Kafin mu shiga cikin bayani game da ma’anar tarken adabi, zai fi kyau mu ɗan waiwaye adon tafiya dangane da ma’anar adabi amma a taƙaice da kuma abin da ya ƙunsa.
Ma’anar adabi
Adabi na nufin fasahar al’umma da ta shafi harshe, ita wannan fasahar ana wanzar da ita ne a magance ko a rubuce. Shi adabi na Hausa ya kasu zuwa gida biyu. Akwai adabin gargajiya ko adabin baka (oral literature ko orature) da kuma adabin zamani ko rubutaccen adabi (modern ko written literature).
Adabin gargajiya wani nau’i ne na adabi da ya samo asali tun daga tale-tale, wato daga wajen al’ummar Hausawa na farko. A taƙaice, kusan babu wanda zai iya ƙiyasta daɗewar wannan adabin a duniya. Ɗangambo (1984) ya karkasa adabin gargajiya zuwa manyan gidaje guda uku, akwai waƙar baka, da wasan kwaikwayo na gargajiya da kuma habarce
(zantuttukan fasaha na al’umma).
Shi ma adabin zamani wato rubutaccen adabi ya kasu zuwa gida uku kamar yadda aka kasa adabin gargajiya. Kashe–kashen sun haɗa da rubutacciyar waƙa da rubutaccen zube, sai kuma rubutaccen wasan kwaikwayo.
Ma’anar tarken adabi
Tarken adabi wata hanya ce ko dabara da masu ilimi ke yi don yin sharhi ko kushe ko ƙarin bayani a kan wani batu na ilimi. Ayyukan adabi kuwa suna cikin batutuwa na ilimi. Masana da kan yi tarke kan wani batu, sai sun yi masa nazari na ƙwaƙƙwafi ta hanyar bin diddiginsa, sannan su feɗe shi daga farko har ƙarshe.
Tarken adabi a gargajiyance
Tarken adabi a gargajiyance kamar yadda Gusau (2008) ya bayyana, ba wata fitacciya ko sananniyar hanyar nazari ba ce wacce aka tsara kuma aka amince da ita ba. Hanya ce wadda ake amfani da ita kara zube don a bayyana ra’ayi game da waƙa ko littafi ko wani rubutu. Ta fi ƙunsar zantuttuka na yabo ko na kushewa da ake amfani da su don auna darajar abu.
• Waƙa
Waƙa na da ma’ana ta fuskoki mabambanta a takaice waƙa na nufin tsararriyar magana ce ta hikima da ake rerawa ba zance irin na maganar yau da kullum ba, cikin zaɓaɓɓun kalmomi don samar da nishaɗi da kuma isar da saƙo.
Gusau (2001) ya ce “waƙa ta bambanta da taɗi na yau da kullum. Aba ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe. Harshen waƙa cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu ƙa’idojin nahawu.
Babu hanyar nazarin waƙa da aka tsara don yin tarkenta a gargajiyance sai dai hanyar da ake amfani da ita kara zube don bayyana ra’ayi. Wannan hanya ta ƙunshi bayyana waƙa da cewa:
– ta yi armashi
– ta ƙayatar
– ta burge
– ta tsaru
– ta waƙu
– ai ba dama
Wannan zantukan su ne ajin farko da ke nuna waƙar ta yi kyau ainin.
Akwai wasu zantukan ko yabon kamar;
– a yaba
– ta yi kyau
– ta gamsar
Waɗannan kuma waƙar mai kyau ce mai daraja ta biyu.
– ba ta kai mini ba
– ba ta yi kyau ba
– ga ta nan dai
Wannan rukunin kuwa ba yabo ba ne kushe ne.
Haka zalika kuma akan lura da waɗannan abubuwa yayin tarken waƙa a gargajiyance:
• daidaitaccen kari (bahari)
• daidaitaccen amsa amo
• salo mai armashi
• amfani da azanci
• sarrafa harshe
• muhimmancin saƙo da amfaninsa
• faɗar gaskiya, kyakkyawan ra’ayi
Malaman addini kan ƙara da cewa: waƙar mai amfani ce ko ta hululu ce, in ta addini ce, shin ta yi daidai da:
– Alƙur’ani
– Hadisi
– Ijma’i
– Ƙiyasi
– Amfani da Larabci
– Ɗariƙa (ko akasi)
• Zube
Zube ya ƙunshi zantuka gajeru ko dogaye na hikima da ake shiryawa jimla-jimla ko shimfiɗe, sannan a gabatar da shi da ka a kuma wanzar ta baka. Waɗannan guntayen zantuka sun haɗa da: tatsuniya, da karin magana, da almara, da kacici-kacici, da zaurance, labarai, da tarihi, da tarihihi da sauransu.
Yahaya (1988) ya bayyana matakan da za a yi amfani da su wajen tarken adabin baka na zube a gargajiyance kamar haka:
• Tubalin Gini: Kamar mutane da dabbobi da tsuntsaye da aljanu da ƙwari da annabawa da mala’iku da rauhanai da wasu abubuwa da sauransu.
• Tasiri: Gargajiya da al’ada da gaskiya da ƙarya da zamananci da addini da hulɗa da sauransu.
• Masu Yi: Samari, yara da mata, da manya da malamai da ɗalibai da jarumai da bokaye da sauransu.
• Lokacin Yi Da Wuri: Lokacin hirar manya da hirar yara da lokacin shaƙatawa da kiciɓis da wani abu na kawo misalai da lokacin fadanci da sauransu
• Zubi Da Tsari: Kara zube da tarƙoƙo wato ɗaurin gwarmai mai neman ba da amsa ko ra’ayi da gudunmawar tattaunawa
• Jigo Da Warwararsa
• Hikimomin Da Suke Ciki
• Salon Sarrafawa: Mai sauƙi ko mai tsauri ko matsakaici ko mai armashi ko mai ban sha’awa ko maras karashi ko mara daɗi.
• Yanayin maganganun taurari (manya da ƙanana), kamar kwaikwayon abubuwa da maimaita kalmomi da cuɗanya gaskiya da ƙarya da tafi da hankali da bazama cikin mafarki
• Taurari (Manya Da Ƙanana)
• Kammalawa.
Wasan kwaikwayo
Wasan kwaikwayo, wasa ne da ake aiwatar da wata matsala ta rayuwa cikin siffar ‘yaƙini’, wato zahiri ko kuma a rubuta shi. Kafin a yi tunanin fara rubuta wasan kwaikwayo, Hausawa sun kasance masu al’adu da dama waɗanda suka danganci wasan kwaikwayo tun da ai da ma wasan kwaikwayo daɗaɗɗiyar al’ada ce a cikin rayuwar Hausawa.
Waɗannan al’adu kuwa akwai waɗanda yara ko samari ke kwaikwaya tsakaninsu, akwai kuma waɗanda manya ke gudanarwa. Wannan shi ne wasan kwaikwayo na asali ko na gargajiya. Wasan kwaikwaiyo na gargajiya sun haɗa da:
– Wasan Gauta
– Wasan Taƙƙai
– Wasan Kalankuwa
– Wasan Langa
– Wasan ‘Yar tsana
– Wasan Dokin Kara
– Wasanin Tashe
– Wasan Bori da sauransu
Tarken wasan kwaikwaiyo a gargajiyance
Akwai wasannin gargajiya da ke da nasaba da addinni irin su Bori, Giwa – Sha- Laka, da sauransu. Akwai kuma waɗanda ba su da dangantaka da addini irin su wasan Gauta, wasan Takkai, wasan Kalankuwa da sauransu. Wato a nan za a iya cewa Bahaushe na da tsarin wasan kwaikwayo tun tale-tale, ba koyo shi aka yi daga wajen Girkawa da Turawa ba. Don haka, akwai matakai da aka gindaya wajen yin tarken wasan kwaikwayo na gargajiya kamar haka:
– Masu Aiwatar Da Wasa- A nan akan yi dubi ne da waɗanda suke gudanar da wasan. Kamar yadda aka bayyana a baya, akwai wasanni da da dama da rukunin al’umma mabambanta ke gudanarwa. Akwai wasannin da yara mata da maza ke yi irin su wasan Dokin Kara da wasan ‘Yartsana da kuma waɗanda samari maza ke yi irin wasan Takkai da wanda ‘Yammata ke yi kamar wasan Gauta da sauransu. Haka zalika akwai wasanni masu nasaba da addini da mata zalla ke yi kamar wasan Giwa –Sha- Laka da kuma wanda maza ke yi kamar wasan Bukin Buɗin Daji da sauransu.
– Lokacin Gudanar Da Wasa – Wasanni irin su Gauta da Kalankuwa suna da lokaci keɓantacce da ake gudanar da su. Wato an fi yin su da lokacin kaka yayin da amfanin gona ya isa gida. A yayin da wasu ba su da wani
lokaci da aka keɓe don yin su. Akan shirya ne a aiwatar idan da buƙatar haka.
– Wuri– Nazarin wurin da ake gudanar da wasan kwaikwayo na gargajiya yana da matuƙar muhimmanci yayin tarke. Wasanni da dama suna da wurare da ake yin su. Misali wasan Gauta ɗaya ne daga cikin wasannin da akan shirya shi a wuri na musamman wato a fada. Mata kuyangi ke yin shiga irin ta sarki da fadawansa suna kwaikwayon yadda ake gudanar da mulki ta yadda zai yi nuni da adalci ko zalunci da nufin sarki da fadawansa su gyara.
– Zubi Da Tsarin Wasa- A wannan ƙaulin akan dubi abubuwa kamar yadda aka shirya wasa da kuma abubuwan da aka yi amfani da su yayin tsara wannan wasan kwaikwayo. Misali a wasan Dokin Kara, da yara maza ke shiryawa domin kwaikwayon yadda sarki da hakimai ke gudanar da rangadi a lokacin bukukuwan hawan sallah. Yaran sukan sami kara su lanƙwasa shi ta yadda zai ba da siffar doki, sa’annan a yi masa kwalliya da ƙyallaye. Daga nan yara kan yi amfani da galura (kala) da suka jiƙa a ruwa don shafa wa dokin karan. Ta haka za su yi shiga irin na sarki da hakimai suna kwaikwayon yadda ake rangadi a yayin bikin sallah.
– Kayayyakin ‘Yan Wasa- Akan yi sharhi game da shiga da kayayyakin ‘yan wasa don bambanta tsakanin wasanin. Misali wasan Giwa-Sha-Laka wanda yake galibi mata ne ke aiwatarwa, sukan yi shiga ta musamman.
Uwar Bori ce ke ba da umurnin kayan da kowace za ta sanya, wato sukan ɗaura baƙin zane na saƙi babu riga, ba ɗan kwali. Bugu da ƙari, sukan yi amfani da taɓo su shafa a jikinsu tare da ɗaure rassa guda biyu a kai daga hagu zuwa dama kamar ƙaho da wani abu kamar haure (haƙori) da suke sakawa a baki. Har ila yau, A wasan Dokin Kara, kayayyakin ‘Yan wasa akasari manyan riguna ne kamar babbar riga da alkyabba da rawani da sauransu.
– Jigon Wasa– A nan akan yi dubi ne da manufar gudanar da wasa. Wasannin kwaikwayon gargajiya na Hausa suna da manufofi mabambanta. Misali, jigon wasan Takkai shi ne gargaɗi ga matasa kan illar aikata ayyukan da ba su dace ba a cikin al’umma.
Kammalawa
Gamsasshen bayani a kan ma’anar adabi da ma’anar tarken adabi sun gabata, haka nan, an yi tsokaci game da ma’anar waƙa da zube da wasan kwaikwayo a mastayinsu na nau’o’in adabin gargajiya. Sannan kuma aka yi bayanin yadda ake tarken nau’o’in adabin Hausa wato waƙa da zube da wasan kwaikwayo a gargajiyance.
Manazarta
Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Vol.4 Vol.1 September, Kano: Department of Nigerian Languages Series V, Bayero University.
Mukhtar, I. (2004). Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai, Kano: Benchmark Publishers Limited
Mustapha, S (2018) Tarken Adabin Hausa A Ƙarni Na 21: Tsakanin Matarkan Gargajiya Da Na Zamani, a cikin Kadaura, Journal of Hausa Multi Disciplinary Studies vol.1 No4 Special Edition. Kaduna: Department of
Nigerian Languages and Linguistics, Kaduna State University.
Yahaya, I da Ɗangambo (1986). Jagoran Nazarin Hausa Don Makarantu Zariya: NNPC.