Skip to content

Wanzanci

Wanzanci na daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa. Sana’a ce da ake yin ta ta hanyar amfani da aska da kuma wasu kayan aiki. Sana’ar wanzanci tana da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa. Wanzami a zamanin baya yana da matsayi iri ɗaya ne da na likita a wannan zamani da muke ciki. Ke nan ana iya cewa a da, wanzami shi ke ba da maganin cututtuka. Wanzami shi ke yin aski, zane, kaciya, da sauransu. Baya ga sana’ar aski, wanzami kan gudanar da wasu ayyuka da suka shafi kawar da cututtuka ko dai ta hanyar bayar da magani kai tsaye, ko kuma ta hanyar tsaga jikin mutum kamar cire agalawa, ɓalli-ɓalli, ƙaho da sauransu. Sana’ar wanzanci tana da sarki da ake yiwa laƙabi da Sarkin Aska. A cikin rukunin masu sana’o’in Hausa, babu wanda ya fi wanzami kusa da jama’a.

wasu daga cikin kayan aikin wanzamci
Wasu daga cikin kayan aikin wanzamci.

Kayan aikin wanzanci

  • Zabira: ita ce jakar wanzamai, a cikinta suke zuba dukkan kayayyakin aikinsu in banda ƙoƙo, da jallon ruwa.
  • Dogari ko mataki: shi kuma ice ne da ake sassaƙe shi. Ana amfani da shi wajen danne harshe idan za a cire hakin wuya (haƙin wuya wani nama ne da yake tsirowa a jikin ganɗa, sannan kuma yana susar hanƙa. Wannan yakan saka mutum ya ji kamar zai yi amai).
  • Ƙoshiya: Aska ce mai lanƙwasa wacce ake yiwa ƙota da itace sannan kuma a rufe ƙotar da fata. Da wannan aska ake cire hakin wuya.
  • ‘Yartsaga: Aska ce ‘yar ƙarama da ake amfani da ita wajen yin tsaga kamar tsagar ƙaho, ɓalli-ɓalli, tsagar fuska, tsaga ƙurji da sauransu.
  • Aska: Aska wuƙa ce ta wanzamai, da ita ake aski, gyaran fuska, kaciya, da sauran ayyukan wanzamai masu yawa.
  • Auduga: Ana kuma kiran auduga da sunan kaɗa a Hausa. Amfanin auduga a wajen wanzamai shi ne share jini. Wato da ita wanzamai ke amfani wajen share jini idan sun yi tsaga ko wani aikin wanzamai da kan haddasa fitar jini.
  • Mawashi: Kala biyu ne, akwai na dutse akwai kuma na fata. Shi na dutse irin ƙananan duwatsun nan ne masu kyau da siffa ta musamman da ake samu yawanci a cikin kogi ko kuma gidin dutse. Na fatar kuwa fatar tsakiyar gadon bayan akuya ce ake yanke ta a jeme ta ana amfani da ita wajen wasa aska.
  • Isga: Jelar saniya ce ake yi mata ƙota da ice, sannan kuma dukawa su yi mata rufi da fata.
  • Sabulu: Ana amfani da shi wajen shasshafawa a suma idan za a yiwa
    mutum aski ko gyaran fuska. Babban amfaninsa shi ne yakan saka sumar ta yi laushi, sannan kuma zafin askin ya ragu.
  • Ƙoƙo: A cikinsa ake zuba sabulun da kuma ruwa kaɗan a samansa.
    Jallo: Buta ce ta duma (ƙwarya), a cikinta wanzamai ke ɗura ruwan aski.
  • Matsefata: Ana amfani da ita wajen cire sartse.
  • Ƙaho: Ƙaho ne na Saniya da ake fiƙe shi a yi masa ƙofa a tsakiya.

Yadda ake yi wa mutum ƙaho

Da farko za a ɗora wannan ƙaho a jikin mutum sai a riƙe shi da hannu, sannan kuma a riƙa zuƙo iska ta wannan ƙofa. Idan wanna ƙaho ya kai matakin da ya kama jikin mutum, to sai toshe ƙofar da hannu sannan a kawo danƙo a liƙe ƙofar (wannan danƙo kuma daga jikin bishiyar gamji ake samo shi). Can kuma bayan wani ɗan lokaci da ake ganin jinin ya taru a wannan guri da aka kafa wannan ƙaho, sai a cire ƙahon, sannan a ɗauko aska a tsattsaga gurin. Bayan an tsattsaga gurin sai kuma a sake mayar da wannan ƙahon, sannan a sake zuƙo shi, a wannan karon jinin nan da ya taru shi ne zai fara fitowa. Idan ya sake kama jikin mutum to sai a sake barinsa na wani lokaci. Can sai a zo a cire shi a zubar da jini da ya taru a ciki. Sannan a sake kafa shi a sake zuƙa. Da haka-da haka sai wannan jini ya fice baki ɗaya. Sannan sai kuma a kawo auduga a ɗan gogge jinin da yake jikin mutum ɗin. Sai kuma a kawo garin magani a ɗan barbaɗa a kan wannan tsaga.

  • Amfanin Ƙaho: Ana amfani da shi wajen cire mataccen jini ko ciwon sanyi daga jikin mutum.

Ayyukan Wanzamai

  • Aski
  • Tsaga
  • Ƙaho
  • Kaciya
  • Cire Sartse
  • Cire Belu
  • Cire Angurya
  • Bayar da magani da sauransu

Bayar da magani

Yana da matukar mahimmanci kafin a fara bayyana ire-iren magungunan gargajiya waɗanda wanzamai suke bayarwa a yi takaicecciyar bita a kan sana’ar wanzanci. A hausance, sana’ar wanzanci tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da koshiya don cire belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba don kuwa ana amfani da yar tsaga don yin kaho da kuma cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’ar wanzanci dai ana yin hujin kunne da yanke yatsan cindo da yanki linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci suna bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda ke bukata.

Daga cikin magungunan da wanzamai kan bayar akwai na yara akwai na manya. A rukuni na farko da ya shafi yara ƙanana da jarirai sun haɗa da maganin tanadin jarirai da ciwon sanyin ciki da ciwon saifa da ciwon kai da ciwon ƙazamin goyo da ciwon damsai da na tamalmala da cibiya da sauransu. Haka sukan bayar da magungunan manya maza da mata da suka shafi ciwon jiri ko na zucciya da haori da kunne da amosanin ƙashi da maƙero da sauransu.

A takaice a iya cewa sanar’ar wanzanci ta tabo aikin likita a ƙasar Hausa kafin zuwan likitan zamani. Dalili kuwa shi ne wani daga cikin ayyukan wanzanci shi ne kula da lafiya musamman ta jarirai da kanann yara, ta wani fannin ma harda lafiyar manya. Masu yin ire-iren waɗannan ayyuka ana kirarsu wanzamai waɗanda dole su suka san cikakkiyar lafiya. Masu
hankali da natsuwa makaho ko wanda ba ya gani sosai, ko mai hannu daya, ko kuturu, ko mahaukaci, ba sa iya yin ayyukan wanzanci don tsoron kar a fiskanci matsalar da za ta iya cutar wa waɗanda za a yi wa ayyukan.

A mafi yawaici maza ne suke yin sana’ar wanzanci, amma ana samun wasu mata waɗanda saboda rashin wani namiji a gidan, ko kuma don wani dalilin su kan koyi wannan sana’ar daga mahaifansu. Ana gadon wannan sana’ar a wajen iyaye ko kakani na wajen uba. A gargajiyance yana da matukar wuya a sami wani mutum wanda bai gaji wannan sana’a ba yana yi dukkan ayyukan wanzanci. A wannan zamani ana samun waɗanda kan koyi aski na saisaye wanda suke yi da kayan askin zamani, amma iyakar su aski don kuwa ba sa iya yin saurar ayyukan wanzanci.Haka kuwa a wajen yin ayyukan wannan sana’a, gado na taka muhimmiyar rawa, don kuwa kowane wanzami yana da gidajen da yake zuwa don gudanar da ayyukansa.

Wani wanzami daban ba ya zuwan gidan da wani wanzami dan uwansa ke yin aiki ya yi. Kowane gida ko zuri’a suna da wanzamin da suka gada wanda yake yi musu aiki, daga shi sai yayansa ko wani daga da ya wakilta ne kadai suke iya zuwa waɗannan gidajen nasa don yin waɗannan ayyuka. Haka suma masu gidajen ba sa kiran wani wanzami daban don yin ayyukan wanzanci a gidajensu sai dole sai wanda suka gada daga iyayensu.

Wani tsari mai ban sha’awa dangane da aiwatar da sana’ar wanzanci shi ne, wanzami ba shi da iyakar ƙasa da zai rinka gudanar da aikin sa. Yana iya fita daga garinsu ko ƙasar dagacinsu ko hakiminsu ko dagacinsu ko sarkinsu, kai wannan zamani har jaharsu ya tafi wuraren da mutanensa suke domin yi masu ayyukan wanzanci. Misali, idan Bahaushe ya auri Bafulatana wanda ita a al’adar su mace ba ta haihuwar fari a gidan mijinta, sai dai ta tafi goyon ciki gidan mahaifanta. To, Idan ta haihu ba mahaifanta ba ne za su kira wanzami ba mijinta ko mahifansa ne za su kira wanzami na gidan su don ya yi ayyukan. Haka kuma, a wannan zamini idan mutum yana aikin gwamnati a wani gari, idan matarsa ta haihu sai ya aiko garinsu don wanzaminsu na gida ya je domin ya yi ayyuka.

Awani lokaci ta kan kama a sauya wanzamin da aka gada. Dalilan da kan sa a yi wannan sauyi sun haɗa da sauyin wurin zama. Wato idan mai gida ya tashi daga garinsu ya koma wani gari da yake nisa da garinsu na asali, to a sabon wurin da ya sauka idan aka yi masa haihuwa, kuma yana bukatar a yi wa yaronsa kaciya, ko dai wata bukata ta aikin wanzanci a gidansa, sai ya nemo wani wanzami don ya yi masa waɗannan ayyuka.

Daga wanna lokaci shi wannan wanzami ya zama na gidansa sai kuwa idan wani dalili ya tilasta a sauya shi. Haka kuma idan wanzamin gidan ya rasu ko wata lalura ta rashin lafiya ta same shi, idan ba shi da mai gadon sa sai waɗanda yake yiwa aiki su sami wani wanda zai maye gurbin sa. Shi ma daga nan ya zama wanzamin wannan gida.

Idan kuma rashin fahimtar juna ko wani saɓani ya shiga tsakanin wanzamin gida da mai gidan da ya ke yi wa aiki, a nan ana iya sauya wannan wanzami. Idan ba ta waɗannan hanyoyi ko makamantansu ba, matukar wani wanzami ya yi shishshigi ya shiga gidajen da wani wanzami yake yin aiki ba tare da izininsa ba, matsala na iya shiga. Domin kuwa kowannen su zai yi ta ƙoƙarin yin ire-iren surkulle da sihirince-sihirincen da ya iya domin nakasar da abokin hamayyansa ko ya lalata ayyukan da ya yi. Wanzaman Hausawa sun kasu zuwa kashi biyu:

  • Waanzaman gado
  • Wanzaman ƙoƙo.

Wanzaman gado su ne waɗanda suka gaji yin sana’ar wanzanci a wajen iyayensu da kakaninsu, kuma suna yin dukkan ayyukan wanzanci waɗanda suka hada da yin aski da kaciya da cire belun wuya da cire angurya da bayar da magungunan gargajiya da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya.

Ire-iren waɗannan wanzamai ne suke gadon gidajen da za su rika yin ayyukan wanzanci. Haka kuma, daga cikin irinsu ne ake nada sarkin aska ko magajin aska. Idan bukatar aikinsu ta tashi mafi yawanci lokacin a gidajensu ake zuwa ake sanar da su lokaci da wuraren da za su je su yi ayyukan su ta wanzanci. Kuma a mafi yawancin lokaci ire-iren waɗannan
wanzamai ba su da rainuwa domin kuwa duk abin da aka ba su a matsayin ladar aikinsu, sai su karba suna yin murna da godiya. An bayyana cewa, dalilin haka shi ne, suna yin waɗannan ayyuka ne don gado ba don ladar da ake biyansu ba.

Wasannin wanzamai

Wanzamai suna da keɓantattun al’adunsu da suke yi a lokutan bukukuwansu, suna kuma da gangarsu ta musamman. Kurya, ita ce gangar wanzamai, bikinsu kuma ana ce da shi Wasan Aska. Idan za a yi
wasan aska, akan saka rana da wuri, sai jama’a su tanadi wannan rana dan kallo, su kuma masu gudanar da wannan wasa su yi shiri. Makaɗin gangar wanzamai yakan je filin da za a gudanar da wannan wasa ya fara kiɗa tun da wuri. Idan jama’a suka jiyo sautin wannan ganga, sai su riƙa zuwa gurin sannu a hankali suna taruwa. Bayan jama’a sun taru, su kuma wanzamai sai su zo don gwada bajimtarsu.

Daga cikin abubuwan da suke yi akwai fito da aska ta yi rawa, yin kaciya ba tare da jini ya zuba ba, yin kaciya daga nesa, yi wa bango ƙaho, kiran zabira, burkaka aska cikin baki, yi wa turmi tsaga da sauransu.

Manazarta

Alhassan, H. da wasu (1982). Zaman Hausawa Na Biyu, Don Makarantun Gaba da Sakondare. Zaria: Institute of Education, Ahmadu Bello University.

Batagarawa, S. A. (2013). “Nason Wasu Al’adu a kan Sana’o’in Gargajiya na Hausawa Mazauna Lokoja.” Katsina State History and Culture Bureau In Collobaration with Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yarsdua University.

CNHN, (2006). Ƙamussun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×