin Pi Network ya ƙirƙiro tsarin kuɗin dijital wanda kowa zai iya shiga a dama da shi.

Mene ne Network Pi?
Pi Network wani shiri ne na fasaha wanda ke ba mutane damar shiga hada-hadar cryptocurrency (kuɗaɗen yanar gizo) ta hanyar amfani da wayar hannu. An fara wannan shiri a cikin shekarar 2019 tare da nufin faɗaɗa harkar crypto zuwa ga mutane da yawa ba tare da manyan kayan aiki masu tsada ko ilimin fasaha ba. Ba kamar Bitcoin ba, wanda ke buƙatar manyan kayan aikin masu tsada, ana iya samun Pi ta hanyar amfani da wayar salula ta yau da kullum.
Malaman Jami’ar Stanford Nicolas Kokkalis da Chengdiao Fan ne suka kirkiro fasahar samar da kuɗin Pi a cikin shekarar 2018. A ranar 14 ga Maris ɗin 2019, suka wallafa farar takarda mai ƙunshe da bayanin Pi tare da sakin manhajar mining ɗin Pi coin.
Yadda Pi Network ke aiki
Tsarin yin mining a Pi Network yana ba da lada ko tukuici iri-iri ga masu amfani da shi. Masu amfani da manhajar suna samun tukuicin shiga cikin manhajar kullum da kullum. Har ila yau, Pi na ƙarfafa gwiwar masu amfani da manhajar don tallafa wa cigaba da inganta yanayin duniyar Pi Network.
Ana amfani da manhajar domin yin mining Pi, inda masu amfani da ita suke shiga ciki su danna maɓallin mining ɗin a duk bayan sa’o’i 24. Masu son fara mining ɗin Pi dole su samu lambobin gayyata daga mamba a da’irar Pi domin yin rijista da manhajar. Pi Network yana da tsarin ba da tukuici wanda masu amfani da manhajar ke samun ƙarin Pi dangane da sabbin mambobin da suka yi rajista.
Tun daga Disambar 2021, Pi na aiki a kan blockchain na fasahar Mainnet ne. A wannan lokacin, masu amfani da manhajar dole ne su kammala tantancewar KYC domin tura Pi ɗin da suka yi mining zuwa blockchain. Pi na ƙoƙarin cire waɗannan takunkumai daga cikin tsarin mining.
Siffofin da tsare-tsaren Pi Network
Pi Network ya mayar da hankali kan ɓangarori guda huɗu ne kamar haka: Pioneer, Contributor, Ambassador and Node Operator.
- Pioneers, su ne masu aiwatar da mining ɗin Pi ta hanyar tabbatar da cewa kullum sun shiga manhajar a wayoyinsu na hannu tare da taɓa maballin mining.
- Contributors, su ne masu gina da’irori na tsaro (security circles) ta hanyar zaɓar amintattun membobi, ƙirƙirar tsarukan tantancewa da tabbatarwa domin gudanar ayyukan manhajar yadda ya kamata.
- Ambassadors, su ne masu alhakin haɓaka manhajar ta hanyar gayyato sabbin masu shiga don yin amfani da ita, yayin da
- Node Operators, su ne ke tabbatar da ayyukan manhajar a kan kwamfutoci.
Pi Network ba ya buƙatar kayan aikin mining masu tsada ko yawan amfani da makamashin lantarki. A madadin haka, yana amfani da tsarin yarjejeniya bisa alakar amincewa da membobi. Masu amfani da Pi Network za su iya mining ɗin Pi ta hanyar amfani da wayoyin hannu na komai da ruwan ka kawai. Pi Network na isar da cryptocurrency ga mutane ba tare da la’akari da ilimin fasaha ko yawan jari da girman na’ura ba.
Tukuicin da Pi Network ke bayarwa
Lokacin da Pi Network ya fara aiki, an saita ƙimar yawan tukuicin da za a samu ta hanyar mining a matsayin 1.6 a kowace awa. Bayan wani lokaci, yayin da yawan masu amfani da Pi Network ke faɗaɗa, tukuicin mining ya sauya, an raba su cikin tsari kamar:
- 0.8 Pi a awa ɗaya bayan adadin masu mining ɗin ya kai 100,000.
- 0.4 Pi a awa ɗaya bayan adadin masu mining ya kai sama da miliyan 1.
- 0.2 Pi a awa ɗaya bayan adadin ya kai miliyan 10.
Ana sa ran tukuicin mining zai ci gaba da raguwa yayin da duniyar Pi Network ke ƙara girma da tumbatsa. An tsara manufar cewa yayin da adadin masu amfani da manhajar ya cimma biliyan daya, lokacin yin mining ɗin Pi ya ƙare.
Yaya darajar Pi coin take?
Har kawo yanzu ba a tantance ƙimar Pi ba a hukumance. Rashin shigar Pi coin cikin jerin kuɗaɗen kasuwar crypto, ya sa kusan a iya cewa ba shi da fa’ida har kawo Nuwamba 2024. A sakamakon haka, babu wani bayanan tarihi kan ayyukan Pi tun da har yanzu ba a ƙaddamar da shi ba a kan kowace manhajar musayar kuɗaɗen cryptocurrency ba.
Mahukunta kamfanin Pi Network ba su bayyana adadin yawan kuɗaɗen da ke yawo ba ko da kuwa an kaddamar da shi a hukumance, amma farar takardar farko da suka wallafa yayin kaddamar da manhajar ta ce ana sa ran samar da jimillar Pi coins ya kai biliyan 100.
Amfani da kuɗin Picoin
Kuɗin Pi wato (Pi coin) yana ba da damar yin hada-hada a tsakanin mutane masu ta’ammali da kuɗaɗe crypto a da’irar Pi Networkba halin yanzu. Masu amfani da manhajar Pi za su iya sayayya da kuɗin Pi a kan kayayyaki da ayyuka a cikin kasuwannin da ke cikin manhajar ta Pi, ko tura tsabar kuɗin daga wani mutum zuwa wani. Developers suna iya ƙirƙirar manhajoji da ke karɓar Pi a matsayin kuɗaɗen sayayya, a tsarin e-commerce wato (kasuwancin yanar gizo). Pi Network yana da tsarin ‘hackathons’ kodayaushe don tallafa wa sabbin hanyoyin inganta manhajar.
Gudummawar Nodes a tsarin Pi Network
Nodes su ne ƙashin bayan kayan aikin fasahar blockchain ta Pi Network. Waɗannan kwamfutoci ne masu gudanar da ayyukan Pi, waɗanda ke tabbatar da hada-hadar cinikayya da tabbatar da tsaron manhajar.
Masu sarrafa kwamfutocin nodes dole ne su kiyaye kwamfutocin, su kasance kodayaushe a kan fasahar yanar gizo (online). Yanar gizon na tafiya bisa tsaruka guda uku: adadin lokacin aiki, damar tashar sadarwa da kuma ayyukan CPU. Nodes tare da tashoshin sadarwa na iya sadarwa kai tsaye da wasu nodes ɗin, wannan na mayar da su masu mahimmanci ga ayyukan tashoshin sadarwa. Manyan Nodes suna buƙatar fasahar sadarwa kodayaushe da wadataccen lokacin aiki tabbatar da aikinsu.
Fa’idojin amfani da Pi Network
Pi Network ya cire takunkumin ilimin fasaha da na kuɗi da suka kewaye duniyar cryptocurrency. Masu amfani da manhajar Pi Network ba sa buƙatar kayan aiki masu tsada ko zurfin ilimin fasaha don shiga wannan hada-hada. Pi yana aiki kamar kowane aikace-aikacen wayar hannu, yana ba wa mutane damar su yi mining ɗin Pi, ta hanyar shiga cikin manhajar kawai su taɓa maballin mining ɗin sai su fita kawai ba tare da makamashin batiransu ya ƙare ko ya ragu ba.
Tsarin algorithm na Pi Network yana amfani da ƙarancin makamashin kuzari fiye da tsarin mining na Bitcoin da sauran su. Wannan hanyar tana rage yawan amfani da makamashin lantarki yayin kula da tsaro da tsarin tabbatar da ayyukan manhajar.
Tsarin tantancewar KYC na Pi yana taimakawa wajen daƙile kutse ko satar asusun mutane, kuma yana tabbatar da ƙa’idar asusu ɗaya ga mutum ɗaya. Pi Network ya haɗa wasu nagartattun na’urori, tare da tabbatar da cewa mai amfani da manhajar yana cikin da’irar amintattun al’ummar Pi Network don kiyaye mutuncin kamfanin na Pi.
Kalubale da haɗarin da Pi ke fuskanta
Pi Network yana fuskantar ƙalubale da yawa. Bayyana tsawon lokacin yin mining, da iyakance hada-hada ta waje, wato ta wasu kuɗaɗen crypto ɗin, suna haifar da wahala ko ma a gaza tantance ƙimar farashin Pi a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen crypto. Masu amfani da manhajar Pi Network dole ne su kammala tantancewar KYC domin samun damar tura Pi ɗinsu zuwa blockchain, wannan kan haifar da cikas wajen karɓar tsarin ga mutane.
Pi yana buƙatar gina ƙaƙƙarfan tsarin manhaja da ayyuka don samar da abubuwa masu amfani na zahiri. Pi yana fuskantar haɗarin zama wani tsari mai ƙima. Dole be Pi Network ya daidaita bunƙasarsa da ingantaccen tsaro yayin da yake ƙara zama buɗaɗɗen tsarin hada-hadar crypto.
Akwai ƙalubale daga sauran kamfanonin cryptocurrencies da sabbin kamfanonin mining na wayar hannu, wannan na iya rage haɓakar Pi. Nasarar Pi Network ta dogara ne ga kulawa da kiyaye buƙatun masu amfani da manhajar tare da haɓaka ingantacciyar hanyar amfani da kuma gwaggwaɓan tukuici mai sauƙi.
Kaddamar da Pi bridge (gadar Pi)
A cikin Satumbar 2022, Pi Network ya sanar da samar da Pi Bridge, wadda ke neman ciki giɓi tsakanin Pi Network da sauran manhajojin harkokin blockchain, wanda ya fara da Binance Smart Chain (BSC).
Pi Bridge, bisa ga ra’ayin developers, sun ce, wata kofa ce wacce za ta kawar da rata tsakanin Pi Network da sauran blockchains, za ta sauƙaƙa samuwar Pi coin ga jama’a tare da samar wa masu amfani da Pi sabon kayan aikin hada-hadar kuɗaɗen crypto marasa tarnaƙi.
Yaushe za a ƙaddamar da Picoin?
Za a ƙaddamar da Pi coin a lokaci guda da bikin buɗe sabon babban shafin yanar gizon Pi Network, wanda ake kira ‘Open Network’, kuma za a jera shi a kan manhajojin musaya da hada-hadar cryptocurrency da sauran manhajojin cinikayyar crypto.
An fara shirin kaddamar da Open Network a shekarar 2022, amma an ɗaga daga baya. Haka nan an ba da sanarwar sakin shi a cikin shekarar 2023, wanda shi ma bai tabbata ba.
Mahukuntan Pi Network sun tsara a cikin Disamba 2023 cewa dole ne a cika wasu sharuɗɗa kafin kaddamar da Open Network da tsabar kuɗin Pi, sharuɗɗan su ne kamar haka:
- Masu amfani da manhajar miliyan 15 dole ne su tsallake tantancewar (KYC).
- Masu amfani da manhajar miliyan 10 kuma dole ne su yi ƙaura zuwa sabon shafin yanar gizon Pi Network.
- Tabbatattun manhajojin 100 na Pi su kasance a wadace a sabon shafin yanar gizon kamfanin na Pi Network.
- Abu na ƙarshe da aka tsara don ƙaddamar da tsabar Pi shi ne rashin samun yanayin waje mai kyau wanda zai iya daƙile nasarar kaddamar da ‘Open Network’.
Pi Network ya fitar da sanarwar a watan Yunin 2024 da ke da rahoton cewa sama da masu amfani da manhajar miliyan 12 sun kammala tantancewar KYC ta asali, tare da miliyan 5.79 sun yi ƙaura zuwa babban shafin. Duk da haka, har zuwa Nuwamba 2024, hukumar Pi Network ba ta sanar da ranar saki da kaddamar da Open Network ba.
Makomar Pi Network a nan gaba
Pi Network yana shirin matsawa daga tsarin da yake a halin yanzu wanda aka bayyana zuwa wani buɗaɗɗen tsari mai faɗi. Wannan cigaba zai ba da damar haɗin-gwiwa da sauran blockchains da musayar crypto, yayin da a hannu guda kuma ake haɓaka yanayin Pi Network ɗin da aikace-aikacen da ke ƙunshe a cikin manhajar. Wani sabon shiri mai taken ‘hackathon’ da Pi Network ke aiwatarwa a yanzu yana ci gaba da samar da kuɗaɗe domin haɓaka sabbin tsare-tsare, tare da cin nasara a baya-bayan nan ta ƙirƙirar kasuwanni, wasanni da ayyukan samun kuɗaɗe.
Pi Network yana da burin zama tsarin hada-hadar kuɗaɗen crypto ta duniya wanda zai samun goyon bayan dukkan kayayyaki da ayyuka na yau da kullun. Taswirar da ke bayyana manufar Pi Network ta haɗa da faɗaɗa ayyukan fasahar nodes, haɓaka musayar kuɗaɗen crypto da samar da haɗin gwiwa tsakanin tsarin kasuwancin na zahiri domin amincewa da karɓar Pi a matsayin kuɗin cinikayyar kayayyaki da ayyuka.
Manazarta
Restha, A. K. (2023, October 4). History of the PI Network and its development team: From the beginning to today. Medium.
“Pi Network (PI): Mining On Smartphones”. (n.d.). Bitget.com.
S, A. (2025, February 7). What is PI Network? Unpacking its vision, prospects, and concerns. BitDegree.
Sergeenkov, A. (n.d.). What is PI Network? Forbes.