Sahara ko Hamada yanayi ne da ke tattare da ƙarancin ruwan sama da ƙarancin ciyayi a wasu yankunan duniya. Ana samun irin wannan wurare a yankuna daban-daban na duniya, kuma sun mamayi kashi ɗaya bisa uku na dukkan doron ƙasar duniya. Mutane da yawa suna tunanin cewa sahara mai yashi ita ce kawai nau’in hamada. Akwai nau’ikan hamada daban-daban da suka haɗa da yashi, dutse, gishiri da sauran su.
Ana samun hamada a kowace nahiya. Dukkan wurin da ke samun ƙasa da santimita 25 (ko kuma inci 10) na ruwan sama ana ɗaukar sa a matsayin yankin hamada. Hamada wani yanki ne na manyan yankuna da ake kira busasshen ƙungurmin daji. Waɗannan wuraren suna da ƙarancin danshi da ruwa.
Duk da cewa ana yawan siffanta hamada da yanayin zafi, amma akwai ciyayi masu sanyi a yankunan. Hamada mai zafi mafi girma a duniya, ita ce saharar arewacin Afirka, yanayin zafin wajen yakan kai har zuwa digiri 50 a ma’aunin celcius (ko kuma 122 a ma’aunin farenheit) a rana. Amma wasu hamadojin koyaushe suna da sanyi, kamar hamadar Gobi da ke Asiya da yankin Polar na Antarctic da Arctic, waɗanda su ne mafi girma a duniya. Wasu kuma hamadojin na duwatsu ne. Bai fi kashi 20 cikin 100 na hamada ne kawai ke rufe da yashi ba.
Mafi bushewar hamadoji, su ne irin su hamadar Atacama ta Chile, tana da sassan da ke samun ƙasa da milli-mita biyu (inci 0.08) na ruwan sama a shekara. Irin waɗannan wurare suna da tsauri tamkar a wata duniyar daban, wanda har masana kimiyya sun yi nazarin su don gano kamanceceniya da duniyar Mars.
Dabbobin da tsirrai a hamada
Dabbobin da ke yankunan hamada suna da hanyoyin da ke taimaka musu su ji sanyi da amfani da ruwa kaɗan. Raƙuma na iya tafiya tsawon makonni ba tare da shan ruwa ba, kuma hancinsu da gashin ido na iya zama shinge ga zafin yashi. Yawancin dabbobin hamada, ba su da lokacin dare, suna fitowa farauta ne kawai lokacin da rana mai zafi ta faɗi. Wasu dabbobi, kamar kunkurun hamada a kudu maso yammacin Amurka, na shafe tsawon lokacinsa a karkashin ƙasa. Yawancin tsuntsayen hamada suna ratsa sararin samaniya don neman abinci. Kuma a cikin ƙwari, ƙwaro na na iya ratsa raɓa daga iska don neman ruwa. Saboda sauye-sauye da suke fuskanta na musamman dalilin yanayin muhallinsu, dabbobin hamada suna da matuƙar rauni na sauya wurin zama.
Tsirran da kan fito a yankin hamada na iya rayuwa ba tare da ruwa ba tsawon shekaru a lokaci guda. Wasu tsirran sun dace da busasshen yanayi ta hanyar girman dogayen saiwoyin da ke zuƙo ruwa daga zurfin ƙarƙashin ƙasa. Sauran tsirrai, suna da hanyoyi na musamman na adana ruwa a jikinsu.
Hamada da canjin yanayi
Wasu yankuna na duniya da ke fama da sauye-sauyen yanayi na iya rikiɗa zuwa hamada cikin ƙaramin lokaci. Wannan sauyi ba fari ne ke haifar da shi ba, amma yawanci yana tasowa ne dalilin sare dazuzzuka da kuma buƙatun ’yan’adam na kauce wa zama a yankin marar ni’ima. Tattaka ƙasa da kofaton dabbobin kiwo na iya sakwarkwata ƙasa wanda hakan kan haifar da zaizayar ƙasa daga guguwa da kuma ruwan sama. A arewacin kasar Sin, bunƙasar gina birane, wanda ya sa akasarin ƙasar ba ta da kariya daga zaizayar da iska ke haifarwa da kuma tarin laka daga hamadar da ke kewaye, ya haifar da matsalar kwararowar hamada, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar ta gina wata babbar katanga mai suna ‘Great Green Wall) a matsayin kariya don hana mamayar hamada.
A cikin hamadojin da ake da su a duniya, wasu suna cikin haɗari saboda canjin yanayi. Ɗumamar duniya tana barazanar canja yanayin ƙasar hamada, yanayin zafi na iya haifar da ƙarin gobarar dajin da ke canja yanayin sahara ta hanyar ƙone bishiyu da ciyayi marasa saurin girma da maye gurbinsu da masu saurin girma.
Yawancin tsirran hamada na iya rayuwa na ɗaruruwan shekaru. Amma a ƙasar California, babbar bishiyar Joshua (Yucca brevifolia), tana da shekaru 1,000, ba za ta iya rayuwa a yanayi mai zafi sosai ba, a cewar masana kimiyya. Idan ba ta iya rayuwa ba, hakan zai iya shafar nau’ikan tsirrai wanda ke sanya ƙwai a cikin furen wannan bishiya.
Haka nan nau’in tsuntsayen hamada na iya kasancewa cikin haɗari daga sauyin yanayi, saboda zafin rana yana haifar da bushewar ruwa da kan kai su ga mutuwa.
Siffofin yankunan hamada
Bambance-bambancen nau’ikan hamada suna da yawa sosai saboda ma’anar ta ƙunshi nau’ikan halittu daban-daban. Dukkansu suna da wasu alamomi waɗanda suka cancanci zama hamada, kodayake yanayin zafi ba ya daga cikin manyan alamomin. Wasu hamadojin suna da zafi sosai ko sanyi sosai, don haka yana da wuya kowace hamada ta fuskanci yanayin zafi gabaɗaya. A takaice hamada yanki ne na ƙasa wanda ke da siffofi kamar:
- Ƙarancin saukar ruwan sama (yawanci ƙasa da milli-mita 250 a shekara)
- Busasshiyar ƙasa/ tsandauri
- Ƙananan shukoki da dabbobi
Idan aka yi na nazarin hamadoji daban-daban, za a ga dukkansu suna da waɗannan siffofi. Ana samun bambance-bambancen abubuwa daban-daban da suka haɗa da matakan zafi, nau’in ƙasa da sauran su.
Nau’ikan hamada
Hamadar dutse
Hamadar dutsen ta ƙunshi duwatsu da ƙasa mai duwatsu maimakon yashi. Waɗannan duwatsun na iya bambanta dangane da girmansu da abin da ke ciki. Sau da yawa ana lalata su ta hanyar tafiyar matakai na lokaci. Rashin tsirowar ciyayi a cikin waɗannan yankuna yana ba da damar bayyanar duwatsu cikin sauƙi kuma su mamaye sarari da yawa. Waɗannan yankunan hamada galibi suna cikin busassun yankuna masu tsandauri tare da ƙarancin saukar ruwan sama. Rashin zuƙar ruwa da adana shi a cikin ƙasa mai dutse yana sa ciyayi yin wahalar girma, yana kuma haifar da ƙarancin ciyayi a cikin waɗannan yankuna.
Yanayin a cikin hamadar duwatsu sau da yawa yana da tsanani. Yanayin rana na iya yin yawa sosai kuma zafin dare na iya raguwa kaɗan. Tsirrai suna da yawa amma suna iyakance a wuraren da ke da tarin ƙasa da ruwa mai yawa. Wasu tsirran na iya kasancewa cikin ƙananan ramuka ko ramukan a cikin duwatsu inda za su iya girma kuma su samu sinadaran haɓaka. Waɗannan tsirrai galibi suna da ƙarfi kuma sun dace da yanayin dazuzzuka da iyakokin ƙasa.
Hamadar yashi
Hamadar yashi sanannen nau’in hamada ne wanda ke da alaƙa da samun yawan yashi a doron ƙasa. Ana samun waɗannan hamadojin a sassa daban-daban na duniya kuma suna ba da siffofi na musamman. Tarin yashi yakan mamaye yankin hamada mai yashi. A irin wannan wurare dai yashi ne ke taruwa kuma yana canjawa akai-akai saboda iskar da ake yi a yankin. Yana iya yin tsayi sosai mai ban sha’awa.
Hamadar yashi yawanci tana cikin busassun yankuna inda ake samun ƙarancin ruwan sama da saukar raɓa. Rashin ruwan sama yana taimakawa wajen tara yashin, domin kuwa ruwa yana da mahimmanci wajen tafiyar da zaizayar ƙasa da jigilar ruwa daga waje zuwa waje. Yanayin da ke cikin hamadar yashi yana da tsananin zafi. A cikin yini, yanayin zafi zai iya yin yawa sosai saboda tsananin hasken rana. Da daddare, yanayin zafi na iya raguwa da sauri saboda rashin girgije da ƙarancin zafi a fagen.
Hamadar Polar
Kodayake ana yawan danganta hamada da yanayin zafi sosai, yanayin zafi ba ma’aunin hamada ba ne. Hamadar Polar tana da yanayin sanyi mai tsananin gaske, tare da ƙarancin yanayin zafi da ƙarancin hazo a lokacin zubar dusar ƙanƙara. Ana iya samun su a cikin yankunan polar na duniya, watau kusa da poles ɗin arewa da kudu.
Raɓa a cikin hamadar Polar tana da iyaka kuma yawanci tana zuwa ta hanyar dusar ƙanƙara. Saboda rashin yanayin zafi, dusar ƙanƙara ba ta narkewa cikin sauƙi kuma tana taruwa a ƙasa. Wannan yana haifar da wani nau’in kankara wanda ke rufe doron ƙasa. Wannan yana ƙara wahalar zuƙar ruwa ga ciyayi kuma yana daƙile girman ciyayin. Wannan ƙarancin ciyayi da ke akwai ya ƙunshi akasari ciyayin lichens da mosses. Sun fi dacewa da matsakaicin yanayin zafi da rashin ruwa fiye da sauran tsirrai. Dangane da dabbobi a cikin hamadar polar su ne beyar polar da penguins. Waɗannan dabbobin suna daidaita da wannan yanayi musamman sanyi, kasancewar suna da kitse mai yawa.
Sahara mai zafi
Ɗaya daga cikin manyan siffofin wannan hamada mai zafi shi ne tsayin yanayin zafi. Hamada mai zafi yanki ne wanda ke da yanayin zafi sama da 40 ºC/104ºF a wasu lokuta. Hazo mai zafi ba ya da yawa kuma ba ya samuwa a bisa ƙa’ida. Tsirrai a cikin hamada masu zafi ba su da yawa kuma sun dace da yanayin zafi da bushewa. Dabbobin da ke rayuwa a wannan yankuna yawanci suna jure yanayin zafi da rashin ruwa.
Saharar bakin teku
Ana samun waɗannan yankuna a kusa da bakin tekuna. A cikin waɗannan wurare, mu’amala tsakanin teku da ƙasa tana haifar da bushewa. Gudun ruwan da iskar bakin tekun na iya kawo danshi a yankunan. Yanayin hamadar bakin teku gabaɗaya ba ta da armashi kuma ruwan sama kaɗan ne. Tsirrai a wannan yanki sun bambanta, ya danganta da wadatar ruwa da kuma tsananin iskar da ke bakin tekun. Kasancewar ruwa a cikin nau’ikan tafkunan kusa, magudanan ruwa ko koguna na iya jawo nau’ikan tsuntsaye da halittun ruwa a yankunan.
Sahara mai gishiri
Waɗannan yankunan sahara ne waɗanda suka yi fice saboda kasancewar yawan gishiri a samansu. Waɗannan abubuwa masu ɗanɗanon gishiri da suka mamaye doron ƙasa, suna samuwa ne lokacin da ruwa ya ƙafe, yana barin sinadaran gishiri wanda ke ƙaruwa a hankali.
Wannan hamada yawanci tana cikin busassun yankuna da ke da busasshiyar ƙasa inda tiririn ruwa ya yi yawa kuma saukar ruwan sama ta yi kaɗan. Rashin ruwan sama da yawan iska yana ba da damar sinadaran gishiri su taru su dunƙule a saman ƙasa. Yanayin na iya zama busasshe da zafi sosai. Tsirrai ba su da yawa kuma kaɗan ne za su iya rayuwa a cikin waɗannan matsanancin yanayi. Dabbobin da ke zaune a cikin wadannan yankuna yawanci suna jure rashin ruwa da yawan gishiri.
Sahara mai sanyi
Waɗannan hamada tana da yanayin sanyi mai tsanani tare da ƙarancin zafi a mafi yawan lokutan shekara. A shekara, yanayin zafi yana kasancewa ƙalilan. A wasu lokuta, waɗannan yankuna suna iya kaiwa ga matsanancin sanyi. Ruwan sama a cikin wannan hamada ya yi ƙaranci ainun, yana sauka ne ta hanyar dusar ƙanƙara.
Tsirrai a wannan yanki ba su da yawa. Yankunan sun ƙunshi tsirrai masu ƙarfi waɗanda suka dace da yanayin sanyi da bushewa. Dabbobin da ke cikin wannan sahara su ma suna samun nagartattun abubuwan da za su iya rayuwa a cikin wannan yanayi mai tsauri. Dabbobin da ke rayuwa a wannan hamada mai sanyi galibi suna da kauri da kitse mai yawa ko kitsen da ke kare su daga tsananin sanyi.
Busasshiyar sahara
Waɗannan hamadoji suna samun ruwan sama na shekara-shekara na kasa da milli-mita 250. Rashin bushewar yanayi a cikin wannan hamada ya samo asali ne saboda dalilai da yawa, kamar saukar iska wanda ke iyakance samuwar gajimare da rashin samun danshi. Akwai hamadar Simpson dake cikin Austiraliya a matsayin misalin busasshiyar hamada.
Manazarta
Nag, O. S. (2018, August 10). What animals live in the Sahara Desert? WorldAtlas.
The Daily Co. Different types of deserts. The Daily Co.
National Geographic (n.d) Deserts explained. National Geographic.