Skip to content

Zumunci

Zumunci sananniyar kalma ce a al’ummar Hausawa. Tana da matsayi ne na aikatau wacce ke bayanin aikin da aka yi na sakamakon zumunta. Ita kuma zumunta suna ne wanda daga gare shi ne aka samu kalmar zumunci. Wasu masanan suna da ra’ayin cewa, an sami wannan kalma ne daga Zumun wadda ke nufin ɗan’uwa.

360 F 168613008 1vbCH8HvHpit37nBeUsUAljzoiYjGLi8
Sada zumunci na ƙara soyayya da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Zumunci ɗabi’a ce da ke da muhimmanci kuma ana yawan sadar da ita tun tsawon lokacin da Hausawa suka fara zama a matsayin al’umma har ya zuwa yau. Babu lokacin da ake tunanin wannan dangantakar za ta tsaya, sai dai tana samun sauye-sauye saboda tasirin zamunna da ta ratso ana tafiya tare da ita. Don haka ana iya kallon zumunci da dangantaka mai kyau tsakanin mutane wanda ya shafi kula da jama’a ko abokan zama ta hanyar ƙulla wata alaƙa mai kyau wacce za ta ɗore.

Abin da zumunta ta ƙunsa

Abubuwan da zumuntar Hausawa ta ƙunsa sun haɗa da:

Ziyara

Ziyara na nufin mutum ya tashi daga inda yake, ya yi tattaki kusa ko nesa domin ya ga wanda yake da alaƙa da shi su gaisa. Wannan ziyara na iya kasancewa tafiya daga unguwa zuwa unguwa ko tsakanin ƙauyuka ko gari zuwa gari, da nufin dubo wani abokin zama ko ɗan’uwa ko masoyi, saboda Allah, ba don neman abin hannun wannan da za a je wajensa ba. A da irin wannan ziyarar gari ake niƙa mata. Wato idan wurin da za a kai ziyarar akwai nisa a tsakani, akan ɗauki lokaci ana shiri musamman ta fuskar guzuri da kuma tsaraba. Mutum zai tanadi abin da zai riƙa na lalurar hanya. Haka kuma zai tanadi abin da zai kai wa wanda zai tafi wurinsa. Kafin samuwar hanyoyin sufuri na zamani (mota da dangoginta) a matsayin hanyar sufuri, Hausawa suna amfani ne da dabbobi kamar jaki da doki ko ma da ƙafa don kai ziyara nesa. Irin wannan tafiyar takan ɗauki kwanaki ana ya da zango har a kai. Yanzu
kuma da aka samu inganattun hanyoyin sufuri, a rana ɗaya ma sai a kai ziyara nesa. ɗan’uwa yakan ji daɗi ƙwarai idan aka ziyarce shi.

Gudunmuwa

Bisa al’ada idan wata lalura ta taso a cikin dangi, ’yan’uwa da abokan arziki za su haɗa kai su bayar da gudummuwa ga wanda ake yi wa lalura a matsayin gudummuwa. Irin wanna yakan ƙunshi kuɗi ko abinci ko kayan amfani da sauran su. Ga tsarin zamantakewa, kowa yana bayar da gudummuwa daidai ƙarfinsa. Wanda kuma bai da abin bayarwa, zai sanya ƙarfi wajen yin aikace-aikace har a gama lalura kowa ya watse. Bayan abin da ya shafi harkokin murna, akwai gudummuwa ta jarabawa kamar wata mummunar ƙaddara ko haɗari ko gobara ko rashin lafiya ko mutuwa, da duk wani abin alhini da zai samu mutum. Akan sadar da zumunci ne a irin waɗannan ta hanyar ba da gudummuwar wani abu don rage masa zafi ko damuwar da yake cikinta. A al’adar Hausawa, duk mutumin da yake da ɗabi’ar bayar da gudummuwa to za a ɗauke shi mai son zumunci.

Jajantawa

Jajantawa wani nau’in gaisuwa ne mai ɗauke da tausayawa da ake yi wa mutum ta hanyar ziyara idan wani abu marar kyau ya same shi. Akan kai irin wannan gaisuwa ne don a taya shi jimami tare da ba shi haƙuri na ya ɗauki dangana bisa ga abin da ya same shi. Irin wannan kulawar tana sa mutum ya ji sanyi ga rayuwarsa, ya san cewa ‘yan uwansa da makusantansa da abokansa na arziki sun damu da shi. Abubuwan da ake yi wa jaje sun haɗa da mutuwa, haɗari, ɓari, gobara, rashin lafiya da sauransu. Bahaushe yana ɗaukar jaje a matsayin hanyar sadar da zumunci.

Kyautatawa

Hausawa suna ƙara sadar da zunumta ta hanyar kyautatawa ta ɓangarori da yawa na rayuwa. Irin wannan kyautatawa ya shafi taimaka wa mutum idan an ga yana buƙata, ko a ba shi abin da bai da ƙarfin da zai iya samunsa. Bayar da kyauta a kai-a kai a lokutan da suka dace kamar lokacin azumi ko lokacin salla (karama da babba) da sauransu duk kyautatawa ne. Ka ga dattijo da kaya a kai ka ɗaukar masa duk kyautatawa ne. Ka gina rijiya ka bar mutane suna amfani da ita kyauta, kyautatawa ne. Ba mutum bashi musamman idan yana cikin tsananin bukata, kyautatawa ne. Yin ire-iren waɗannan a al’umar Hausawa yana ƙara samar da zumunci tsakanin wanda ya yi da wanda aka yi wa.

Ɗaukar nauyin lalurori

Yana daga cikin hanyar tabbatar da zumunta mutum ya rinƙa ɗaukar nauyi na ɗawainiyar ‘yan’uwa musamman idan yana da zarafi. Haka ma zumunta ta maƙwabtaka ko sanayya na san a rinƙa ɗaukar irin wannan nauyin. Hausawa sun ɗabi’antu da ɗauke irin wannan nauyin idan wani ɗan’uwa ya rasu ya bar yara ƙanana. Daga cikin nauyin da akan ɗauke akwai lalura ta karatu ko gini ko ciyarwa ko hidimar aure da dai sauran su. A al’umar Hausawa, zumunta takan ƙara ƙarfafa tsakanin wanda ya ɗauke nauyin irin waɗannan lalurori da waɗanda aka ɗauke wa nauyin.

Bayar da kariya ta tsaro

Idan akwai zumunta tsakanin mutane ana samun taimakekeniya na bayar da kariya ko tsaro tsakanin juna. Misali dangantakar da ke tsakani za ta sanya idan aka ga abin da zai cutar da mutum ko iyalinsa ko dukiyarsa, a sa ido ko a tsawata ko da bayan idonsa ne. Wannan zai sa ko mutum ba ya nan, yana da kwanciyar hankalin da ya san ya bar masu kula da abin da ya bari ba tare da wata damuwa ba. Wannan ko shi ne muhimmancin zumuntar da zamantakewa mai kyau a cikin al’umma. Amma wanda duk ba ya da wannan dangantaka mai kyau da jama’a ba zai sami da wannan gata ba.

Bayar da shawarwari

Zumunta wadda ta ƙunshi kyakkyawar dangantaka tana sanya ka isa ga mutum har ka gaya masa gaskiya ko ka ba shi shawara musamman idan ka ga ya kauce hanya. Haka kuma akan ba mutum shawara idan aka yi wa mutum tunanin da shi bai yi wa kansa ba. Mutane sun fi neman shawara daga waɗanda suke da zumunci da su a kan abin da ya shafi rayuwarsu ko abin da suke so su aiwatar ko neman ƙarfafawa da ƙarin haske. A cikin ‘yan’uwa ma akwai wanda aka fi jituwa da shi, wanda idan har hakan ta taso, babu fargaba, ana ba shi shawara, shi kuma ya faɗi abin da idan an yi aiki da shi za a samu biyan buƙata.

Sasantawa

A dalilin zumuncin da ke tsakanin mutane, idan an samu saɓani tsakanin ɓangarori biyu, ‘yan’uwa suna samun waɗanda alhakin sasanta ɓangarorin ya rataya ga wuyansu. A irin haka, akan kira kowanne ɓangare don jin ta bakinsu, sa’annan daga baya a sulhunta su. Haka kuma akan kwaɗaitar da su na su riƙe zumunci saboda zama ya yi kyau.

Girmama juna

Idan akwai zumunta ko dangantaka ta zaman tare, za a samu girmamawa ga ma’abota ita, inda kowanne yana girmama ɗan’uwa ta yadda wanda yake babba za a ba shi girmansa, shi ma ƙarami za a mutunta shi yadda ya kamata. Wannan shi ke ƙara ɗankon zumunta, zama ya yi daɗi.

Ƙulla alaƙa ta aure

Idan zumunta ta yi daɗi, hakan shi zai sa magabata su yi tunanin ƙulla aure tsakanin ’ya’ya saboda zaman ya ƙara armashi kuma a ci gaba da cin moriyar juna. Wannan ya sanya Bahaushe ke da auren zumunta.
Wannan auren zumunta idan ya yi kyau, zumunta za ta ƙara daɗi gwanin ban sha’awa. Amma idan ya lalace ko ya zama ɗaya ake cutarwa, hakan ba zai yi daɗi ba. Idan ba a kai zuciya nesa ba, zumuntar da ke tsakani tana iya samun tangarɗa.

Rabe-raben zumuncin

Dalilai ko hanyoyin da aka bi wajen samar da zumunci a al’umar Hausawa ita ta bayar da damar karkasa shi zuwa rukuni-rukuni.

Zumunta ta jini

Wannan shi ne babban rukuni na zumunta da muke da shi, wacce ta dalilin silar haihuwa ta samu. Haɗa jini babbar dangantaka ce da mutum zai tashi tare da abokan haihuwarsa wuri ɗaya cikin kulawa da
mu’amala mai kyau. Ta hanyar wannan zumunci al’umma ke watsuwa wurare daban don a yi ta yaɗuwa, amma duk asali ɗaya ne.

Zumunta ta Addini

Wannan zumunta akwaita cikin al’ummar Hausawa tun lokacin da suke aiwatar da addininsu na gargajiya. Bayan Hausawa sun samu cuɗuwa da baƙi suka karɓi addinai da suka haɗa da musulunci da kiristanci, wannan zumuntar ta ƙara ƙarfafa. Kasancewar al’ummar Hausawa mafi yawansu musulmi ne da suke bin koyarwar addinin musulunci, wannan ya sanya suka yi riƙo da wannan zumunta, domin kuwa addinin musulunci ya ƙarfafa muna wannan zumuntar, na kasancewar musulmi ɗan’uwan musulmi duk inda aka haɗu.

Zumunta ta ƙabila

Zumuncin ƙabila, zumunci ne da aka taso cikin ƙabila ɗaya, launin fata ɗaya, harshe ɗaya, al’adu ɗaya, muhalli ɗaya ana tafiyar da rayuwa bisa tsari da dokokin da al’umma suka gindaya, cikin yarda da amincewar juna. Wannan zumunta ba makawa mutum yana sadar da ita, ko ya sani ko bai sani ba, domin kuwa idan mutum ya bar garinsu zuwa wata duniya, duk lokacin da ya haɗu da ɗan garinsu zai ji daɗi sosai. Wannan ya sanya mutanen da ke rayuwa a wani gari ko ƙasa da ba tasu ba, suka zama a unguwa ɗaya da suke tafiyar da rayuwarsu. A cikin Nijeriya ana samun unguwannin Hausawa a garuruwan da ba na Hausawa ba, tare da sana’o’insu kamar zango, tudun-wada, unguwar Hausawa da sauransu.

Zumunta ta sana’a

Mafi yawan masu sana’a iri ɗaya, ta hannu ce ko ta zamani suna da dangantaka mai kyau a tsakani. Hakan ya sa za a ga suna zama wuri ɗaya inda suke yin sana’ar ko kuma suna zama a unguwa ɗaya. Wannan ya sanya ake samun unguwanni masu ɗauke da masu nau’in sana’a iri ɗaya a ƙasar Hausa. Misali a wasu sassa na ƙasar Hausa akan sami unguwanni masu alaƙa da sana’o’i kamar maƙera, marina, majema masaƙa da sauran su.

Zumunta ta auratayya

Dalilin auratayya tsakanin ɓangarori biyu yana ƙara ƙulla danƙon zumunci ta yadda ‘yan uwan ɓangarorin sun zama ‘yan uwan juna. Wannan yakan sa duk inda aka haɗu tun da suna da dangantaka ta fuskar ‘yan’uwansu ma’aurata, sai ya zama su ma suna ganin kansu a matsayin ‘yan’uwan juna. Misali a al’umar hausawa, idan namiji ya aure mace, duk ’yan’uwan matar nan zai rinƙa yin zumunta da su. Haka ita ma duk ’yan’uwan miji sun zama ’yan’uwanta sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen yi musu hidimar da ta dace a dalilin aure.

Zumunta ta sanayya

Wannan tana samuwa a dalilin karatu a makaranta ɗaya, ko wata tafiya da ta haɗa mutane, ko wani aiki, ko kasuwancin da ya shiga tsakani da sauransu. Irin waɗannan haɗuwa suna ƙulla danƙon zumunci mai ƙarfi tsakanin masu wannan dangantaka. A wasu lokuta idan har ba bayani aka yi ba, ana iya ɗauka zumunta ce ta jini a tsakani.

Zumunta ta Barantaka ko koyon aiki ko sana’a

Barantaka shi ne mutum ya zauna a ƙarƙashin wani su kansance yaro da ubangidansa. A irin wannan yanayi, yaron yakan yi wa ubangida aiki da
hidimomi daban-daban. Ubangidan kuma shi yake da alhakin kyautata wa wanda ke ƙarƙashinsa ko biyansa haƙƙinsa na aikin da yake aiwatarwa. Ana yin barantaka ta fuskoki da dama da suka haɗa da kasuwanci da almajiranci da hidimomi na ayyukan gida da sauransu. Haka kuma mutum yana samun ubangida a wajen koyon wata sana’a ko a wajen aiki. Wannan dangantaka tana zama zumunta mai ƙarfi, musamman idan ana zama mai kyau.

Zumunta ta maƙwabtaka

Wannan babbar zumunta ce a idon Bahaushe, sai kuma addinin musulunci ya ƙara ƙarfafa ta. Bahaushe yakan ɗauki maƙwabci kamar ɗan’uwansa. A wasu lokutan ma zumuncin maƙwabtaka ta Bahaushe yakan sa ya bar wa maƙwabci wasiya ko kalihu ko kulawa na wani lamari da dai sauran su. Maƙwabcin Bahaushe yana da ikon ya tsawata wa yaran maƙwabci idan ya ga abin da zai cutar da su. Yana iya bai wa mutum shawara na duk abin da ya ga ya dace.

Al’adun Hausawa da suka ƙarfafa zumunta

A dalilin riƙo da zumunta da Bahaushe ke yi da tasirin da take da shi a cikin al’umma, ya ƙarfafa wasu al’adu da suka haɗa da:

Wasannin barkwanci

Hausawa suna yin wasannin barkwanci ne tsakanin masu dangantaka ta jini kamar ta kaka da jika; ko tsakanin taubasai (waɗanda suke ’ya’yyan maza da ’ya’yan mata). Haka kuma akwai irin wannan wasa tsakanin Hausawa mazauna gari ko ƙasa daban-daban kamar Kanawa da Zagezagi.

Tatsuniya

A cikin tatsuniyoyin Haussawa ana cin karo da tasirin zumuncin Bahaushe, inda za a kawo labari wanda ya danganci hakan kamar labarin wa da ƙane, miji da mata, kishiya da kishiya, sarki da talakawansa da sauransu. Haka ma yanayi da tsarin tatsuniyar ta ginu ne a kan zumunci. Wato yara su fito daga gidaje daban-daban su taru a wuri ɗaya a yi musu tatsuniya.

Zaman makaranta

Makaranta kowace iri a al’ummar Hausawa takan zama wani dandali na samar da zumunci a tsakanin mutane. A duk lokacin da yara suka haɗu a makaranta ɗaya na lokaci mai tsawo don karatu, to zumunci ne abin da zai biyo bayan maƙasudin da ya tara su. Ta nan ne za a ga dangantakar ta ɗore har abada. Wasu daga nan ne ake ƙulla aure a tasanin ɗaliban ko a tsakanin ’ya’yansu ko zuri’arsu.

Gayya

Hausawa sukan gudanar da al’adar gayya inda ake taruwa a gudanar da wani aiki don taimaka wa wani ko taimakon al’umma. Irin wannan al’ada takan samar da zumunta tsakani wanda ya yi gayyar da wanda aka yi wa. Haka kuma ana samun zumunta a tsakanin waɗanda suka aiwatar da gayyar wadda takan iya ɗorewa har abada.

Manazarta

Bala, R. S. (2023, December 24). Sada zumunci da abubuwan da ke yanke shi a zamanin nan. Leadership Hausa.

Mustapha, O. (2014, January 9). Matsayin sada zumunci a Musulunci. Aminiya.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×