Skip to content

Tetanus

Cutar Tetanus, cuta ce mai hatsari da ke kama mutum ta hanyar kwayar cuta da ke shiga jiki daga raunuka, musamman idan raunukan suka ci gaba da zama a buɗe ko suka kasance a cikin ƙazanta. Cutar tana da saurin yaɗuwa a cikin jiki ta hanyar jijiyoyi, tana haddasa tsukewar tsoka da kumburin jijiyoyi, wanda zai iya kai wa ga mutuwa idan ba a magance ta da gaggawa ba.

Tetanus cuta ce mai tsananin hatsari da za ta iya kashe mutum cikin ‘yan kwanaki idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba. Sai dai abin farinciki shi ne, ana iya riga-kafin wannan mummunan cuta cikin sauƙi idan aka bi ka’idojin tsafta da yin riga-kafi. Dole ne mutane su kasance masu kula da lafiya ta hanyar tsaftace rauni, yin riga-kafi da wuri, da kuma taimaka wa iyaye su fahimci illar cutar da yadda za a guje mata. Idan aka ɗauki matakan da suka dace, za a iya magance yaɗuwar cutar Tetanus a Najeriya da sauran sassan duniya.

Asalin cutar Tetanus

Tetanus cuta ce da wata kwayar cuta mai suna Clostridium tetani ke haddasawa. Wannan kwayar tana rayuwa ne a wurare kamar a cikin ƙasa, toka, hanji da kashin dabbobi da na mutane, da kuma saman fata da kayan aiki masu tsatsa kamar ƙusa, allura, da wayoyi masu sarkakiya. Waɗannan ƙwayoyin suna da ƙarfin jurewa zafi da sinadarai, kuma za su iya rayuwa tsawon shekaru a cikin yanayi. Idan wannan ƙwayar ta shiga cikin jikin mutum, musamman ta hanyar rauni, za ta fara haifar da wani sinadari mai guba wanda ke haddasa matsalar jijiyoyi da tsokoki a jiki.

Hanyoyin kamuwa da tetanus

Kowa na iya kamuwa da tetanus, amma cutar na da tsanani a tsakanin jarirai da mata masu juna biyu da ba su karbi riga-kafi ba. Idan cutar ta bayyana a lokacin goyon ciki ko cikin makonni shida bayan haihuwa, ana kiran ta tetanus ta uwa. Idan ta bayyana a cikin kwanaki 28 na farkon rayuwar jariri, ana kiran ta tetanus ta jarirai. Mutum na iya kamuwa da Tetanus ta hanyoyi da dama, kamar:

  • Yin rauni daga abu mai kaifi kamar ƙaho, ƙusa, ko ƙarfe mai tsatsa wanda ya ke da ƙazanta.
  • Samun rauni dalilin hadari kamar faɗowa ko ƙonurwa da ba a wanke ko kula da su da wuri ba.
  • Saunin yankan dabbobi da ba a tsabtace ba.
  • Cutar haihuwa (Neonatal tetanus) inda jarirai ke kamuwa da cutar ta hanyar amfani da ababen yanke cibiya masu datti.

Saboda haka, ana iya cewa Tetanus ba cuta ce da ke yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ba, sai dai tana bukatar shiga cikin jiki ta hanyar rauni.

Yawaitar yaɗuwar cutar

Tetanus na daga cikin manyan matsalolin lafiya a ƙasashe masu ƙarancin ci gaba inda riga-kafin bai karbu ba, kuma ana ci gaba da haihuwa a wuraren da ba su da tsafta. Yawancin lokutan tetanus ta jarirai na faruwa ne sakamakon amfani da abubuwan da ba su da tsafta wajen yanke cibiya, ko sanya abubuwa masu ƙazanta a wurin. Haihuwa da ake yi da hannaye masu ƙazanta ko a wurare marasa tsafta na daga cikin manyan haɗura.

tetanus 1 1024x683 1
Cutar tetanus na kama kowa amma ta fi kama yara ƙanana da illata su.

A shekarar 1988, kimanin jarirai 787,000 ne suka mutu sakamakon cutar tetanus, amma zuwa 2018 adadin ya ragu zuwa 25,000, sauƙin kashi 97%. Wannan raguwar na da alaƙa da ƙarfafa shirin riga-kafi a ƙasashe masu fama da cutar. Duk da haka, akwai barazana ga matasa da manya maza masu yin kaciya, musamman inda ba a yi musu riga-kafin ƙarfafa kariya ba.

Alamomin cutar tetanus

Alamomin Tetanus na fara bayyana ne cikin kwanaki 3 zuwa 21 bayan mutum ya samu raunin da ya kai ga shigar kwayar cutar. Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:

  • Tsukewar fuska (lockjaw): Wanda ke hana mutum buɗe baki ko cin abinci.
  • Takurewar wuya da ƙafafu: Jiki tukurewa ya yi wa mutum kamar an ƙara ƙarfi har ya kasa yin motsi.
  • Matsanancin ciwon jiki da kuma kasala da gajiya.
  • Wahalar numfashi da iya kai mutum ga mutuwa idan ba a ɗauki mataki ba.
  • Zazzabi da jin nauyi a jiki.
  • Bugun zuciya da sauri da kuma rawar jiki.

Alamomin kan fara da sauƙi, amma sukan ƙara tsanani cikin ƙanƙanin lokaci.

Illolin cutar tetanus

Idan ba a kula da cutar Tetanus da wuri ba, tana iya haddasa matsaloli masu tsanani kamar haka:

  • Mutuwa: Musamman a yankunan da ba a samun gaggawar kulawar kiwon lafiya.
  • Kasala ta dindindin: Tsokoki da jijiyoyi sukan sauya na dindindin ba sa aiki yadda ya kamata.
  • Doguwar jinya: Ana bukatar kula mai tsanani da amfani da na’urorin taimakon numfashi.
  • Illata kwakwalwa sakamakon matsin lamba ko rashin iskar oxygen.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana, Tetanus na daga cikin cutukan da ke kashe dubban jarirai da manya a kasashe masu tasowa, musamman a Afrika da Asiya.

Tetanus a jikin jarirai

Wannan nau’in Tetanus yana faruwa ne a lokacin haihuwa, inda jariri ke kamuwa da cutar daga cibiyar da ake yankewa da kayan aiki masu datti ko kuma an haihu ne a gurare marasa tsafta. Wannan cutar na daya daga cikin manyan musabbabin mutuwar jarirai a wasu yankuna na Najeriya da Afrika gabaɗaya. Alamomin da ake gani sun hada da:

  • Jariri zai daina sha nono.
  • Tsukewar jiki da fuskarsa.
  • Daina motsi ko rawar jiki da zazzabi.

Samun riga-kafin ga uwa kafin haihuwa na taimakawa ƙwarai wajen hana wannan cutar.

Riga-kafin cutar Tetanus

Rigakafi ita ce hanya mafi inganci wajen hana tetanus. WHO na ba da shawarar mutum ya karɓi allurai 6 na TTCV (alluran da ke ɗauke da tetanus-toxoid): allurai 3 na farko da ƙarin allurai 3. Ana fara riga-kafin tun lokacin da jariri ya kai makonni 6, sannan a maimaita hakan da tazara ta aƙalla makonni 4. Ana ba da ƙarin allurai a shekaru 1–2, 4–7, da 9–15. Cutar Tetanus tana da riga-kafi mai inganci. Ana bayar da riga-kafin Tetanus bisa tsarin riga-kafi kamar haka:

1. Allurar (DTP) ta yara

  • Ana ba da allurar DTP (Diphtheria, Tetanus, Pertussis) sau uku a watanni 6, 10 da 14 na haihuwa.

2. Riga-kafin manya

  • Ana ba wa manya riga-kafin Tetanus duk bayan kowace shekara 10.
  • Masu yawan fuskantar rauni kamar masu aikin gona, masu haƙar ma’adinai, da masu aikin gini su kan buƙaci ƙarin riga-kafin.
  • Mata masu juna biyu na bukatar riga-kafin Tetanus don kare jarirai daga kamuwa da cutar a yayin haihuwa.

3. Riga-kafi bayan rauni

  • Idan mutum ya samu rauni mai hatsari, ana iya ba shi allurar Tetanus toxoid ko tetanus immunoglobulin (TIG) da gaggawa don daƙile kamuwa da cutar.

Maganin cutar tetanus

Bayan kamuwa da cutar, babu wani magani da ke kawar da kwayar cutar gabaɗaya, amma ana iya kula da mara lafiya ta hanyar:

  • Ba da allurar TIG (Tetanus Immune Globulin) domin rage yaɗuwar ƙwayar cutar.
  • Ba da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) kamar metronidazole ko penicillin.
  • Magungunan rage ciwo da narkar da tsoka kamar diazepam.
  • Kulawa ta musamman a asibiti da suka haɗa da taimakon numfashi idan buƙata ta taso.
  • Tsaftace rauni sosai domin hana ƙwayar cutar yin nisa a jiki.

Matakan kariya daga tetanus

  • Yin amfani da kayan aikin kiwon lafiya masu tsafta lokacin yanka rauni ko cibiya a yayin haihuwa.
  • Tsabtace rauni da gaggawa bayan samun raunin.
  • Riga-kafi da tsaftataccen jiki.
  • Kauce wa amfani da kayan yanke cibiya marasa tsafta kamar gashi ko ƙaho ko tsohuwar reza ko aska.
  • Yin haihuwa a cibiyoyin kula da kiwon lafiya maimakon a gida.
  • Wayar da kai a cikin al’umma kan muhimmancin riga-kafin cutar da kuma tsafta.

Tetanus a Najeriya – Matsaloli da Kalubale

A Najeriya, riga-kafin cutar Tetanus yana cikin tsarin riga-kafi na yara (RI – Routine Immunization). Sai dai akwai ƙalubale da dama da ke hana yaɗuwar riga-kafin kamar:

  • Rashin isassun cibiyoyin kula da lafiya a karkara.
  • Ƙarancin wayar da kai a tsakanin iyaye.
  • Rashin isassun ma’aikatan kiwon lafiya da kayan aiki.
  • Ƙin amincewa da riga-kafi a wasu al’ummomi.

Wadannan kalubale na bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, kungiyoyi da hukumomin lafiya da al’umma domin tabbatar da kariya ga yara da mata masu juna biyu.

Ƙoƙarin duniya na kawar da cutar tetanus

A shekarar 1989, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ƙaddamar da shirin kawar da tetanus ta jarirai, da burin ganin babu fiye da ɗaya cikin 1000 na kamuwa da cutar a kowanne yanki. A shekarar 1999, hukumomi irin su WHO, UNICEF da UNFPA suka ƙarfafa wannan shiri tare da ƙaddamar da MNTE Initiative.

A watan Yuli 2023, ƙasashe 11 ne kaɗai suka rage da cutar tetanus ta jarirai, wannan ƙasa yake da burin MNTE. Don tabbatar da wannan nasara, wajibi ne a ci gaba da shirin riga-kafi ga yara da mata masu ciki, haihuwa cikin tsafta, da inganta riga-kafin makarantu.

WHO ta ba da shawara cewa kowa ya karɓi allurai 6 na TTCV don riga-kafin cutar tetanus tun daga shekarun ƙuruciya zuwa girma domin kariya daga tetanus na tsawon rayuwa.

Manazarta

Bhattacharjee, A., & Olsen, K. S. (2023). Global analysis of tetanus incidence and mortality in children under 5 years. International Journal of Infectious Diseases, S1201‑9712(23)00532‑5.

Medscape. (2025). Tetanus: Background, Pathophysiology, Etiology. Medscape

Stevens, D. L., & Aldape, M. J. (2012). Tetanus (Clostridium tetani infection). In StatPearls. NCBI Bookshelf.

World Health Organization. (2024). Tetanus.  WHO

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×