Sinadarin Europium sinadari ne daga cikin sinadaran da ke da matuƙar muhimmanci a masana’antun zamani, musamman a fannoni da suka shafi fitulu, lantarki, fasahar alluna masu nuna hotuna, da kuma harkokin tsaro. Ana samun shi a matsayin sinadarin ƙarfe mai laushi wanda ke cikin rukunin Lanthanides, wato rukunin sinadarai guda goma sha biyar (15) da ke tsakanin lamba ta 57 zuwa 71 a kan teburin jadawalin sinadarai (Periodic Table) a Turance. Europium yana da alamar Eu kuma yana da lamba atomic 63.
Duk da kasancewar Europium ba a samun shi da yawa a cikin ƙasa, ƙarancin samun nasa ba ya hana amfani da shi a cikin fasahar zamani saboda muhimmancin da yake da shi. Ana amfani da shi wajen ƙera na’urar phosphors da ke fitar da launuka iri-iri a talabijin, allunan kwamfuta da wayoyin hannu na zamani. Har ila dai ana amfani da shi wajen sarrafa takardun kuɗi domin kariya daga jabun kuɗaɗe, da kuma a fannin nukiliya domin ɗaukar neutron.
Tarihin gano Europium
Sunan wannan sinadari na Europium, ya samo asali ne daga sunan nahiyar Turai (Europe), an yanka wa wannan sinadari sunan ne kasancewar an gano shi a nahiyar a duk faɗin duniya. Wannan sinadari ya kasance wani ɓangare na wasu sinadarai da aka gano tun farko kamar samarium da gadolinium, amma daga baya wani masanin sinadarai daga Faransa mai suna Eugène-Anatole Demarçay ya ware shi a shekara ta 1901.

Demarçay, wanda ya shahara wajen nazarin spectroscopic (wato nazarin haske da siffar makamashin sinadarai), ya lura da wani abu da bai dace da samarium ba, kuma bayan bincike mai zurfi ya gano cewa akwai wani sabon sinadari a cikin samfurin. Wannan sabon sinadari shi ne Europium, wanda daga nan aka fara warewa a matsayin sinadari mai zaman kansa.
Europium sinadari ne da aka gano sama da shekara 120 da suka wuce, kuma har yanzu yana taka muhimmiyar rawa a cigaban ayyukan fasaha a duniya. Duk da cewa ana samun shi a ƙanƙanin adadi, amfani da shi ya wuce yadda ake tsammani.
Siffofin sinadarin Europium
- Europium yana da launin karfe fari mai ɗan rawaya, yana da laushi sosai har ana iya yanyanka shi da wuƙa.
- Yana oxidizing da sauri idan ya haɗu da iska ko ruwa, yana samar da Europium oxide (Eu₂O₃) da hydroxide (Eu(OH)₃).
- Yanayin oxidation mafi yawa da Europium ke shiga su ne +2 da +3.
- Yana narkewa a zafin da ya kai 822°C kuma yana tafasa a 1527°C.
Yadda sinadarin ke samuwa a duniya
Europium ba a samunsa a yanayi a matsayin sinadari mai zaman kansa. Ana samun shi ne daga cikin ma’adinan da ke ɗauke da sinadaran lanthanides kamar:

- Monazite: Wani mineral ne mai arzikin sinadaran lanthanides.
- Bastnäsite: Mineral ne da ke da sinadarai irin su cerium da europium.
Waɗannan ma’adanai ne da ake hakowa daga ƙasa, sannan a ware Europium ta amfani da fasahohin sinadarai da injiniya (hydrometallurgy da solvent extraction). Ƙasashe kamar China, Brazil, da India ne ke da manyan ma’adanan da ke ɗauke da Europium.
Matakan samar da Europium daga waɗannan mineral da aka ambata a sama sun haɗa da:
- Niƙawa da tace minerals.
- Ware sinadarai ta hanyar ion-exchange ko solvent extraction.
- Sarrafa shi zuwa siffar oxide ko metallic Europium.
Amfanin sinadarin Europium a aikace
1. Phosphors a cikin allunan na’urorin haska hotuna
Wani babban amfanin Europium shi ne samar phosphors — sinadarai masu taimakawa wajen fitar da haske lokacin da suka fuskanci makamashi. Ana amfani da su a cikin:
- Talabijin CRT da LCD
- LED lights
- Allunan kwamfuta da wayoyin hannu
- Lampen fluorescent.
Europium (III) oxide yana fitar da launin ja, yayin da Europium (II) ke fitar da launin shuɗi. Waɗannan launuka biyu su ne ginshiƙai a tsarin RGB (Red-Green-Blue) na na’urorin haskawa.

2. Kariya a takardun kuɗi
Babban Bankin Turai (European Central Bank) na amfani da sinadarin Europium a takardun kuɗi na euro domin hana ƙirƙirar jabunsu. A ƙarƙashin hasken ultraviolet, Europium na fitar da launin haske wanda zai bayyana a matsayin kariya. Wannan na nufin cewa masu yin jabun takardun kuɗin ba za su iya kwaikwayon wannan hasken ba.
3. Masana’antar makamashin nukiliya
Europium yana iya ɗaukar neutrons sosai ba tare da fitar da su ba. Wannan siffar ce ta sa ake amfani da shi a matsayin neutron absorber a cikin tashoshin nukiliya domin sarrafa zafin da ke fitowa daga nukiliya.
4. Gwaje-gwajen kimiyya da magunguna
Ana amfani da gishirin Europium wajen gano sinadarai a fannin spectroscopy da kuma a cikin binciken likitanci, musamman a fannin gano ƙwayoyin cuta ko abubuwan da ke gurɓata ruwa da abinci.
5. Ma’aikatar lantarki
Akwai wasu ƙarin amfani da Europium a masana’antun lantarki kamar:
- Sensors masu amfani da hasken UV
- Na’urori da kayan aikin ganowa (detectors)
- Ƙananan kayan lantarki masu amfani da photoluminescence.
Rabe-raben Isotopes a Europium
Isotopes su ne nau’o’in sinadari guda ɗaya da ke da adadin proton iri ɗaya a cikin ƙwayar halittarsu, amma suna da adadin neutron daban-daban. Europium na da nau’o’i da dama na isotopes, amma biyu ne suka fi ɗorewa kuma ake samun su cikin yanayi (natural occurrence):
1. Europium-151 (¹⁵¹Eu)
- Adadin Proton: 63
- Adadin Neutron: 88
- Adadin samuwa a tsarin natural kusan: 47.8%
- Siffofinsa: Isotope ne mai ɗorewa, baya rushewa cikin sauƙi. Ana amfani da shi wajen binciken sinadarai a fannoni irin su nuclear physics da nazarin haske.
2. Europium-153 (¹⁵³Eu)
- Adadin Proton: 63
- Adadin Neutron: 90
- Adadin samuwa a tsarin natural kusan: 52.2%
- Siffofinsa: Shi ma isotope ne mai ɗorewa, kuma shi ne mafi yawa a doron ƙasa. Ana amfani da shi a masana’antu da fasahar lantarki, musamman wajen samar da sinadarai masu ɗauke da phosphors.
Baya ga waɗannan biyu, akwai wasu isotopes da ba sa ɗorewa, kamar Europium-152 da Europium-154, waɗanda ake amfani da su a wasu fannonin binciken kimiyya da nukiliya.
Matsayinsa na oxidation (oxidation states)
Sinadarin Europium yana da matsayi biyu na oxidation, wato yawan electrons da yake rasawa lokacin da ya shiga cikin sinadarai. Waɗannan matsayi suna da matuƙar muhimmanci wajen tantance irin haɗuwar da Europium zai yi da wasu sinadarai.
+2 Oxidation State (Eu²⁺)
Wannan shi ne matsayi mafi ƙaranci na oxidation da Europium zai iya samu. A wannan hali, Europium yana rage electrons biyu, kuma yana samar da haɗin da ke da launin shuɗi mai haske.
- Yana da sauƙin haɗuwa da iskar oxygen da ruwa.
- Ana amfani da wannan nau’i a wajen ƙera phosphors masu hasken shuɗi ko kore a talabijin da fitilun zamani.
+3 Oxidation State (Eu³⁺)
Wannan shi ne mafi kwanciyar hankali da ɗorewa daga cikin dukkanin matsayin sinadarin a yayin oxidation.
- A wannan mataki, Europium na rasa electrons uku.
- Yana da mahimmanci wajen samar da hasken launin ja a LED, plasma TV, da sauran na’urorin haske.
- Mafi yawan haɗin Europium a cikin masana’antu yana cikin wannan oxidation state ɗin.
Rabe-raben haɗuwar sinadarin (Chemical Compounds)
Europium na iya haɗuwa da wasu sinadarai domin samar da gishiri da sauran sinadaran haɗaka (complex compounds). Wasu daga cikin manyan nau’ikan sinadarai da Europium ke samarwa sun haɗa da:
- Europium(II) chloride (EuCl₂)
- Europium(III) oxide (Eu₂O₃)
- Europium(III) nitrate (Eu(NO₃)₃)
- Europium-doped yttrium oxide (Y₂O₃:Eu³⁺) – wanda ake amfani da shi wajen samar da hasken ja a fitilun TV da monitor.
Wadannan sinadarai su ne ke da alhakin samar da nau’o’in launuka daban-daban a na’urori masu fitar da haske (displays).
Matakan kariya yayin amfani da Europium
Duk da cewa Europium ba guba ba ce , yana a matsayin sinadari, ana buƙatar matakan kariya lokacin sarrafa shi, saboda dalilai kamar:
- Shaƙa (Inhalation): Ƙurar sinadarin Europium na iya haifar da cutukan huhu.
- Iska: Europium tatacce na iya kamawa da wuta cikin sauri idan ya haɗu da iska.
- Wuta: Ana ajiye shi a cikin kayan kariya kamar mineral oil don hana oxidization.
- Jiki: Ba a san ko yana da illa ga fata ba sosai, amma an ba da shawarar amfani da safar hannu da hula lokacin aiki da shi.
Mahimmancin Europium ga cigaban zamani
A yau sinadarin Europium yana taka muhimmiyar rawa a rayuwar ɗan’adam ta yau da kullum, duk da ƙarancin shi. Yana daga cikin sinadarai da ke ƙarfafa:
- Fasahar LED
- Ingancin allunan kwamfuta da talabijin
- Kariya ga takardun kuɗi
- Tabbatar da ingantaccen sarrafa makamashin nukiliya.
Cigaban bincike a fannin kimiyyar kayan aiki (material science) da nanotechnology na ƙara buɗe sabbin hanyoyin amfani da Europium a masana’antu daban-daban.
Manazarta
Greenwood, N. N., & Earnshaw, A. (2012). Chemistry of the Elements (2nd ed.). Butterworth-Heinemann.
Gschneidner, K. A., & Eyring, L. (Eds.). (2000). Rare Earths: Science, Technology, and Applications IV. The Minerals, Metals & Materials Society.
Emsley, J. (2011). Nature’s Building Blocks: An A–Z Guide to the Elements. Oxford University Press.
Thomas, P. J., Carpenter, D., & Bajpai, R. K. (2016). Introduction to Biological and Small Molecule Drug Research and Development: Theory and Case Studies. Elsevier.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 23 July, 2025
An kuma sabunta ta 25 July, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.