Skip to content

Dan tayi

Ɗan tayi kalma ce da ake amfani da ita don bayyana mataki ko zango daga cikin rukunan matakan da rayuwar ɗan’adam takan riskar kafin haihuwa. A cikin mutane, wannan mataki yana farawa a mako na tara na shigar ciki kuma yana ci gaba har zuwa lokacin haihuwa. A wannan lokaci, ba a kiran kwayoyin halitta masu tasowa a matsayin ’embrayo’, sai dai a kira shi da ‘fetus’ shi ne ɗan tayi a Hausance.

GettyImages 1288913695 230c3b035bce4442b29e1598a492022d
Wani ɓangare na yanayin ɗan tayi a cikin mahaifa. Hoton – Getty Images

Haka nan ɗan tayi yana iya motsi kuma yana iya karɓar sauye-sauye ga abubuwa na waje, yana nuna alamomin girma da fahimta ko azanci. Yana da mahimmanci a lura cewa ana yi amfani da kalmar ɗan tayi ne musamman a zangon da ciki yake kafin haihuwa, kuma yana bambanta da lokacin da ciki yake matakin embrayo ko kuma jariri. Wannan zango na girma yana da mahimmanci ga cikakkiyar lafiya da tsari girman ɗan tayi, yayin da yake shirin zai shiga wani zangon na girma da haɓaka bayan haihuwa.

Ɗan tayi yana wakiltar matakin girma bayan mako na tara na ciki, wanda ke da saurin girma, wanzuwar gabobin jiki, da kuma samuwar gaɓoɓin hankali.

Matakan girman ɗan tayi

Zangon girman tayi yana ƙunshi matakai da dama masu ban sha’awa sosai kuma suna da ɓangarori da suke faruwa tun a lokacin daukar ciki. Tun daga lokacin da ciki ya shiga, girman ɗan tayi yana tsarawa ta matakai da yawa domin samar da cikakke kuma lafiyayyen jariri.

A cikin watanni ukun farko, ɗan tayi yakan wuce matakin embrayo. Wannan shi ne lokaci ko muhimmin zangon da gabobin jiki da tsarin jiki suke fara samuwa. A wannan lokacin ne zuciyar jariri, ƙwaƙwalwa, da ƙashin bayansa suke fara girma. A ƙarshen watanni ukun farko, ɗan tayin ya riga ya haɓaka ƙananan hannaye da ƙafafu, kuma yanayin fuskarsa ya fito yadda za a iya gane fuska ce.

A cikin wasu watanni ukun na zango na biyu, ɗan tayi yake shiga matakin ‘fetal’. Wannan shi ne lokacin da jikinsa yake ci gaba da girma. Ɗan tayin zai fara samar da yatsunsa da ƙasusuwa sannan kuma tsoka ta yi karfi. A tsakiyar cikin, ɗan tayin yana iya jin sauti daga duniyar waje, kuma uwa za ta riƙa jin motsinsa.

A cikin watanni uku na zango uku, ɗan tayi yake kammala girma tare da fara shirin fitowa waje wato haihuwa. A wannan lokacin, gaɓoɓin ɗan tayin suke ci gaba da girma, sannan yana ƙara yin nauyi da sauri. Yana ƙara zama mai kuzari, ta hanyar bige-bigensa da motsinsa yana ƙara ƙarfi yin. A ƙarshen wannan zango na ukun ƙarshe, ɗan tayin yakan zama cikakke jinjiri tare da shirin shigowa duniya.

Siffofin jikin ɗan tayi

Siffofin jikin ɗan tayin na iya bambanta a dukkan tsawon lokacin renon ciki. A matakin, ɗan tayin yana da ƙanƙanta, yawanci tsayinsa ƙasa da inci ɗaya ne, kuma yanayin nauyinsa ma kaɗan ne. Yayin yake girma, yana fara ɗaukar ƙarin fasali da siffofi. A karshen wata na biyu na cikin, ɗan tayin yakan fitar da dukkan manyan gabobinsa kuma a wannan lokacin ne dai hallau yake fara samun kitse a ƙarƙashin fatarsa.

Ɗaya daga cikin fitattun siffofin jikin ɗan tayi shi ne yanayin fuskarsa. A cikin watanni ukun zango na biyu, yakan fitar da idanunsa, hancinsa, da bakinsa, waɗanda galibi ana iya gani a jikin dubban ‘yan tayi. Bugu da ƙari, ɗan tayi zai fitar gaɓoɓi da ‘yan yatsu. Waɗannan siffofin jiki suna ci gaba da bunƙasa da girma yayin da ɗan tayi ya shiga cikin watanni ukun zango na uku.

Wata muhimmiyar siffar ɗan tayi ita ce samuwar wani ruwa da ake kira ‘amniotic’ wanda ke kewaye da ɗan tayin. Wannan ruwan yana ba wa ɗan tayi kariya kuma yana ba da damar motsi a cikin mahaifa. Haka nan yana taimakawa wajen daidaita yanayin zafin jikin ɗan tayi.

Dukkanin siffofin jikin ɗan tayi alamomi ne masu tsari da ban mamaki a yayin renon ciki da shirye-shiryen haihuwa, kama daga ƙanƙanen girmansa a matakin farko zuwa cikakkiyar halitta a ƙarshen watannin renon ciki, ɗan tayin yana samun sauye-sauye masu ban mamaki a cikin kankanin lokaci.

Motsawar ɗan tayi da girman gaɓoɓin hankali

A lokacin renon ciki, ɗan tayi yana fuskantar jerin matakai yayin da yake tasowa. Ɗaya daga cikin mahimman abubuwan da ke nuna girman ɗan tayin shi ne fara motsi. Tun daga makonni takwas (8), ɗan tayin zai fara bayyana motsinsa, kamar idan an taɓa cikin ko kuma sauti daga cikin mahaifa. Waɗannan ayyuka suna zama da niyya a yayin da ɗan tayin ke ci gaba da girma.

Yayin da tayin ke girma, bunƙasar tunaninsa da hankalinsa suna ci gaba. A cikin watanni uku na zango na biyu, ɗan tayin yana iya ganowa da mayar da martani ga abubuwan da ke haifar da motsa jiki daga waje, kamar haske da sauti. Wannan wani muhimmin mataki ne a tsarin girman ɗan tayi, domin shi ne lokacin kafa harsashin da ɗan tayin ke gane duniya a wajen mahaifa bayan haihuwa.

Bincike ya nuna cewa bunkasar tunanin ɗan tayi tana da alaƙa da lafiyarsa gabaɗaya. Alal misali, bincike ya nuna cewa, bayyanar da sauti da sauran nau’o’in abubuwan da kan haifar da motsawa na iya haifar da tasiri mai kyau ga girman ɗan tayin. Saɓanin haka, abubuwa kamar damuwar uwa ko wasu magunguna na iya hana girma da kuzarin dan tayi.

Kula da motsin ɗan tayi da bunƙasar tunani da azanci su ne muhimman al’amura ta fuskar kulawa da haihuwa. Masana kiwon lafiya sukan ƙarfafa gwiwar iyaye mata masu juna-biyu da su riƙa zuwa a kula da motsin ɗan tayi kuma su faɗi duk wani canje-canje ko damuwa da suke fuskanta. Wannan hanya mai mahimmanci tana taimakawa wajen tabbatar da cewa ɗan tayin yana tasowa kamar yadda ake tsammani kuma zai iya nusar da masana kiwon lafiya ga duk wata matsala mai mahimmanci da za ta buƙaci ɗaukar mataki.

Lafiyar ɗan tayi da kula da shi

Tabbatar da lafiya da jin daɗin tayin tana da matuƙar mahimmanci yayin renon ciki. Zuwa awon ciki a kai a kai da saka idanu suna da mahimmanci wajen bin diddigin girma da lafiyar ɗan tayi.

Yayin zuwa wannan awo da binciken yanayin ɗan tayi, ma’aikatan kiwon lafiya na iya gudanar da gwaje-gwaje daban-daban domin tantance lafiyar ɗan tayin. Wannan na iya haɗawa da bincikar ɗan tayi domin fahimtar lafiyarsa, lura da bugun zuciyarsa, da kuma auna girmansa da nauyinsa.

Bugu da ƙari, ana iya shawartar iyaye mata masu juna biyu da su kula da tsarin rayuwa mai kyau, wanda ya haɗa da cin daidaitaccen abinci, motsa jiki na yau da kullun, da samun isasshen hutu don tallafabwa lafiyar ɗan tayin. Nisantar abubuwa masu cutarwa kamar barasa, taba, da wasu magunguna shi ma yana da mahimmanci ga lafiyar ɗan tayi.

Har ila yau, lura da lafiyar ɗan tayi a dukkan lokuta yana da mahimmanci domin tabbatar da samun nasarar haihuwa lafiya, kuma yana da mahimmanci ga iyaye mata masu juna-biyu su ba da fifiko ga lafiyarsu da ta ɗan tayin ta hanyar kula da matakan kiwon lafiya na yau da kullun da kuma zaɓin tsarin rayuwa mai kyau.

Lokacin haihuwar ɗan tayi

Yayin da lokacin haihuwar ɗan tayin ya gabato, lokaci ne mai mahimmanci ga iyaye da kuma likitoci. Wannan lokaci yana kawo ƙarshen doguwar tafiyar ciki da farkon sabon babin rayuwar iyali. Haihuwar ɗan tayi tsari ne mai rikitarwa wanda zai iya ɗaukar sa’o’i ko ma kwanaki, kuma yana buƙatar kulawa da hankali da tallafi daga ƙwararrun masana kiwon lafiya.

A lokacin naƙudar haihuwa, ɗan tayi yakan fara motsawa zuwa kofar haihuwa ta mahaifa, nan ma wata tafiya ce wadda za ta iya zama mai ƙalubale da gajiya. Mahaifiyar na iya samun matsananciyar naƙuda yayin da jikinta ke aiki don fitar da ɗan tayin, yana da mahimmanci a gare ta ta samu maganin da zai sauƙaƙa mata ciwon da kuma tallafin motsawa a wannan lokacin. Tawagar likitocin za su lura da ci gaban naƙudar zuwa haihuwa a hankali, har ma sukan kasance cikin shiri ko ta kwana, idan buƙatar hakan ta taso don tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta.

Da zarar an haifi ɗan tayi, sai ya fara shan iska ta farko sannan ya fara canjawa zuwa rayuwa a wajen mahaifa. Tawagar likitocin za su ci gaba da sa ido kan lafiyar jaririn da kuma ba da duk wata kulawa da ta dace don tallafa wa lafiyarsa. Ga iyaye, haihuwar ɗan tayi abu ne mai ban sha’awa da farinciki, kuma za su kasance tare da sabon jariri, su kuma fara yin tsarin zama iyali. Haihuwar ɗan tayi wani muhimmin al’amari ne da ke buƙatar sa ido a hankali da goyon baya daga kwararrun masu kiwon lafiya.

Yawaitar mutuwar’yan tayi

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, Hukumar Lafiya ta duniya WHO, Bankin Duniya da sashen kula da yawan mutane na Majalisar Dinkin Duniya, sun ƙaddamar da rahoto na farko na haɗin gwiwa dangane da batun yadda ‘yan tayi ke mutuwa a lokacin haihuwa, inda suka nuna cewa, a ko wace shekara, ‘yan tayi kimanin miliyan 2 ne suke mutuwa a lokacin haihuwa a duniya, inda aka yi kisayin cewa, ɗan tayi ɗaya yana mutuwa a cikin dukkan daƙiƙoƙi 16 a lokacin haihuwa a duniya. Barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta ƙara tsananta irin wannan halin da ake ciki a duniya.

Wannan rahoto mai lakabin “abin tausayi da aka kau da kai: mutuwar ‘yan tayi” ya yi bayani da cewa, alƙaluman ƙididdiga sun tabbatar da cewa, yawancin ‘yan tayin da ke mutuwa a lokacin haihuwa suna da alaƙa da rashin kulawa mai dacewa a lokacin samun ciki da kuma lokacin haihuwa. Manyan ƙalubalen da ake fuskanta yanzu su ne, rashin isassun hidimomin da ake bai wa masu juna biyu kafin haihuwa da kuma a lokacin haihuwa, da matsalar ƙarancin aikin horarwa da zuba jari kan majiyyata da ungozoma.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa da yawansu ya kai kaso 84 cikin 100 suna faruwa ne a ƙasashe masu ƙarancin kuɗin shiga da kuma ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin kuɗin shiga. Ban da haka kuma, a dukkan kasashe masu ƙarancin kuɗin shiga da kuma ƙasashe masu yawan kuɗin shiga, yawan mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ya fi yawa a yankunan karkara, gwargwadon yadda lamarin yake a birane. Rahoton ya kara da cewa, ana iya magance mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ta hanyar ba da kulawa mai dacewa cikin hanzari.

A yankunan nahiyar Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da yankin tsakiyar Asiya da kuma yankin kudancin Asiya, mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ta fi yawa gwargwadon a nahiyar Turai, arewacin nahiyar Amurka, kasashen Australiya da New Zealand.

Manazarta

Dnp, L. R. (2025, March 10). What is the difference between an embryo, a fetus, and a baby? Hello Clue.

NCI Dictionary of Cancer Definition of fetus . (n.d.). Cancer.gov.

The Editors of Encyclopaedia Britannica. (2025d, February 22). Fetus | Growth, development, nutrition. Encyclopedia Britannica.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page