Skip to content

Ciwon zuciya

Ciwon zuciya dai ciwo ne da ake wa lakabi da ciwon bugun zuci. Wannan ciwon na faruwa ne ya yin da jijiyoyin zuciya suka yi rauni ko kuma suka yi tsauri, abinda zai hana su harba jini ga sauran sassan jiki.

Har ila yau masana a fannin kiwo lafiya sun bayyana ciwon zuciya da cewa ciwo ne da yake faruwa a sanadiyar gazawar jijiyoyin zuciya wajen aika jini zuwa ga sassan jiki kamar yanda sassan jikin ke bukata. Ciwon zuciya dai na da alaka da ciwon hawan jini da ba a bashi kulawar da ya kamata ba.

Abubuwan da ke kawo ciwon zuciya

  1. Hawan jini
  2. Kibar da ta wuce kima
  3. Yawan shan giya
  4. Tu’ammali da guba
  5. Cin abinci marar tsafta
  6. Gadon ciwon
  7. Kwayoyin cuta
  8. Karancin sinadarai a jiki

Alamomin ciwon zuciya

  1. Faduwar gaba ko saurin gajiya
  2. Wahalar numfashi yayin kwanciya ruf da ciki
  3. Zaka ji kanka kamar baka da nauyi
  4. Rashin jurewar motsa jiki
  5. Tari matsakaici ko mai tsanani
  6. Numfashin da ke bayar da sauti
  7. Saurin gajiya
  8. Daukewar jin yunwa
  9. Kumburin fuska da kafafuwa 

Hanyoyin kiyaye kamuwa da ciwon zuciya

  1. Masana a kulli yaumin suna fadin cewa babban kariya ga duk wani cuta shine samun isheshen kulawan likitoci, bi ma’ana, duk mai son kariya daga kamuwa da cutar ciwon zuciya toh, a kulli yaumin ya ke ziyartan likitoci don tabbatar da lafiya da ingancin jikin shi, musamman mata masu dauke da juna biyu.
  2. Duk mai son kariya daga kamuwa da wannan muguwar cutar toh, ya rage cin abu da zai sa shi kiba, sannan ya rage cin kitse.
  3. Mai son kare kanshi daga kamuwa da cutar ciwon zuciya, lallai ne ya yawaita motsa jiki (exercise).
  4. Har ila yau, masana sun bayyana bari ko rage yawan shan barasa ko giya da yana daya daga cikin matakai na kare kai da kamuwa da cutar ciwon zuciya.
  5. Hakama bari ko rage yawan cin gishiri shima na taimakawa wajen rage barazanar iya kamuwa da wannan cutar.

Idan aka kiyaye wadannan abubuwa in Allah ya yarda za’a magance duk wani hadari dake tattare da kamuwa da cutar ciwon zuciya.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×