Wannan kalma ta sulhu Balarabiya ce da ta shigo cikin harshen Hausa mai nufin samar da daidaito a tsakanin masu jayayya da juna a kan wata matsalar rayuwa. Kalmar sulhu kan yi shige da fice a cikin magangannun Hausawa na yau da kullum ba sai a fagen warware rikicin faɗa ba, a’a ana amfani da kalmar domin a sasanta masu cikini a kasuwa. Misali akan ce “Na sulhunta cinikin.” Ma’ana, an sasanta masu sayen wani abu.
Sulhu wata hanya ce ta tattaunawa domin warware wata matsala a tsakanin mutum da mutum. Misali
akan sasanta a tsakanin mata da miji idan wata matsala ta faru, ko a tsakanin aboki da aboki ko maigida da yaronsa ko maƙwabci da maƙwabci ko kuma al’umma da al’umma. Sulhu wata hanya ce ta cimma matsaya a tsakanin al’ummu biyu da suke jayayya da juna. Sulhu wata hanya ce ta tattaunawa da ake yi da nufin magance fitina tare da samar da wata yarjejeniyar zaman lafiya da fahimtar juna.
Idan aka yi la’akari da bayanan da suka gabata za a ga cewa, sulhu ya ƙunshi duk wata hanyar tattaunawa da za a yi amfani da ita domin shawo kan wata matsalar yaƙi ko tarzoma ko bijerewa ko tawaye a tsakanin masu jayayya da nufin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Sulhun gargajiya
Wannan dabaru ne da al’ummar Hausawa ke amfani da su wajen magance rikici da fitina a cikin al’umma tun gabanin su shaƙu da wasu baƙin al’ummu. Irin wannan sulhu Bahaushe ya gade shi ne tun kaka da kakanni bai samo tasiri daga wasu al’ummu ba. Dama akwai irin wannan al’ada a cikin ɗabi’un Bahaushe na zamantakewa, kafin
Musulunci ya zo ya ƙarfafa shi.
Rabe-raben sulhu
Masana ilimin zaman lafiya da sasantawa sun kasa sulhu gida biyu; sulhun ruwan sanyi da lumana da kuma sulhun fafatawa.
Inda suka tafi a kan cewa shi sulhun ruwan sanyi, sulhu ne da ake yi a farkon rikici kafin shiga yaƙi a tsakanin ɓangarora guda biyu. Masu shiga tsakani kan shiga su warware matsalar ba tare da ɓata lokaci ba. Yayin da sulhun fafatawa yake nufin irin sulhun nan ne da ake yi bayan ɓarna da zubar da jini, wato yaƙi. A irin wannan sulhun waɗanda aka rinjaya za su nemi aje makamai domin a sasanta. Dangane da haka akwai sulhun gargajiya iri biyu muhimmai kamar haka:
Sulhun cikin gida
Wannan nau’i ne na sulhun gargajiya ana yin sa ne a tsakanin mutane da ke zaune a muhalli ɗaya, suke kuma gudanar da rayuwarsu tare da al’adunsu iri ɗaya. Bisa ga al’adar Bahaushe, idan aka sami wani rashin jituwa ya faru a tsakanin mutum da mutum akan sanya magabaci misali, maigida domin ya shigo ciki ya sasanta lamarin. Idan ya fi ƙarfinsa ne yakan kai ga mai unguwa ko hakimi domin ya sulhunta lamarin. Shi kuwa mai unguwa ko Hakimi yakan kai matsalar a gaba idan ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Daga cikin matsalolin da ke buƙatar sulhun cikin gida akwai sulhun:
• Zamantakewa a cikin gida
- Mata da Miji.
- Kishiya da kishiya.
- Ɗa da Mahaifinsa ko Mahaifiyarsa.
- Wa da ƙanensa.
- Matan wa da ƙani.
- Matan ɗiya da mahaifan maigida.
• Zamantakewar yau da kullum
- Maigida da yaronsa.
- Maƙwabci da maƙwabci (maƙwabcin gida ko gona ko rumfar kasuwa ko wajen aiki).
- Hakimi da talakawansa.
- Limami da babiyansa.
- Masu sana’a iri ɗaya (masunta, da manoma da mahauta da ma’aska da magina da sauran su.
Sulhun waje
Wannan nau’i ne na sulhu wanda ake yi a tsakanin al’umma da wata al’umma da suke da mabambantan ra’ayoyi ko aƙida ko sana’a. Irin wannan sulhu an fi samun sa bayan an fafata da gwada ƙarfin tuwo da na iko. Daga cikin ire-iren wannan sulhu kuwa sun haɗa da:
- Sulhun ƙabila da ƙabila.
- Sulhun daula da daula.
- Sulhun ƙasa da ƙasa.
- Sulhun manoma da makiyaya.
Rikice-rikicen da ke haddasa sulhu
Akwai abubuwa da dama da ke haifar da rikice-rikice a cikin al’umma waɗanda ke buƙatar zaman sulhu kamar haka:
- Yaƙi.
- Rikicin Aure.
- Rikicin addini.
- Cinikin gona da gida da filaye.
- Ɓarnar Fulani a gona.
Dalilan sulhu
Al’umma kan buƙaci sulhu ne idan ɗayan waɗannan dalilan suka faru kamar haka:
- Idan wani sashe na al’umma ya cuci wani.
- Idan ana tsoron kai wa ga abin kunya.
- Idan ana tsoron a ce kuna kallo aka yi ɓarna.
- Idan ana tsoron ka da rikici ya kawo a gare ka/ku.
- Idan ana tsoron ka da a zalunci mai gaskiya ko marar ƙarfi.
- Idan ana tsoron zumunci ya lalace.
- Idan ana tsoron ɓarnata dukiya da rayuwa.
- Don kaucewa wata ɓoyayyar manufa, misali tattalin arziki daga mai yin sulhun.
Sigogin sulhu
Sulhu yana da sigogin da ke tabbatar da samuwarsa a cikin al’umma. Waɗannan sigogin kuwa sun haɗa da:
- Sulhu na buƙatar masu shiga tsakani domin warware matsalar.
- Sulhu na buƙatar samar da wata manufa ta musamman.
- Dole a bayyana tare da tattauna manufar a tsakanin ɓangarorin da ke rikici ko jayayya.
- Bayan tattaunawar, akwai buƙatar samar da wata yarjejeniyar zaman lafiya.
- Sulhu na buƙatar mutunta yarjejeniyar tare da kare ta a kowane irin yanayi ba tare da karya ta ba, ko da kuwa ɗayan ɓangaren zai cutu da sakamakon.
- Masu sulhuntawa su kasance ‘yan ba ruwanmu a zahiri.
Muhimmancin sulhu
A nan darasin zai dubi matakan sulhu da zaman lafiya da Bahaushe yake da su a jiya tare da kallon yadda za su taimaka wajen magance rikice-rikicen da ƙasar nan take ciki a yau. Daga cikin darussan da za a koya a matakan tsaro da kariyar Bahaushe a yau sun haɗa:
Tattaunawa tsakanin gwamnati da tsagerun Nija Delta da ƙungiyar Boko Haram da kuma ‘yan ta’adda waɗanda ke garkuwa da mutane da kawo barazana ga zaman lafiya da tattalin arzikinmu. Wannan matakin jihar Zamfara ta ga amfaninsa, jihar Katsina ma ta yi irin wannan yunƙurin na sasantawa da Fulani.
Samar da yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa kamar yadda ya faru a tsakanin daular Sakkwato da ta Kabi, kuma yake faruwa a yanzu da wasu Fulani ‘yan tada zaune tsaye.
Yaƙar cin hanci da rashawa tare da ɗebe kwaɗayin abin duniya da mutane suka sanya a gaba a yau.
Sanya ci gaban kasa da bunƙasar tattalin arzikinta bisa ga abin da mutum zai samu na ganimar siyasa, kamar yadda masu jihadi suka yaƙi sauran daulolin ƙasar Hausa da nufin faɗaɗa daular da a ƙidojinta.
Manazarta
Jonah, Onuaha; Nigotiation and Mediation Process: in Peace Studies and Conflicts Management in Nigeria. UNN, 2009, page 110.
Jonah, Onuaha; Violent and Non Violent Methods of Negotiation. Nigotiation and Mediation Process: in Peace Studies and Conflicts Management in Nigeria. UNN, 2009, page 130.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.