“A Man Of The People” labari ne mai ban sha’awa da Chinua Achebe ya rubuta, wanda aka buga a shekara ta 1966.
Ta hanyar ba da labari mai ma’ana, Achebe ya nuna sarƙaƙiya da saɓanin siyasar Afirka, ya kuma yi ƙarin haska ƙalubalen gina ƙasa, cin zarafi, da gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da adalci a cikin al’umma. A Man Of The People, labari ne mai tunzura jama’a wanda ya yi duba game da dambarwar siyasar nahiyar Afirka da yanayin rayuwar ɗan’adam. Hakazalika, labarin ya dace kuma ya nuna ƙarfin cin hanci da rashawa a siyasa a cikin al’ummomin wannan zamani.
A cikin littafin A Man Of The People, Achebe ya bayyana wani matashin malami mai suna Odili Samalu, wanda ya yanke ƙauna game da gurɓatattun ayyukan siyasa na Minista Nanga, da farko ya karɓi tayin ya kasance mai goyon bayan ministan, amma tun tafiyar ba ta yi nisa ba ya yanke shawarar kalubalantar shi a siyasance.
Labarin ya ginu ne a wata ƙasa da ba a bayyana sunanta ba, wacce ba ta jima da kuɓuta daga hannun Turawan mulkin mallaka ba. Chinua ya rubuta labarin ta salon wakilin suna na ɗaya, wato tauraro cikin fage, wannan wani salo ne da ke sa mai karatu ya ji daɗin karatu yayin da yake karanta labarin da kansa.
Babban jigon labarin
Muhimmin jigon labarin shi ne cin hanci da rashawa da ya danganci mulki. Labarin ya kwatanta yadda masu mulki kamar Cif Nanga, sukan miƙa wuya ga cin hanci da son abin duniya kacokan, su yi watsi da nauyin da ke kansu na al’umma.
Wasu ƙarin jigogin sun haɗa da:
- Yawaitar ɗaukar fansa
- Ra’ayoyin jama’a game da salon mulki
- Mayar da mata saniyar ware
- Matsalolin da kan taso bayan kuɓuta daga mulkin mallaka
Bayanin littafin a taƙaice
– Mawallafi: Chinua Achebe
– Karantawa a audio: Babu
– Zanen bango:
– Harshe: Ingilishi
– Maɗaba’a: Heinemann(UK)
John Day (US)
– Kwanan watan ɗab’i: 1 ga Janairu, 1966 (An kuma sake bugawa 19 ga Janairu, 1989)
– Wajen wallafa: Amurka da Birtaniya
– Adadin shafuka: 167
– Lamabr littafi ta ƙasa da ƙasa:
ISBN-10 0385086164
ISBN-13 978-0385086165
Ra’ayoyin wasu makaranta littafin
Miranda
“Wani abokina ne ya bayyana mini wannan littafi a matsayin hanya mafi kyau don fahimtar dalilin da ya sa Afirka ta kasance kamar yadda take… Haka kuma kasancewar shi abin karatawa mai kyau, sarkakiyar siyasar Afirka a bayyane take a nan, tashin hankalin bayan mulkin mallaka, da buri da sukar gwamnati, da cin hanci da rashawa, abin ban sha’awa ne sosai.”
Hannah Kageche
“A Man Of The People, na Chinua Achebe, ya kasance cikin jerin littafai na gaba-gaba a wajena. A baya a makarantar sakandare, akwai littattafan marubutan Afirka gabaɗaya waɗanda ake kira Pacesetters. Sun haɗa da litattafai 130 da Macmillan ya buga a cikin jerin, amma mun ƙare da cin zarafi da furta kalmar muzanci ga duk wasu manyan littattafai da manyan marubutan Afirka suka rubuta.
Waɗansu al’amuran soyayya a cikin littafan sun haifar da hirarrakin sha’awa a tsakanin ɗalibai a lokacin hutu da kuma lokacin darusa ga marasa hankali.
Ban taɓa samun damar karantawa ba saboda dalilai guda biyu, na farko ni memba ce ta kungiyar Kiristoci kuma ina jin tsoron abin da mutane za su ce. Na biyu kuma, waɗannan littattafan ba su da sauƙin samu. Ban san wanda zan ba wa cin hanci ba ya ba ni na karanta… Hakan ya saɓawa dokar Christian Union, babu cin hanci, kuma babu soyayya.
Shekarar 2018 ita ce shekarar da na ji na isa in sa hannu kan wannan waɗannan littafai na 1966. Kuma tabbas, na ga babban tashin hankali. Yanzu da na girma, na fahimci dalilin da yasa zai zama abin damuwa ga yarinyar da ba ta balaga ba… amma duk wanda ya wuce wannan shekarun zai mutunta shi don wasu halaye.”
Hanan
“Na tsani kashi biyu bisa uku na farkon wannan littafin, amma na ji daɗin ƙarshensa. Kamar yadda yake tare da sauran littattafan Achebe, yana da ma’ana mai kyau. Da farko labarin ya zama kamar wata tatsuniya ce ta ɗabi’a, ta mutumin kirki da ya sauya zuwa gurɓatacce. Amma sai dai mai ba da labarin (tauraon), wani matashi ne mai akida a cikin shekarunsa ashirin, ya yanke shawarar tsayawa tsayin daka ga mai cin zarafi da wasu dalilai marasa kyau. A wannan lokacin, sai Achebe ya bayyana yadda yake matashi da wauta da girma kai da son kai da manufa da kyauta, duk a lokaci guda. Haka kuma yadda ake kula da alakar tauraron da mahaifinsa abu ne mai girma.”
Taƙaitaccen tarihin marubucin
An haifi Chinua Achebe a ranar 16 ga watan Nuwamba 1930, ya kuma rasu a ranar 21 ga watan Maris 2013. Marubucin ɗan Najeriya ne, mawaki ne kuma farfesa, sannan masharhanci ne. Littafinsa na farko shi ne, Things Fall Apart (1958), shi ne littafin da aka fi karantawa a cikin ayyukan adabin Afirka na zamanin.
Achebe wanda ya samu kulawar iyayensa a garin Ogidi da ke kudu maso gabashin Najeriya, ya yi fice a makaranta inda ya samu gurbin karatun digirin farko. Ya zama mai sha’awar addinan duniya da al’adun gargajiya na Afirka, kuma ya fara rubuta labari tun yana ɗalibin jami’a. Bayan kammala karatunsa, ya yi aiki da gidan rediyon Najeriya (NBS). Ba da jimawa ba ya koma babban birnin Legas. Hankalin duniya ya yo kansa dalilin littafinsa Things Fall Apart a ƙarshen 1950s; littattafansa na baya sun haɗa da No Longer at Ease (1960), Arrow of God (1964), A Man of the People (1966), da Anthills Savannah (1987). Achebe ya rubuta litattafansa a cikin harshen Turanci kuma ya kare dokokin amfani da Ingilishi, a cikin adabin Afirka.
Lokacin da yankin Biyafara ya ɓalle daga Najeriya a shekarar 1967, Achebe ya zama mai goyon bayan ‘yancin Biafra kuma ya zama jakadan yankin. Yaƙin ya yi wa al’ummar Biafra kaca-kaca, yayin da yunwa da tashe-tashen hankula suka yi ƙamari, ya yi kira ga al’ummar Turai da Amurka da su ba da taimako. A lokacin da gwamnatin Najeriya ta sake karɓe yankin a shekarar 1970, ya tsunduma kansa cikin harkokin siyasa, amma takaici da cin hanci da rashawa, ya sa shi yin murabus. Ya zauna a Amurka na shekaru da dama.
Manazarta
Amroun, K. (2016). Chinua Achebe a man of the people. Ummto.
SuperSummary. (n.d.) A Man of the People summary and study Guide. SuperSummary.
Goodreads (n.d.) A man of the people . Goodreads.
GradeSaver. (2024, March 1). A Man of the People Bibliography GradeSaver.
Wikipedia contributors. (2024c, July 19). Chinua Achebe. Wikipedia.