Kyamara wata na’ura ce da ake amfani da ita wurin ɗaukar hotuna da bidiyo, ko haska shirye-shiryen gidajen talabijin, ta hanyar amfani da wutar lantarki. Kyamara na’ura ce ta fasaha a fagen ɗaukar hotuna da bidiyo. Na’ura ce da ke taka muhimmiyar rawa ga cigaban fasahar kafofin watsa labarai da nishaɗi da tsaro da kuma bincike kan abubuwa da dama musamman na kimiyya.
Masana sun tabbatar da cewa kyamara ta wanzu a duniya a ƙarni na 19, kuma ta ci gaba da kawo cigaba masu yawa a faɗin duniya tun daga abin da ya shafi fannin ilmi da kuma kimiya da fasaha har zuwa ƙarni na ashirin da ɗaya.
Muhimmancin kyamara
Kyamara na’ura ce da ta ƙunshi ɗaukar ɓangare mai mahimmanci na al’adun zamani kuma ta yi tasiri mai yawa a wasu fannoni na rayuwar yau da kullum wanda suka haɗar da;
Adana tarihi
Kymara na ba da damar ɗauka da adana abubuwan da suka faru na musamman domin tarihi, kamar abubuwan da suka a faru wurin gudanar da biki ko kuma wani taro na musamman wanda yake buƙatar adana bayanan da suka haɗa da hotuna da bidiyo domin tarihi ko kuma wata buƙata.
Sauƙaƙa sadarwa
Kyamara tana taimakawa ƙwarai da gaske wurin sauƙaƙa wa al’umma fahimta da riskar bayanan abubuwan da suka faru ba sa nan. Kamar abin da wani taro ko biki ya ƙunsa. A takaice za a iya cewa tana taka muhimiyar rawa wurin sadar da hotunan abubuwan da suka faru tsakanin abokai da ‘yan uwa ga waɗanda ba su samu damar halartar abin ba.
Binciken kimiyya
Kyamara na’ura ce mai muhimmanci a fanni binciken kimiyya, domin da ita ne ake ɗauka tare da tantance duk wani abu da ya kamata a nuna ko kuma a ba da hoton misalinsa ga ɗalibai ko kuma ga masana.
Taimakawa ga tsaro
Kyamara na ba da gudunmawa wurin tsaro, domin da ita ne ake iya ganin abubuwa da suke gudana, idan aka duba abubuwan da suke faruwa a ƙasashe ƙetare ko kuma a fina-finai za a ga yadda kyamara take take taimakawa wajen ba wa ‘yansanda da jami’an tsaro damar kama masu aikata laifuka cikin sauƙi. Tana kuma ba da tsaro a titina da duk wani saƙo da lungu da ake buƙatar yin bincike. Haka suma masu aikata laifuka matuƙar sun tabbata akwai kyamarar tsaro to ba su cika yin ta’annaci a wuri ba saboda sun san cewa dole sai an nemo su duk inda za su shiga.
Nishaɗi
Kymara tana taka rawar gani wajen samar da nishaɗi ta hanyar amfani da ɗaukar shirye-shirye wasan kwaikwayo da raye-raye ko waƙe-waƙe da sauransu.
Kafofin yaɗa labarai
Kymara tana taimakawa ga cigaban kafofin yaɗa labarai, musamman a wannan zamanin muke ciki. ‘Yan jaridu kan yi amfani da kyamara domin ɗauka da naɗar rahotannin labarai sawa’un ta hanyar amfani da hoto mai motsi ko kuma sandararre.
Ire-iren kyamara
Akwai ire-iren kyamara da ake amfani da su waɗanda suka haɗa da:
Brigde Cameras
Kyamara ce da ta ƙunshi damar ɗaukar hoto amma kuma tana da ƙaranci abubuwan amfani na zamani. Kyamara ce da ake amfani da ita tun a shekarar 1980.
Digital Camera
Na’urar ɗaukar hoto ce da ake amfani da ita wurin ɗaukar hotuna masu ƙayartarwa. Yawancin kyamarorin da ake amfani da su a yanzu duk nau’inta ne. Suna taimakawa wurin ƙawata hoto sosai.
Action camera
Kyamara ce da ta ƙunshi ɗaukar rahoton da ya shafi aiki ko kuma abin da ake gudanar da shi a aikace ba wai iya hoto ba.
CCTV Camera
CCTV nau’in kyamara ce da ke da matuƙar muhimmanci wadda kuma take taimakawa wurin tabbatar da tsaro da kuma cigaba a duniya baki ɗaya. Akan yi amfani da kyamarar domin tabbatar da tsaro a wurare mabambanta kamar; kasuwani da tituna, manyan shaguna na saye da sayarwa da kuma bankuna, asibitoci da kuma wurin taron manyan mutane.
Na’urar tana taimaka wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na kama masu laifi. Ta kuma taimaka matuƙa wurin sake kawo cigaba ta fuskar ƙara matakan tsaro a duniya.
Ɓangarorin kyamara
Kyamara tana da ɓangarori da dama, waɗanda suka kasance kowane da aikinsa da kuma amfaninsa ta kowace fuska. Ɓangarorin kyamara suna da yawa, ga bayanin wasu muhimmai daga ciki;
- Viewfinder: Wani ɓangare ne a kyamara wanda yake a bayanta, shi ne yake bayar da damar tantance hoto kafin a kai ga ɗauka.
- Pentaprism: Wani madubi ne na musamman a tattare da kyamar da ke ba da damar tantance hasken da ya kamata ya yi tasiri a tattare da kyamara.
- Built-in Flash: Ƙaramin haske ne da ke a gaban kyamara wanda yake taimakawa wurin fitar da haske mai ƙarfi. Aikinsa kawai sai za a ɗauki hoto yake haskawa domin tabbatar da fitar da abin da za a ɗauka. A lura sosai wannan hasken yana kunna kansa ne kawai lokacin da za a ɗauki hoto don a iya ganin abin da ake son ɗauka da kyau.
- Lens Hood: Yana hana hasken da ba a so shiga lens, yana rage flare domin tabbatar da ingancin hoto.
- Circular Polarizer: Yana rage hasken kyamara yayin da za a yi hoto domin inganta launi ko kalar abin da za a ɗauka ko kuma yayin bayyanar da abu mai duhu ne ko kuma mai haske ne.
- Flash Button: Shi ma ɗaya ne daga ɓangarorin kyamara da ke amfani wurin haska abin da za a ɗauka kusan suna tafiyar kura ne da built flash ɗaya na taimakawa ɗaya.
- Lens Mount: Wannan shi ne idon kyamara. Domin kuwa shi ɗin wata mahaɗace da ke tattara daidaiton hotunan da mai ɗauka ya ɗauka. Da shi ne ake iya fahimtar wannan hoton bai dace ba, a sauya shi zuwa wani lens din daban.
- Light Diffuser: Tana taimakawa wurin rage haske yayin gudanar da aikinsa domin daidaita abin da za a ɗauka da kyau.
- Buffer: Wannan na a matsayin ma’ajiya. Waje ne da ke riƙe da hotuna kafin ya kai su wurin da zai zama ma’adana ko kuma mazaunarsu. Yana taimakawa matuƙa wurin tace hotuna kafin a fitar da su. Domin da shi ne ake cire wanda ake buƙata a kuma tura wanda ba a buƙata zuwa inda ya kamata. Yakan taimaka sosai yayin da ake buƙatar ɗaukar hoto cikin sauri domin yana adana duk abin da aka ɗauka.
Kayan kariya ga kyamara
Bayan waɗannan ɓangarori da aka kawo da bayanansu, akwai wasu kayan aiki da take ɗauke da su kamar:
- Camara Bag: Wannan tana kare kyamara da lens ɗinta yayin tafiya ko adanawa. Wato dai wannan ita ce jakar kyamara.
- Clear Kits: Yana amfani wuri ba wa ita kanta kyamara kariya, haka ma lens, uwa uba kuma mai tantance hoto kansa wato viewfinder.
Manazarta
Wikipedia contributors. (2024, December 3). Camera. Wikipedia.
Picoult, J. (2024, June 2). 22 Main Parts Of A Camera & How They Work. MeFOTO.
Paessle (n.d.) What is CCTV? Definition and Details Paessler