Skip to content

Tumatir

Tumatir shuka ce daga cikin kayan lambu mai gajarta da ganye wacce ke yin ‘ya’ya a shekara-shekara daga cikin shuke-shuke dangin Solanaceae, waɗanda suke girma tare da samar da ‘ya’yan itacen da ake ci. Shukar tumatir a tsaye take da gajeren tushe ko karan da ‘ya’yan itacen ke fitowa a jiki tare da rassa.

Tumatir shi ne tushen sinadaran beta-carotene, lycopene, da bitamin C, dukkanansu antioxidants ne waɗanda ke ba da kariya daga lalacewar ƙwayoyin halitta (cells).

Siffar shukar tumatir

Karan ko gangar jikin shukar tumatir na da wani gashi-gashi mai laushi sannan ganyayyakin jere suke a karkace. Tumatir yana samar da furanni masu launin rawaya, wanda suke girma, kuma yawanci ‘ya’yan itacen a zagaye suke. Suna da fata mai santsi, kuma suna zama jajaye ko launin ruwan hoda ko launin purple ko launin ruwan kasa ko launin lemo ko kuma launin rawaya.

Shukar tumatir na iya girma har tsayin mita 0.7-2 m (ƙafa 2.3-6.6) a matsayin kayan lambu na shekara-shekara, ana girbe shi sau ɗaya kawai. Tumatir ya samo asali ne daga Kudanci da Tsakiyar Amurka, amma yanzu ana shuka shi a duk faɗin duniya. Tumatir na ɗaya daga cikin kayan lambu da ake nomawa a Afirka. Ana shuka shi don amfanin gida a kusan kowane lambu da ke bayan gidaje a faɗin yankin kudu da hamadar sahara.

Tumatir shi ne tushen samuwar bitamin  kuma amfanin gona ga masu ƙaramin karfi da manoma masu matsakaicin jari. Tumatir da ake amfani da shi a matsayin sinadarin ƙara ɗanɗano a cikin abinci koyaushe ana buƙatar shi sosai.

Yanayin da tumatir ke buƙata

Domin samun kyakkywar yabanya mai yawa da kuma inganci, tumatir ya fi son yanayin sanyi, busasshen yanayi marar laima. Duk da haka tumatir na iya fitowa da girma a yanayi daban-daban. Tumatir na iya girma har a arewa mai nisa (kamar yankin Arctic da kuma kudu) a yanayin zafi ƙarƙashin kulawa ta musamman. Yanayin zafi tsakanin digiri 21 da 24 °C shi ne matsakaicin yanayi don girma da bunƙasar tumatir. Tsawon yanayin zafi ƙasa da digiri 12°C na iya haifar da sanyi. Yanayin zafin da ya kai ko ya haura digiri 27 °C yana da mummunan tasiri dangane da girma da tsarin ‘ya’yan tumatir.

Furanni da ƙwayoyin ƙwayaye suna lalacewa lokacin da matsakaicin zafin rana ya kai digiri 38 °C kuma har sama da kwanaki 5 zuwa 10. Tsarin ‘ya’yan tumatir ɗin kuma gabaɗaya yana yin rauni lokacin da zafin dare ya wuce digiri 21 °C kafin da kuma bayan samuwar fure. Lalacewar fure na iya haifar da zafi ko bushewar iska.

Tsayin yini ba ya shafar tumatir, yana iya samar da ‘ya’yan itacen a cikin lokaci mai tsawon sa’o’i 7 zuwa 19. Ana iya shuka tumatir a cikin nau’ikan ƙasa iri-iri, kama daga ƙasa mai yashi zuwa ƙasa mai yumɓu mai yalwar ƙwayoyin sinadarai masu muhimmanci ga girma da haɓakar shuka. Madaidaicin pH na ƙasa shi ne maki 6 zuwa 6.5; yawaitar ko ƙarancin pH na iya haifar da ƙarancin mineral ko kuma sinadarin guba. Ambaliyar ruwa ta tsawon lokaci tana da illa ga girma da ci gaban tumatir.

Tsirowar irin tumatir

Ana iya shuka tumatir kai tsaye ta amfani da iri ko a dasa shi a cikin gonaki, amma wannan hanya tana da tsada saboda ana buƙatar iri mai yawa (kimanin gram 500 zuwa 1000 na tsaba a dukkan hecta ɗaya) kuma ana ƙara yawan makonni huɗu na aikin tsigar ciyawa wanda hakan ke buƙatar biyan kuɗin aiki masu yawa.

Bunƙasa dashen ƙananan shukar tumatir ta musamman a lambu, yana ba manoma damar samun kyakkyawan nau’in iri yayin amfani da ƙarancin iri da kuma tanadin kuɗi ga aikin tsige ciyawa.

Kulawa da shukar tumatir

Tumatir yana da ƙarancin tsarabe-tsarabe, yana karɓar kowane nau’in taki. Akan zuba cokali ɗaya ko uku na dutsen phosphate a kowace ramin shuka. Idan ƙasa tana da ƙarancin ƙwayoyin halitta, yana da kyau a shuka amfanin gona mai inganci kamar, waken soya kafin a yi dashen tumatir.

A guji sanya da takin nitrogen saboda yawan nitrogen yana haifar da kumburin ‘ya’yan tumatir da ruɓewa, da kuma yawaitar ciyayi. Idan nitrogen ya yi yawa a cikin ƙasa yana sa ganye ya yi laushi kuma yana sa shukoki su zama masu sha’awar ƙwari da cututtuka. Matsalar ciyayi na iya zama babba, musamman a wurare masu zafi.

A riƙa tsige ciyayi masu tasowa a kusa da ƙasa kamar yadda zai yiwu tsakanin layuka na tumatir don sarrafa ciyawa a kan amfanin gona na ƙasa. A bar ciyawar da aka tsige a ƙasa don taimakawa wajen hana zaizayar ƙasa da rage zafin ƙasa har ma da kare danshin ƙasa. Ya kamata a ƙara wannan ciyayi ta hanyar cirewa da hannu a cikin layuka da ciyawa suka yi kaka-gida. Don guje wa yaɗuwar cutar mosaic ta taba, masu shan taba ya kamata su wanke hannayensu da sabulu sosai kafin su sarrafa tsiron tumatir.

Tumatir mai nauyin kilogiram ɗaya yana samar da iri tsakanin gram 1 zuwa 4.

Tumatir na buƙatar wadatar ban ruwa a farkon matakan girman shukar da fitowar ‘ya’yan itace da kuma lokacin girman su. Daidaita samar da ruwa ga shukar yana da mahimmanci wajen samun girma na bai-ɗaya. Har ila yau yana rage faruwar ɓarkewar cutar fure, wannan cuta ce ta rashin sinadarin calcium yayin girman ‘ya’yan itace. Ana buƙatar ban ruwa aƙalla sau biyu a mako a cikin busasshen yanayi. Yin ban ruwa ta sigar yayyafi ita ce hanya mafi inganci kuma mara haɗari ta ban ruwa.

Lokacin girbin tumatir

Ana girbe tumatur a lokacin da ya girma koda kore ne. Sannan ana amfani da sinadarin Ethylene a wasu lokuta don saurin girma kafin a tura su kasuwa, amma wannan yana da tasiri ga ingancin tumatir ɗin.

Samar da irin tumatir

  • Domin samun irin tumatir, lokacin girbi sai a ɗauki ‘ya’yan tumatir masu ƙarfi, marasa cututtuka.
  • A wanke ‘ya’yan itacen, don rage haɗarin kamuwa da cuta.
  • A yanka tumatir ɗin biyu a ɗebo irin da cokali ko kuma a matse su a cikin mazubi mai tsafta na roba ko kwano ƙasa kamar tukunya.
  • A bar shi har sai ruwan ‘ya’yan tumatir ɗin ya bushe, ya rage irin kawai.
  • A rufe kwanon da tsumma mai kyau don kiyaye datti da sauran gurɓatattun abubuwa, amma kar a sanya shi cikin iska.
  • A bar irin ya yi kwanaki 1 zuwa 5 (yawanci kwanaki 2 zuwa 3 a wurare masu dumi).

Idan ba za a iya shuka iri nan da nan ba, ya kamata a adana shi a cikin mazubin da ruwa ba zai iya riska ba. A zuba toka a cikin kasan kwandon don kiyaye danshi da kare irin daga sauye-sauye. Lokacin adana irin a cikin tukwane ko kwalabe, ya kamata a rufe murfin sosai don hana lalacewa dalilin ruwa da kamuwa da cuta. A ajiye kwandon iri a wuri mai sanyi marar laima. A riƙa bincika irin akai-akai (akalla mako-mako). Idan an samu wata matsala ya kamata a sake bushe shi. Ana iya adana iri har tsawon shekaru biyu idan an busar da shi da kyau. Tumatir mai nauyin kilogiram ɗaya yana samar da iri tsakanin gram 1 zuwa 4.

Alfanun tumatir ga Las lafiya

Tumatir shi ne tushen sinadaran beta-carotene, lycopene, da bitamin C, dukkanansu antioxidants ne waɗanda ke ba da kariya daga lalacewar ƙwayoyin halitta (cells). Bincike ya nuna cewa sinadaran gina jiki a cikin tumatir  na iya rage haɗarin cututtukan zuciya da nau’in ciwon sukari na 2.

Sau da yawa mutane suna ɗaukar tumatir a matsayin kayan lambu don amfanin abinci mai gina jiki saboda ɗanɗanonsa, sai dai alfanun tumatir ya wuce haka, yana ƙunshe da sinadaran gina jiki. Tumatir yana zuwa a nau’i-nau’in daban-daban. Wasu

• Rage haɗarin cutar kansa

Bincike da yawa sun gano cewa maza masu yawan cin tumatur, musamman dafaffen tumatur, suna da raguwar haɗarin ciwon dajin maraina.
Beta-carotene da lycopene da antioxidants a cikin tumatir, na iya daƙile haɗarin cutar daji. Antioxidants suna hana lalacewar DNA a cikin ƙwayoyin halitta kuma suna sa ƙwayoyin cutar kansar su mutu.

• Inganta lafiyar zuciya

Tumatur na iya rage haɗarin cututtukan zuciya, babban abin da ke haifar da mutuwa ga manya a ƙasar Amurka. Wata bita ta ruwaito cewa yawan shan sinadarin lycopene da kuma wadataccen jini na ya rage haɗarin cututtukan zuciya da kashi 14%. Haka nan hawan jini, ko hauhawar jini, cuta ce mai haɗari ga a cikin cututtukan zuciya. Masana sun bayyana cewa yawan shan tumatur ya haifar da raguwar haɗarin kamuwa da hawan jini da kashi 36%.

• Daƙile ciwon ciki

Rashin isasshen sinadarin fiber na iya haifar da yin bahaya ne mai wahala. Cin tumatir, wanda shi ne tushen fiber marar narkewa na iya taimaka wa masu fama da matsalolin da ke da alaƙa da bahaya.

• Rage haɗarin ciwon sukari na 2

Kusan 15% na manya a ƙasar Amurka suna da ciwon sikari. Wasu shaidu sun nuna cewa sinadarin lycopene na iya daƙile nau’in ciwon sukari na 2 ta hanyar kare ƙwayoyin cuta daga lalacewa da rage kumburi.

• Inganta lafiyar ƙwaƙwalwa

Fiye da manya miliyan shida masu shekaru 65 da haihuwa a ƙasar Amurka suna da cutar Alzheimer (AD), wani nau’in ciwon hauka da ke shafar ɗabi’a, ƙwaƙwalwar ajiya, da tunani. Babu magani ga AD, kuma yanayin yana ƙaruwa bayan lokaci.

Wasu shaidu sun nuna cewa antioxidants a cikin tumatir, irin su lycopene, na iya zama kariya daga AD. Bincike ya gano cewa, raguwar aikin ƙwaƙwalwa a tsakanin mutane masu shekaru 70 da haihuwa da ke yawan shan lycopene yana da ƙaranci idan aka kwatanta da sauran mutane da ba sa sha.

Sinadaran da ke cikin tumatir

Ɗanyen tumatur guda daya yana samar da adadin sinadirai kamar haka:

  • Sinadarin kuzari (Calories): gram 22.5
  • Sinadarin kitse ko maiƙo (fata): gram 0.25
  • Sinadarin sodium: 6.25 milligrams
  • Sinadarin carbohydrates: gram 4.86
  • Sinadarin fiber: gram 1.5
  • Sinadarin ƙara sikari: 0
  • Sinadarin frotin: gram 1.1
A riƙa zuba ɗanyen tumatir a cikin abinci kamar farar shinkafa da gurasar da kwaɗon salad.

Lafiyayyen tumatir mai kyau tushen minerals ne da yawa, wanda suka haɗa da:

Folate

Na taimakawa wajen samar da DNA, samar da jajayen ƙwayoyin jini don hana cutar anemia, kuma yana aiki tare da bitamin B12 da C don narkarwa, amfani, da ƙirƙirar sabbin sunadarai frotin da kuma tantanin halitta (tissue).

Potassium

Na taimakawa wajen samar sunadarai a jiki, narkarwa da kuma amfani da sinadarin carbohydrates, kuma yana daidaita bugun zuciya da ma’aunin pH.

Bitamin C

Yana aiki a matsayin antioxidant, yana inganta warakar ciwo, yana taimaka wa jiki wajen zuƙar sinadarin bronze.

Bitamin K

Wannan bitamin na taimakawa wajen daskarewar jini kuma yana taimakawa wajen samun kasusuwa masu ƙarfi.

Hadarin amfani da tumatir

A tabbatar cewa an wanke ko dafa ɗanyen tumatur kafin a ci. Kamar yadda yake tare da sauran kayan amfanin gona, ɗanyen tumatur na iya samun ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar da cututtukan abinci kamar Listeria da Salmonella. Cutukan abinci sun fi tasiri ga waɗanda:

  • Suka kai shekaru 65 da haihuwa ko 5 da ƙasa
  • Suke da ciki (juna-biyu)
  • Suke da matsalolin kiwon lafiya (misali, ciwon daji, ciwon sukari, da cututtukan hanta da koda)
  • Suke sha magungunan da ke rage ƙarfin jiki don yaƙi da kwayoyin bakteriya da cututtuka
  • Tumatir kuma na iya dagula yanayin da ake ciki kamar gastroesophageal reflux (GERD) da ciwon kai na kullum.

Dabarun cin tumatir

A rika cin tumatur akai-akai ta fuska daban-daban, waɗanda suka haɗa da ɗanye da dafaffe. Don cin gajiyar fa’idojin da za a iya samu a tumatir ga wasu hanyoyin da za a yi amfani da tumatir a cikin abinci:

  • A riƙa zuba ɗanyen tumatir a cikin abinci kamar farar shinkafa da gurasar da kwaɗon salad
  • A riƙa saka tumatir a miya da sauran girke-girke kamar taliya, dafa-duka da sauran su
  • A riƙa shan ruwan tumatir kamar yadda yake
  • Yawancin fa’idojin tumatur suna haifar da samun sinadarin lycopene. Bincike ya gano cewa tumatir a da ake nomawa a gonaki yana ɗauke da sinadarin lycopene mai yawa fiye da wanda ake nomawa a gidajen gonaki. Dafa tumatir shi ma yana ƙara yawan sinadarin lycopene.

Manazarta

Cherlinka, V. (2024, June 14). Growing tomatoes: How to plant, maintain, and harvest. EOS Data Analytics.

Rd, C. S. M. (2024, August 2). 5 Health benefits of tomatoes. Health.

Plants Village (n.d).Tomato | Diseases and Pests, Description, Uses, Propagation. Plant Village

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×