Ciwon haƙori ciwo ne daka iya haifar da rashin jin daɗi a kusa da haƙori, ko kuma abin da yake da dangantaka da haƙori. Sau da yawa yana iya zuwa da zafin jiki ko takura ga masu fama da shi. Ciwon yana nuna yiwuwar lalacewa ko kamuwa da cuta, yawanci daga cavities ko kumburi da ake kira pulpitis hakan ke afkuwa. Ƙashin haƙori mai ɗauke da jijiyoyi da magudanar jini, na iya kumbura ko kamuwa da su saboda kogo ko tsagewa, wanda ke haifar da ciwon haƙorin kai tsaye.
Alamomin ciwon haƙori
Waɗannan duk a bayyane suke, domin alamomin ba su cika zama ɓoyayyu ba. Misali:
- Kumburi
- Yawan dalalar ko taruwar miyau.
- Jin zogi wanda ke kuɗa har kunne akan iya jin ciwon da wuya
- Wahalar haɗiyar abinci.
- Zafi yayin tauna.
- Zafin yayin waige, ko haƙori yake ruwa.
- Nauyin numfashi, da warin numfashi.
Ciwon haƙori tare da zazza6i lokaci guda yana nuna yanzu haka ƙwayoyin cutar suna kan aikinsu, kamar kura ce take cin barewa da ranta batare data kashe ba. Shi ya sa azabtar ciwon ba a cika daure mata ba.
Ire-iren ciwon haƙori
Ciwon haƙori mai tsutsa
Irin wannan ciwon haƙorin zahiri akan iya ganin tsutsar ta fado a wasu lokutan daga bakin mai fama da lalurar. Musamman idan aka yi amfani da maganin da ya danganci kuskure baki.
Ciwon haƙori mai kumburi
Irin wannan ciwon haƙorin kan iya sanya sauyawar halittar fuska, kamar kumburi ko karkacewar baki ko kuma saka baki ya yi tsayi tamkar shantu.
Ciwon haƙori mai kakkaryewa
Irin wannan nau’in ciwon haƙorin kan sa haƙori ya dinga karyewa a hankali yana barin ɗan uwansa. Irin sa ga fi haɗari domin haƙorin da ransa yake karyewa idan ba a kula ba wurin karyewar yakan bar guntun haƙori wanda kan iya nutsewa a cikin dassashi ya haifar da matsala.
Ciwon haƙori mai kogo
Irin wannan ciwon haƙorin yana sanya ɗimaucewa ga mai fama da shi, domin rami ne yake haifar wa a wurin haƙorin wanda ko ruwa mai ciwon ya sha matuƙar ya bi ta wurin sai ya ɗanaɗana kuɗarsa domin zai ji kamar an zuba masa wuta ne a wurin.
Abin da yake jawo ciwon haƙori
Dalilai da yawa kan iya kawo afkuwar ciwon haƙori kamar:
- Akwai ciwon haƙorin dake faruwa dalilin lalura ta sanyin jiki wanda Allah Ya hallici kowane ɗan Adam da shi.
- Akwai ciwon haƙori na dalilin shan abu mai zaƙi, wanda masu irin wannan ciwon haƙorin za ka ga suna fuskantar sauyawar kalar haƙora wanda ake kira da suna (Shan zuma).
- Akwai kuma ciwon haƙori na amosanin baki. Irin wannan ciwon haƙorin haifar da wari a barin mai fama da lalurar ko da kuwa kullum yana cikin wanke bakinsa ne.
- Lallacewar haƙori kan iya haifar da ciwon haƙori. Lallacewar kan iya faruwa ta hanyoyi mabanbanta. Kamar faɗuwa ko haɗari ko kuma rashin kula da haƙorin gaba ɗaya ta fuskar tsafta da sauran su.
- Daga cikin dalilan kamuwa da ciwon haƙori akwai ruɓewa. Wadda akasari rashin kula ke kawota ko kuma lalura ta sanyi ko amosanin. Hakan kan sa ya shiga cikin enamel da dentin, wanda ke haifar da ciwon haƙori.
- Gingivitis zai iya haifar da ciwon danko da haƙori saboda kumburi da aljihun da ke kewaye da haƙora.
- Kumburi na cavities na sinus na iya yin laushi na sama, hakan kan iya haifar da ciwon haƙori.
- Trigeminal neuralgia yana haifar da zafin fuska mai kaifi. Daga nan ya kan iya taɓa haƙori ya samu matsala.
- Shaye-shayen ƙwayoyi na iya haifar da ciwon haƙori.
- Rashin vitamin babbar matsala ce a jikin ɗan’adam, wanda haɗarinsa kan iya haifar da haɗarin kamuwa da ciwon haƙori.
Kariya daga ciwon haƙori
Hanyoyin kariya daga kamuwa da ciwon haƙori suna da yawa. Ga wasu daga ciki:
- Gujewa shan taba sigari.
- Gujewa amfani da brush ɗin wani.
- Gujewa shan abu mai zaƙi.
- Gujewa shan abu mai sanyi.
- Gujewa amfani da abu mai tsini da sunan saka ce ko wani abu daban, domin daga nan ne ake soma tsokano asalin ciwon.
- Cin abu mai gina jiki da ƙara ƙarfin dassashi.
- Amfani da kayan wanke baki masu inganci.
Wasu shawarwari game da haƙori
- Lura da tsaftar haƙoraHalori shi ne mahimmi. Don haka idan kana kokonto game da yadda ake brush ka daure ka ware lokaci minti 5 kacal ya isa ka buɗe YouTube, ka binciko bidiyo game da yadda ake wanke baki da brush.
- Bayan ka iya ko ka koya to mafi ƙarancin shi ne ka goge baki sau 2 a rana, mafi inganci sau 4 ko duk bayan gama cin abinci.
- Yayin goge baki idan an goga makilin to ba nan da nan ake kurkurewa ba, dole a jira minti 2 zuwa 5 a bari fluorides ɗin makilin ɗin ya yi aikin kashe ƙwayoyin cutar idan ba haka ba ko da an goga burushi yadda ya dace ba za a kashe komai ba, kuma hakan ba zai hana haƙora ciwo ba.
- Yawaita amfani da dental floss ko interdental cleaner ana tsefewa ko sakace tsakanin haƙori. Saboda wannan ma mahimmi ne, galibi ta inda bakteriya din ke fara samun mazauni ke nan
- Shi kansa brush akwai buƙatar ko da sati-sati ake tsomashi a ruwan ɗumi ya ɗan dahu saboda bakteria ɗin. Sannan a sani brush na expire a wata 3 ne indai kullum ana amfani da shi. Don haka duk wata 3 zuwa 4 ake canza sabo.
Magunguna
Magungunan ciwon hakori suna da yawa, kuma akwai na gargajiya akwai na likitanci.
Magungunan gargajiya
Ana amfani da wasu hanyoyi da magunguna na gargajiya don magance cututtukan baki ciki har da ciwon hakori. Wasu daga cikin magungunan sun haɗa da:
- albasa
- ganyen guava
- ganyen mango
- ganyen dankalin turawa
- ganyen sunflower
- ganyen taba
- tafarnuwa
Magungunan likitanci
- Ibuprofen: Adadin da ake sha shi ne 400 gm duk bayan awanni 4 – 6. Kada a wuce fiye da 3,200 gm kowace rana.
- Aspirin: Adadin da ake sha shi ne 1-2 325 gm na ƙwayar maganin duk bayan awanni 4, ko ƙwayoyi 3 bayan awanni 6. Kada a wuce kwayoyi 12, ko 3,900 gm, kowace rana.
- Naproxen: Likitoci sun ba da shawarar farawa na 500 mg, sannan 250 mg duk bayan awanni 6 – 8 kamar yadda ya cancanta. Kada a wuce adadin yau da kullun na 1,250 mg
- Diclofenac: Adadin da aka ba da sha shi ne 100 mg kowace rana. Kada a wuce sai dai idan likita ya ba da shawarar hakan.
Manazarta
Contributors to Wikimedia projects. (2024, February 19). Ciwon hakori. Wikipedia.
Hospitals, M. (n.d.-a). Ciwon Haƙori: Dalilai, Bincike da Jiyya. Medicover Hospitals.
Umar, H. (2022, May 5). LAFIYA UWAR JIKI: Tattaunawa kan matsalar ciwon Hakori, Mayu 05, 2022. Voice of America.
Preventing tooth decay. (n.d.). Oral Health Foundation.