Hawainiya dabba ce, sunanta na kimiyya shi ne Chamaeleonidae. Wani nau’in kadangaru ce wanda aka sani da baiwar canja launukan fata. Akwai nau’ikan hawainiya sama da guda 160 da suka bazu a cikin Madagascar, Spain, Afirka, Asiya, da Portugal. Suna da manyan idanu da dunƙulallun wutsiyoyi. Wasu nau’ikan na iya canja launin fatar jikinsu don sajewa da wajen da suke a matsayin hanyar kariya daga mafarauta. Waɗannan nau’in ƙadangaru na iya canja fatarsu zuwa ruwan hoda ko shuɗi ko ja ko launin lemo ko kore ko baƙi ko launin ƙasa ko shuɗi mai haske ko rawaya, da sauran su.
Hawainiya na iya gani har nisan ƙafa 32 a gabansu. Wannan yana sauƙaƙa musu gano gyare da dodon koɗi da sauran nau’ikan abin da suke kalaci da shi. Suna da ƙarfin hangen nesa na tsawon digiri 360 a jikinsu. Wannan baiwa ta musamman tana ba su damar farautar abinci da gano mafarauta sosai. Sai dai hawainiya na da kyakkyawan tsarin gani, amma ba ta iya ji sosai. Kamar maciji, tana iya jin sauti a wasu mitoci amma ta fi dogara da ganin ido don kama ƙwari.
Siffofin da yanayin hawainiya
Hawainiya dabba ce mai ban mamaki tare da ƙwarewa ta musamman wajen canja launinta da sajewa cikin yanayi. Tana da yawa siffofi da girma da launuka dangane da nau’ikanta. Yawancin hawainiya suna da baƙaƙen jiki da dogayen wutsiyoyi masu ɓangarori biyar a kan kowace ƙafa waɗanda aka daidaita don kama rassan bishiya ko wasu ɓangarori. Idanunsu ɗaya na iya motsawa ba tare da ɗayan ba, wanda ke taimaka musu wajen bincika abubuwan da ke kewaye da su. Hawainiya suna da harshe wanda suke amfani da shi wajen kama abin farauta kamar ƙwari ko ƙananan ƙadangaru. A tsaka-tsakinsu, suna da girma daga inci 2 har zuwa inci 24 a tsayi. Game da nau’ikansu, yawanci suna nuna launuka masu haske na kore da rawaya tare da alamomi iri-iri a ko’ina cikin jikinsu.
Muhallin hawainiya
Hawainiya dabbobi ne da ake samu a cikin daji da kuma yankin hamada iri ɗaya, a Afrika, Asiya, da wasu sassan kudancin Turai, da kuma wasu tsibiran da ke Tekun Indiya. Da can kuma hawainiya ta bayyana a wasu sassan Arewacin Amurka. Yawancin waɗannan dabbobi masu siffar ƙadangaru suna rayuwa ne a cikin bishiyoyi ko a cikin kurmi. Wasu ‘yan nau’ikan hawainiya ne kawai ke rayuwa a doron ƙasa ƙarƙashin tarin ganyayyaki. Ta wanzu kusan miliyoyin shekaru kuma an yi imanin cewa ta fito ne daga dangin iguanid.
Mahara da mafarauta
Akwai dabbobi da yawa da suke cin waɗannan nau’in halittu. Wasu daga cikin dabbobi da ke cin hawainiya sun haɗa da macizai, tsuntsaye, a wani lokacin kuma har birai.
Dabarun kariya daga mafarauta
Ƙarfin hawainiya wajen canja launi da dacewa da yanayinta shi ne hanyar kare kanta lokacin da mafarauci yake kusantar ta. Idan hawainiya tana kan reshe, fatarta na iya juyawa zuwa launin da ke kusa da launin reshen. Mafarauta da yawa na iya wucewa ba tare da ganin hawainiyar a zaune a nutse a kan reshen bishiyar ba.
Tsarin halittar hawainiya
Tsarin halittar hawainiya ya ba ta damar haɗa halaye masu ban sha’awa da yawa waɗanda suka sa ta dace da wurin zama na musamman. Tana da idanu na musamman da hangen nesa mai nisan digiri 360 wanda ke ba ta damar ganin mafarauta daga kowace hanya, tana da dogayen harsuna da suke taimaka mata ta iya kama abin farauta da sauri, wutsiyarta mai tsayi wadda ke taimaka mata hawan bishiyu cikin sauƙi, da farata waɗanda ke ba ta damar kama rassan da ƙarfi. Bugu da ƙari, launin fatar jikinta yana ba ta damar sajewa da wajen da take, a daidai lokacin da mafarauci ko wasu dabbobi suka yi mata barazana.
Halayen wahainiya
Sanannen hali mai ban mamaki game da hawainiya shi ne iya canja launi, amma kuma tana da wasu halaye masu ban sha’awa. Hawainiya halitta ce mai jure zaman kaɗaici, tana ƙarar da mafi yawan lokutanta ita kaɗai ko kuma su bibiyu. Ana iya ganin su sau da yawa suna yin barcin rana a kan rassa ko ganye, kuma idan aka takura musu za su yi faɗawa cikin ganyen. Dogayen harsunansu na taimaka musu wajen kama abin farauta kamar ƙwari da ƙananan dabbobi masu rarrafe; suna da ƙarfin hangen abubuwa daga nesa wanda ke taimaka musu su gano hanyoyin samun abinci daga nesa. Lokacin da mafarauta suka yi musu barazana, hawainiya na iya kumbura kansu har su yi girma fiye da na yadda suke kuma su ba da sautin hayaniya a matsayin alamar mayar da martani. Baya ga wannan hali na kariya, wasu nau’in hawainiya na iya yin faɗa da juna ta hanyar amfani da wutsiya.
Hawainiya dabbobi ne masu mu’amala da juna ta hanyar amfani da harshen jikinsu. Misali, hawainiya da ke ƙoƙarin kare muhallinsu daga masu kutse suna iya juyawa ta gefe. Wannan yana sa su fi girma da kuma firgitarwa. Hawainiya da ke jin barazana na iya buɗe baki don ƙoƙarin tsoratar da wani.
Tsarin haihuwar hawainiya
Yawancin nau’in waɗannan kadangaru suna yin ƙwai, yayin da wasu kaɗan ke da tsarin haihuwa. Macen wahainiya tana tona rami a cikin ƙasa ta sa ƙwayayenta a ciki don su ji dumi. Yawancin lokaci, suna yin ƙwai kusan guda 20, amma yana iya zama fiye ko ƙasa da haka dangane da nau’inkan wahainiyar. Tana iya ɗaukar watanni huɗu zuwa shekara kafin ƙwan ya fito. Hawainiyar Jackson misali ne na jinsin da ke ɗaukar ciki da haihuwa. Wannan nau’i na iya haifar jarirai daga 8 zuwa 30 bayan sun dauki ciki na kusan watanni shida.
Hawainiya, kamar sauran dabbobi masu rarrafe, suna haifuwa ta hanyar jima’i. A lokacin da suka yi nufin neman haihuwa, mazajen hawainiya za su nuna launuka masu haske don jawo hankalin abokan matan. Hakazalika mazajen hawainiya suna amfani kansu a matsayin hanyar yin kwarkwasa da fafatawa da abokan hamayya domin jan hankalin mata. Idan namiji ya yi nasara wajen nuna launukansa, mace za ta iya zaɓar shi don ƙulla alaƙar aure.
Lokacin ɗaukar ciki na ƙwan hawainiya na iya faruwa a kodayaushe daga wata ɗaya zuwa watanni da yawa dangane da nau’in halitta da yanayin muhalli kamar yanayin zafi. Bayan saka ƙwayayen da aka shimfiɗa a ƙarƙashin ƙasa ko a cikin bishiyoyi, ana ƙyanƙyasar ‘ya’yan hawainiya ba tare da kulawar iyaye ba, don haka dole ne su taimaki kansu bayan ƙyanƙyasa.
Tsawon rayuwar hawainiya ya dogara da nau’ikansu, amma gabaɗaya suna farawa daga shekaru biyar zuwa goma sha biyar idan aka tsare su a ingantaccen yanayi kamar cin abinci mai kyau da kula da muhalli akai-akai. Hawainiya da ke rayuwa a cikin daji suna da ɗan gajeren lokacin rayuwa saboda rashin samun abinci, kamuwa da cututtuka da sauransu, wanda zai iya rage tsawon rayuwarsu idan ba a magance su yadda ya kamata ba.
Abincin hawainiya
Hawainiya na cin abinci iri-iri, kamar ‘ya’yan itace, kwari, da tsirrai. Wasu nau’in hawainiya suna cin nama, wasu kuma sun fi son cin ganyayyaki. Dukkan nau’o’in hawainiya za su iya cin duk abin da ya haɗa da berries, ganye, ‘ya’yan itatuwa, kwari, tsutsotsi, dodon koɗi. Wasu manyan nau’ikan hawainiya kuma suna farautar ƙananan dabbobi masu rarrafe. Hawainiyar da ke cin ƙwari tana amfani da dogon harshe don kama fara, ciyayi da dodon koɗi. Tun da yawancin hawainiya suna tafiya a hankali, dogon harshensu na iya samun abin da za su ci. Da zarar ƙwaron ya shiga cikin bakin hawainiya, sai muƙamuƙai su taune shi. Wasu manyan nau’ikan hawainiya sukan ci ƙananan tsuntsaye.
Hawainiya ba ta shan ruwa mai yawa amma tana buƙatar samun shi akai-akai. Hawainiya da ke rayuwa a cikin dajin tana shan ɗigon ruwa daga ganyen bishiya bayan ruwan sama ya ɗauke. Yawancin hawainiya suna neman ruwa mai ɗigowa maimakon na tafki a cikin dajin.
Manazarta
Vitt, L. (2025, January 16). Chameleon | Description, Camouflage, & Facts. Encyclopedia Britannica.
Yum! – Chameleons Snatch Bugs. (n.d.). Animals.
Vedantu. (n.d.-a). Facts about Chameleon. VEDANTU.