Wakokin baka kamar yadda sunansu ya nuna, su ne wakokin da aka yi da baki, abin nufi a nan shi ne, su dai wakokin baka shirya su ake yi a zuci, kuma a gabatar wa mutane da su ta hanyar rera su da baki. Tun ainihinsu ba a rubuce suke ba, kuma mawakan da suke tsara su, ba a rubuce suke tsara su ba, sun ɓullo da su ne ta hanyar rerawa da baki, wani lokaci tare da kida, wani lokaci kuma babu.
Wakokin baka sun kunshi wakokin mata na aikace-aikacen cikin gida da wakokin yara na dandali da wakokin cikin tatsuniyoyi da kuma wakokin makada da mawakan Hausa na gargajiya. Wakar baka wani sako ne cikin zance da azanci da ake rerawa ba fada kurum ba, ta hikima da fasaha da zaɓaɓɓub kalmomi waɗanda suka dace da sakon, kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa da sautin murya da kida da armashi da gaɗa da tafi mai saka zuciya jin daɗi.
Gusau, (1983) ya ce “Wakokin baka na Hausa sun shiga ko’ina a dukkan bangarorin rayuwar Bahaushe. Wakar baka takan yi ruwa ta yi tsaki a duk inda ta ga Bahaushe ya jefa kafarsa. Kasancewar wakokin baka suna da wannan halayya ta ratsa kowane zango na rayuwar Hausawa ya sa suka zama suna tafiya daidai da rayuwar yara ƙanana da matasa da kuma manyan mutane, maza ko mata.
Rabe-raben waƙoƙin baka
Za a iya karkasa waƙoƙin baka na Hausa zuwa gida-gida kamar haka:
Waƙoƙin baka na yara
Wannan nau’i na wakoki ya kunshi sassan wake-wake da yawa wadanda yara ‘yan maza da ‘yan mata suke gudanarwa da suka hada da wakokin wasannin dandali da wasannin tashe da wasan kwaikwayo da bikin aure da sallar takuutaha da rokon ruwa da sauransu. Ga wasu misalansu:
Wakokin yara maza
Wakokin yara maza su ne wadanda suke shiryawa a lokacin da suke wasansu na dandali. Irin wadannan wakoki akan sami jagora mai bayarwa, sauran yara kuwa suna karbawa, kamar a wakar sha burburwa:
Bayarwa: Shaburburwa,
Amshi: Sha.
- Bayarwa: Kowa ya bace,
Amshi: Sha. - Bayarwa: A sha shi da kulki,
Amshi: Sha. - Bayarwa: Kulkin kira,
Amshi: Sha. - Bayarwa: Ba na aro ba,
Amshi: Sha. - Bayarwa: Ku ba shi gidanai,
Amshi: Sha. - Bayarwa: Har ya kawo,
Amshi: Sha.
Wakokin ‘yan mata
Wakokin ‘yanmata su ma nau’i-nau’i ne kuma su ne ake kira wakokin gada ko na bojo. Su ma ‘yan mata suna gudanar da wasanninsu ne a dandali ko a wasu wurare na musamman kamar a wajen bikin aure ko bikin sallar takutaha ko lokacin rokon ruwa ko tashe a watan azumi da sauransu. Misalan wadannan wakoki akwai kamar haka:
• Wakar Talle
- Bayarwa: Amshi:
- Maina ya kone, talle
- Ba da talle ba, talle
- Jirkita mani, talle
- In ciwo kashi. talle
• Wakar Sabara
- Bayarwa: Amshi:
- Na tai tsarince, Sabara
- Magarya tai mani jar tsikara, Sabara
- lye, lye, lye Sabara
- Magarya ba haka nan akan yi ba, Sabara
- lye, iye, iye, Sabara
- ‘Yar bakin gulbi, Sabara
- Ta yi liya-liya, Sabara
- Ku yayyafa mata ruwa, Sabara
- Shaf, shaf, shaf, Sabara
- Ka dauko naka ka tura daka, Sabara
- Ka dauko dan wani kai ta damfara Sabara
Wakokin baka na manyan mata
Wakokin baka na manyan mata su ne wakokin da yawanci mata suke yin su a lokacin da suke aiwatar da wasu ayyukan gida. Manyan mata suna yin wakoki a lokacin daka ko raino ko dabe ko nika ko wanke-wanke da sauran lokuta na gudanar da wasu hidimominsu na yau da Kullum.
Wakokin daka
Wakokin daka su ne wakoki wadanda mata suke yi lokacin da suke daka inda za su dinga gwama tabarya da turmi, sai su ba da sautin da ake kira lugude ko mama. Misaim wakar daka ita ce:
- Ana lugude ana mama,
- Cikin shigifa cikin soro,
- Mama ba habaici ce ba,
- Salon daka a haka nan,
- Ga macen da ba a so ta haihu,
- Ta haifi kwandamin da namiji,
- Shugaban daka shi ka daka,
- ‘Yan tanyo kissa su kai,
- Sukus-sukus sai su aje,
- Gidan Marafa kaji ka daka,
- Tarmani na izon wuta,
- Angula na kirba dawo.
Wakokin reno
Wakokin reno su ne wadanda mata suke yi a lokacin da suke rainon yara suna yi musu tawai don su yi shiru su bar kuka a kwantar da hankalinsu a sanyaya musu rai. A cikin wakokin akan fadi nasabar yaro da ayyukan da ake yi a gidansu da yabon masoya da zambo da habaci ga magabta in akwai su. Ga misali:
- Yi shiru bar kuka,
- Ku taho ku gane shi,
- Ku yo ziyara,
- Dan yaro sai dai a bi ka.
Wakokin dabe
Wakokin dabe su ne wakokin da manyan mata suke yi a lokacin da suke aikin dabe Yawanci wakokin dabe sukan kunshi bege da zambo da habaice-habaice da kalmomin batsa da na zage-zage da sauransu. Ga misali:
- Ina Lumu shege,
- Mai malmala ga munta,
- Kare bakin bahwade,
- Ya hana mu walawa.
Wakokin nika
Wakokin nika su ne wakoki wadanda mata suke yi lokacin da suke nikan tsaba a kan dutsen nika na gargajiya. Wakokin sun kunshi begen miji ko wani masoyi ko habaici ga kishiyoyi ko uwar miji ko ta hanyar shagube ko ambaton juyayin nakuda da dai sauransu. Ga misali daga wakar nakuda:
- Wayyo nakuda ta tashi,
- Ciwon nakuda ya tashi,
- Kuma ciwon nakuda ya motsa,
- Yau kam babu zama zaure,
- Wayyo inna ki cece ni,
- Da kis sha dadinka,
- Shin wai ke tuna inna ta cece ki?
- Ko ko Ke tuna da baba ya cece ki?
- Wayyo nakuda ‘yar ziza,
- Ciwon nakuda hon ne,
- Ko ko nakuda hauka cc?
Wakokin talla
Wakokin talla su ne wakoki wadanda ake yin su a lokacin da ake tallan wani abu. A cikinsu akan zuga sana’ar da ake tallar tare da fito da kwarjiinta ko amfaninta. Misali:
- Ku sai dawon geroda barkono,
- Furata da ‘yan yaji rankandam,
- Sai da nid daka nib burke,
- Had da gudajin nono.
Wakokin baka na cikin labarai da tatsuniyoyi
Gusau, (1980) ya ce haka kuma akwai wasu ‘yan wake –wake da ake sakawa a cikin labarai ko tatsuniyoyi don kara musu armashi ko jawo hankali da tunanin mai sauraro. Ga wani misali daga tatsuniyar Madaci da Yarinya:
- Yaninya: Madaci, Madacci ubana,
Gare ka anka ban ni,
Gare ka za ni tsira. - Madaci: Ishunki, ishunki diyata,
Gare ni anka bak ki,
Gare ni za ki tsira,
Mutum dari da goma,
Manzo dai kan kai gida.
Wakokin baka mai tafiya da kade-kade
Gusau, (1980) ya ce “Wakokin baka masu tafiya da kade-kade wakoki ne wadanda makadan baka suke shiryawa. Wakokin makadan baka sun karkasu dangane da ire-iren makadan da ke aiwatar da su, ko ta hanyar kayan kidan da ake amfani da su ko kuma ta yanay-yanayen wadanda ake yi wa su. Wakokin baka masu tafiya da kade-kade sun hada da:
Wakokin jama’a
Wakokin jama’a su ne wakoki wadanda ake yi wa attajirai da ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a. Makadan da ke yin wakokin jama’a suna da yawan gaske, sunayen wasu daga cikinsu sun hada da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Abdu Karen Gusau da Mammalo Shata da Garba Supa da Shehu Ajilo da Sabo Saya-Saya da Musa Danba’u da Aliyu Gadanga da Haruna Uji da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu.
Wakokin maza
Wakokin maza, wakoki ne da ake yi wa wasu rukunin jama’a da suka hada da ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan kokawa, da ‘yan baura da sauransu. Daga cikin makadan wannan sashe akwai Kassu Zurmi da Muhammadu Bawa Dan’anace da Isa Danmakaho da Illon Kalgo da Muhammadu Gambu da makamantansu.
Wakokin sana’a
Wakokin sana’a, wakoki ne wadanda ake yi wa masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da mahauta (runji) da manoma da masunta da makera da majema da masaka da sauransu. Yawancin makada na rukunin wakokin maza su ne suke shirya wakoki na rukunin wakokin sana’a kamar Dan’anace.
Wakokin fada
Wakokin fada wakoki ne wadanda ake shirya wa sarakuna da sarautunsu na gargajiya. Wasu daga cikin fitattun makadan fada sun hada da Ibrahim Gurso da Ibrahim Narambada da Salihu Jankidi da Abubakar Akwara da Buda Dantanoma da Muhammadu Dodo Maitabshi da Musa Dankwairo da Abdu Inka Bakura da Aliyu Dandawo da Sani Dandawo da sauransu.
Wakokin ban dariya
Wakokin ban dariya, wakoki ne wadanda ake aiwatarwa domin nishadantarwa da yi wa rai yayyafi. Daga cikin makadan ban dariya akwai ‘yan kama da ‘yan gambara da ‘yan galura da sauransu.
Wakokin sha’awa
Wakokin sha’awa su ne wakokin da ake shirya wa abubuwan da suka ba mutum sha’awa ko suka kayatar da shi. Da wuya a ware makadi daya daga cikin makadan Hausa a ce wakokin sha’awa kawai yake shiryawa, amma akwai wasu makadan da suke tsarma ire-iren wadannan wakoki jefi-jefi a cikin wakokinsu kamar Haruna Uji da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu.
A dunkule, wakokin baka na Hausa suna nan jibge kuma sun ratsa dukkan sassan rayuwar Hausawa ta fuskar zamantakewa da siyasar zama ko tattalin arziki ko addini ko ta hanyar al’adu ko wasanni da sauransu.
Wannan makala babu shakka ta fayyace muhimman abubuwa da suka haɗa ma’anar waƙa da ire-iren waƙoƙin baka da misalan wakokin baka iri-iri.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.