Skip to content

POS

POS (Na’urar cirar kuɗi)

Na’urorin POS sun canza yadda ake gudanar da ma’amalolin kuɗi a bangaren cinikayya. A matsayin kayan aiki mai mahimmanci ga kowane kasuwanci, suna daidaita ratar da ke tsakanin hanyoyin hada-hadar kuɗi na da can da kuma na zamani (digital age).

POS ko kuma POP wato (Point of Purchase). Duka biyun a asalinsa suna nufin tsarin kididdige cinikin da mai kanti ya yi a nan take ba tare da wata wahala ba. An fara ƙirƙiro tsarin POS tun a 1879 M. Da sunan ‘Cash Register’.

Na’urar POS da ake cirar kuɗi da ita

Sunan wanda ya fara ƙirƙiro shi James Ritty. Yana da babban shago kayan masarufi. Amma sai ya fahimci ma’aikatansa suna yi masa ɗingushe. Don haka sai ya sa aka kirkiro inji da sunan ‘Incorruptible Cashier’ don ya riƙa sanin adadin abin da ya shigo lalitarsa. A 1906 aka fara jona wannan inji da wuta, ta yadda ya ƙara sauri wajen aikinsa. Sai kuma a shekarun 1970s aka fara haɗa wannan fasaha da na’ura mai ƙwaƙwalwa. Haka ya wanzu har shekarun 1990s a inda aka fara ƙera injina na zamani, waɗanda su da kansa kwanfiyuta ne. Shigowar shekarun 2000s a nan ne aka fara samar da irin waɗannan injin amma waɗanda za a iya ɗauka a hannu daga nan a kai su can, suna kiran su da ‘mPOS’-wato Mobile POS.

Tsarin POS ya shigo Nigeria sosai 2012 M. A lokacin da Babban Bankin Tarayya ya sahale wa ‘yan ƙasa su riƙa amfani da shi saboda rage zirga-zirga da kuɗaɗe a hannu. Kafin haka kaso 90% na cinikayya ana yin su da kuɗaɗe a hannu tsirara!

Akwai POS kala-kala wanda kamfanoni da wuraren sayar da abinci da abin-sha da otel-otel suke amfani da su. Kowanne yana neman wanda ya dace da buƙatarsa. Amma amfani da POS a matsayin wurin da za a iya zuwa a nemi su ba ka wani gwargwado na kuɗi, su kuma su yi amfani da katin mutum na ATM su ɗibi wannan kuɗin su tura zuwa account ɗinsu a maimakon wanda suka ba shi a nan take, wannan ya fara ne a ‘yan shekarun nan, ba da daɗewa ba.

Na’urar POS marar madannai

Kafin mutum ya buɗe wurin harkar POS sai ya bi wasu matakai kamar haka:

i- A dokokin Ƙasa an yarda a buɗe irin waɗannan wurare kamar yadda aka faɗa a baya.

ii- Masu harkar POS suna da alaƙa da bankuna ta fuskar sai sun je sun yi rijista da wani banki tukuna. Daga cikin hikimomin yin haka shi ne don bankin zai ga ana hadahadar kuɗaɗe masu yawa akai-akai, sai ya zamo ba zai damu ba, saboda ya yarda da account ɗin da ake wannan hadahadar da shi.

iii- Akwai certificate da bankin zai bawa wanda ya yi rijista da shi a matsayinsa na “agent”-wakilinsu. Don haka zai yi rawa da bazar wannan bankin a iya ɓangaren da suka yarjewa POS ya yi hidima.

iv- Bankin da aka yi rijista da shi yana son ya ga motsin wannan POS aƙalla sau goma a rana don ya tabbatar da yana aiki. Wannan ba tare da ya kula da yawan kuɗin da za su shiga ko za su fita ba ta hanyar wannan POS ɗin.

v- Zai biya kuɗin hayar shago da wutar lantarki da kuɗin data da yake amfani da ita don hawa kan intanet ko kuɗin cajin waya, da sauransu.

A cewar Malam Isa Abdullahi, wani masanin tattalin arziki, kawo harkar POS na ɗaya daga cikin abubuawa mafi alheri da aka yi a harkar tattalin arziki a Nijeriya cikin ‘yan shekarun nan.

Galibi saboda yadda harkar ke bai wa ɗimbin matasa damar samun aikin yi musamman waɗanda ba su yi karatu mai zurfi ba.

Ya kuma ce na’urorin POS sun sauƙaƙa hada-hadar kuɗi kuma farin jininsu na karuwa ne saboda ‘’suna ƙofar gidanka.

Malam Isa Abdullahi, wanda babban malami ne a Sashen Nazarin Tattalin Arziki da Raya Kasa a Jami’ar Tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, ya ce cibiyoyin POS na da saukiny sha’ani’’ kuma ba sa ɓata lokaci.

Ya ce , “muhimmancin POS ya ƙara fitowa fili ne saboda babu bankuna a galibin yankunan karkara, ko hatta a birane inda ake da bankuna, mutane kan shafe sa’o’i da dama a bankunan ko a layin na’urorin hadahadar kuɗi na ATM.

Ko da yake Nijeriya ƙasa ce da tattalin arzikinta ya dogara kusan kacokam a kan man fetur, harkokin POS yanzu sun nuna cewa lallai akwai babbar dama a fannonin da ba na man fetur ba kuma suna ƙara shigar da mutane a harkar banki da hadahadar kuɗi.

Shi ma Shugaban Kungiyar Masu Hadahadar Kudi ta Tafi-da-Gidanka ta Nijeriya, Victor Ojolo, yana da irin wannan ra’ayi, gudummowarsu ga tattalin arziki gagarumace.

A cewarsa, harkar POS na samar da ɗimbin ayyukan yi, ba ga masu harkar kai tsaye kaɗai ba, har ma da masu wasu harkokin da ke da nasaba da su kamar kamfanonin da ke yin takardun da ake yin rasidi da su.

Wannan na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar rashin aikin yi a Nijeriya wanda adadinsa ya kai kashi 33 cikin dari a 2021.

Mr Olojo ya ce “cibiyoyin POS na tallafa wa ayyukan bankuna da kuma sauƙaƙa su domin ba dole sai mutane sun shiga bankuna za su yi hadahadar kuɗi ba, musamman na ƙananan kuɗaɗe.”

“Harkar POS ta kawo juyin-juya-hali a ayyukan banki a Nijeriya,” inji shi. Ya kara da cewa yanzu “POS ta kutsa lunguna da sako-sako yadda bankuna ba su taɓa tunani ba.”

A zahiri ma shagon POS wani ƙaramin banki ne da yake gudanar da wasu daga ayyukan bankin da yake da rijista da su. A lokacin da mutum ya yi amfani da ATM ya ɗebo kuɗi daga injin da banki suka ajiye don ɗibar kuɗaɗe, zai ga bankin sun ɗebi wasu ‘yan kuɗaɗe na hidamar da suka yi wa mutum. Bankin da mutum yake da account suna ɗan yi masa ragi. Amma wani bankin daban suna ɗiba fiye da yadda nasan suka ɗiba. Don haka, shi kansa mai POS ba dalilin da zai sa ba zai karɓi wani kaso na hidimarsa ba!

Masu POS suna yin amfani da ƙwarewarsu da wani ɓangare na kuɗi da suka sa a katin wayarsu ko na data ɗin da suka saya. Haka nan suna amfani da wutar lantarki da injin POS ɗin kansa da suka saya da zaman da suke yi na kuɗi a shaguna. Bugu da ƙari, sun ragewa mutane wahalar bin layin ATM ko na cikin bankuna da aka saba yi. Wannan duka a bayyane yake cewa sun yi wa mutum aiki, don haka masu POS suna da cikakken haƙƙin a biyasu kuɗin wahalarsa.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×